Connect with us

Manyan Labarai

Ana zargin wata amarya da yanke makarfafar angonta bayan da ta fara sumar da shi da Tabarya.

Published

on

Tunda fari dai amaryar ta bukaci angon nata da ya siyo mata Madara ne bayan da ya dawo daga wajen sana’anarsa ta saran Itace a Jeji, lamarin da yasa ya je siyar da itacen bai siyu, inda ya ranto kudi ya siyo ya kawo mata, dan haka ta bukaci ya rakata bakin Labi ta tsinko ganyen Magani, ashe ta boye Tabarya da wuka a Hijabi.

Suna zuwa bakin labi gurin da babu mutane kawai sai yaji ta kwantare masa Kai da tabaryar ta baya har ta kai ta karya masa Mumamuki ta zubar masa da Hakora ya suma, daga nan akayi zargin ta zaro wukar inda ta yankesu ta saka su a Leda.

Bayan da asirinta ya tonu ne aka kai ta wajen ‘yan sanda, inda a yanzu shi kuma yake kwance a Asibitin koyarwa na Mallam Aminu kano, sai dai likitoci sun ce idan ma ya rayu to babu zancen Makarfafar domin yanzu haka ta riga ta rube a ledar har an binne ta

A zantawar wakilinmu Ibrahim Abdullahi sorondinki da ‘yar-uwar angon Zulaihat Muhammad ta ce, auren zumunci aka yi musu, kasancewar iyayen angon mai suna Sa’idu Lawal ‘yan uwan iyayen amaryar ne.

Ta kuma ce yanzu haka amaryar da ake zargin ta na hannun mahukunta a jihar Kaduna, inda al’amarin ya faru a garin Tafa har zuwa aga abun da hali zai yi dangane da jikin angon na ta idan ya rayu, kasancewar kwanaki 12 da yin bikinsu al’amarin ya faru.

Manyan Labarai

Wata Sabuwa: Lauya ya nemi kotu ta kama kwamishinan Shari’a na jihar Kano

Published

on

Wani lauya mai zaman kan sa a jihar Kano Barista Haruna Musa Muhammad, ya yi ƙorafi a gaban babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar, akan ta kama kwamishinan Shari’a na jihar Kano Barista Haruna Isah Dederi, da wasu manyan mukarraban gwamnatin jihar.

Lauyan wanda yake wakiltar mai kara Nura Bashir Ahmad, ya bayyana cewar gwamnatin jihar Kano ta rushe wa Nura gida duk da cewar ya samu hukunci a babbar kotun tarayya akan kada a rushe masa gidan.

Cikin wata ƙunshin Shari’a mai lamba FHC/KN/CS/240/2023, mai Shari’a Simon Amobida, ya ayyana cewar kotun tarayya ta gamsu da takardun mallaka da mai ƙara Bashir Ahmad ya gabatar mata, don haka ne ma ta ayyana cewar gidan mallakinsa ne.

Kotun dai tun a ranar 13 ga watan biyu na shekarar da ta gabata ta 2024, ta zartas da hukuncin akan batun.

Mai karar Bashir ta bakin lauyansa Barista Haruna Musa, sun bayyana cewar sun rubuta koke zuwa gaban kotun da ta yi hukuncin tun da dai suna zargin waɗanda ake ƙarar sun raina wannan hukunci kamar yadda ya bayyana a zantawar sa da wakilin Dala FM Kano.

Akan wannan batu ne wakilin namu ya tuntuɓi kwamishinan Shari’a na jihar Kano Barista Haruna Isah Dederi, ta wayar salula, sai dai bai samu damar ɗaa wayar ba, ya kuma aike masa da gajeren saƙon kar ta kwana nan ma bai bada amsa ba, amma yana dakon sa.

Continue Reading

Manyan Labarai

Budurwa ta mutu yayin wata Gobara da ta kama cikin gidan su a Kano

Published

on

Wata Gobara da ta tashi a wani gida ta yi sanadiyyar rasuwar wata budurwa a unguwar Ja’en Sabere da ke ƙaramar hukumar Gwale a Kano da ke arewacin Najeriya, tare da ƙonewar wasu sassan gidan.

Mamallakin gidan da lamarin ya faru mai suna Saminu Abba ne ya tabbatar wa tashar Dala FM faruwar lamarin a ranar Alhamis, 16 ga watan Janairun 2025.

Ya ce gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe ɗaya na daren jiya Laraba, lamarin da jami’an hukumar kashe Gobara ta jihar Kano da ma ƴan Bijilanten yankin da sauran al’umma suka kai ɗauki.

“Muna cikin Bacci muka ji wata ƙara da ihun mutanen unguwa, da muka tashi muka ga Gobara ce ta tashi a wasu sassan gidan mu kuma wutar ta tare hanyar da za mu fita gashi tana ci ba ƙaƙƙautawa, “in ji Saminu”.

Ya ci gaba da cewa, “Bayan jami’an hukumar kashe Gobara da ƴan Bijilanten yankin, da sauran al’umma sun kawo musu ɗauki, ne aka fasa Gini ta gidan maƙotan su inda su shida suka fita daga gidan sai dai ƴar su budurwa mai shekaru 18 mai lalurar Sikila ta rasu”.

Mallam Saminu Abba ya ƙara da cewa, kayayyakin su na sawa da wasu tarin kayayyaki da dama ne suka ƙone ƙurmus, lamarin da ya nemi ɗaukin mahukunta da su kai musu ɗauki bisa halin da suka samu kan su a ciki.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ba kan ta: An sace birkin jirgin sama guda 80 a Kano

Published

on

Kotun majistret mai lamba 70 da ke jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Faruk Ibrahim Umar, ta aike da wasu mutane gidan ajiya da gyaran hali bisa zargin su da haɗa baki da Sata.

Ƙunshin zargin da ake yi wa mutanen ya ayyana cewar, a ranar 11 ga watan 12 na shekarar da ta gabata ta 2025, wani mutum mai suna Otaru Bashir ma’aikaci a kamfanin sifirin jiragen sama na Azman, ya yi ƙorafi cewar mai gadin kamfanin nasu ya haɗa baki da wasu mutane sun sace musu birkin jirgin sama guda 80.

Ana dai zargin mutanen ne da sace waɗannan barakun wato birkin jirgin sama guda tamanin a filin jirgin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano.

Mutanen da ake zargin sun hadar da Nuhu Auwalu da Yakubu Bala da Emanuel Luka, sai kuma safiyanu Abdullahi.

Ko da aka karanta wa mutanen ƙunshin zargin da ake yi musu dukkaninsu sun musanta, a nan ne kotun ta aike da mutanen gidan gyaran hali tare da sanya ranar 11 ga watan gobe dan sauraron shaidu akan shari’ar.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewar, yayin zaman kotun an ambata cewar, binciken ƴan sanda ya bayyana cewar kimar kayan ya kama Naira miliyan dari da arba’in, sai dai yayin bincike an gano birkin jirgin guda uku a hannun wanda ake zargi na uku mai suna Yakubu Bala.

Continue Reading

Trending