Connect with us

Hangen Dala

An kuma:- shugabannin kananan hukumomi uku sun koma jam’iyyar NNPP

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya karɓi shugabannin ƙananan hukumomi su 3 zuwa jam’iyyar NNPP da suka fito daga APC, sun haɗar da na Nasarawa Auwalu Lawan Shu’aihu Aranfosu, Sai na Garin Malam Mudassir Aliyu da kuma na Dawakin Tofa Hon Ado Tambai kwai, inda gwamnan yace zasuyi aiki tare domin kawowa jihar Kano ci gaba.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan da yammacin Asabar yayin da yake karɓar su a fadar gwamnatin Kano da sauran kansilolin ƙananan hukumomin.

Gwamna Yusuf ya kuma ce a shirye gwamnatin sa take domin karɓar duk wani da yake da kishin al’umma domin ciyar da jihar kano gaba.

Da suke jawabi shugabannin ƙananan hukumomin yayin karɓar tasu sun ce zasu kasance masu bawa gwamnati haɗin kai.

Gwamna Abba yace yanzu haka dukkan shugabannin ƙananan hukumomin da suka dawo za’a dunga gudanar da taron jam’iyya tare da su domin suma sun zama ƴan jam’iyya.

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Hangen Dala

Gaya Ajingi Albasu:- Dan majalisa ya raba kayan abinci

Published

on

Dan majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu Dakta Ghali Mustafa Fanda ya fara rabon tallafin kayan abinci ga al’ummar kananan hukumomin uku.

 

Yayin rabon tallafin kayan abincin, Dakta Ghali Mustafa yace yayi rabon tallafin ne domin fara sauke nauyin al’ummar da yake wakilta.

 

” Wannan tallafi zamu bayar da shi ne domin fara sauke nauyin al’ummar da suka zabe mu, kuma wannan shi ne karon farko, kuma yayi daidai da bukatar al’umma a yanzu, shiyasa muka fara da tallafin kayan abinci”.

 

“A cikin wannan tallafi mutane kimanin dubu ashirin ne zasu amfana, wanda zamu bayar da buhunan Shinkafa da Gero da Garin masara.”

 

Haka kuma ɗan majalisar ya bayar da tallafin Naira miliyan ashirin ga matasan kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu.

 

Sai kuma ɓangaren dalibai mata, wanda shima a yau dan majalisar ya dauki nauyin karatun dalibai mata guda 60 a bangaren lafiya.

 

Haka kuma cikin jawabin nasa Hon Ghali ya kuma ce nan gaba kadan zai bayar da tallafin taki ga manoma, da kuma farfaɗo da dukkanin rijiyon burtsatse na kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu a wani mataki na samar da ruwan sha.

 

Da yake nasa jawabin mataimakin gwamnan Kano Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo wanda ya samu wakilcin mai baiwa Gwamna Shawara kan harkokin siyasa Hon Sunusi Surajo Kwankwaso kira yayi ga sauran wakilan al’umma da suyi koyi da Dakta Ghali Mustafa Fanda wajen ayyukan alkhairi da kuma jin kan al’umma.

 

Haka kuma Hon Sunusi Surajo ya yabawa dan majalisar bisa bayar da tallafin ga ƙananan hukumomin uku.

 

Taron dai wanda ya gudana a cikin Islamic Centre na karamar hukumar Gaya ya samu halartar manya, da kuma jagororin yankunan uku, kuma nan take Dan majalisar Tarayya Dakta Ghali Mustafa ya fara rabon tallafin

Continue Reading

Hangen Dala

Shugaban kasa ya bayar da umarnin bude Boda

Published

on

Shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin bude iyakokin kasar nan.

Cikin sanarwar da ya fitar shugaban ya ce duk wata iyaka dake tsakanin Nigeria da jamhuriyar Nijar a gaggauta bude ta.

Karin bayani na nan tafe…

Continue Reading

Trending