Connect with us

Addini

Samar da darasin hukunce-hukuncen addinin musulunci a makarantun gaba da sakandire zai taimaki dalibai – Prof. Bashir Aliyu Umar

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Alfurkan dake nan Kano Farfesa Bashir Aliyu Umar, ya shawarci masu ruwa da tsaki da su samar da wani fanni da za’a rinka koyar da dalibai masu koyon aikin lafiya hukunce-hukuncen addinin muaukunci a cikin makarantun gaba da sakandire da na koyar da harkar lafiya, bisa mahimmancin da hakan ke da shi ga al’ummar musulmi.

Limamin ya bayyana hakan ne ta bakin wakilicin da ya samu na Daraktan gidauniyar Alfurkan Charity Foundation Dakta Abubakar Muhammad Abubakar, yayin taron wayar da kai akan yadda ya kamata ma’aikatan lafiya su kiyaye hukunce-hukuncen addinin musulunci a aikin su.

Kungiyar musulmai masu lura da lafiya Jinya ta kasa IMAN, ne da hadin gwiwa da Kungiyar mata musulmi ta Afrika ta kasa AMWA, suka shirya taron inda aka gudanar a ranar Lahadi.

Ya kuma ce akwai bukatar ma’aikatan lafiyar su kara kiyaye hukunce-hukuncen addinin musulunci yayin gudanar da ayyukansu, musamman ma wajen kula da kwadaitar da marasa lafiya yin ibada ko da kuwa yana cikin tsananin ciwo ne bisa mahimmancin da hakan ke da shi.

Da take nata jawabin shugabar Kungiyar mata musulmi ta Afrika ta kasa AMWA, Aisha Ishak Sulaiman, da shugabar Kungiyar musulmai masu lura da lafiya ta kasa IMAN, Salamatu Ibrahim, sun ce sun shirya taron ne domin wayar da kan ma’aikatan lafiyar a mahanga ta addinin musulunci, domin ganin an gudu tare an kuma tsira tare.

A nata jawabin mukaddashiyar babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano a bangaren mata, Hajiya Khadijah Sagir Sulaiman, shawartar ma’aikatan lafiyar ta yi da su kiyaye da dokokin Ubangiji S.W.T, a aikin su.

Yayin taron dai jami’an Jinya, da ma likitoci da sauran al’umma da dama ne suka samu damar halarta daga sassa daban-daban na jihar Kano.

Addini

Matsin Rayuwa: Shugabanni ku sassautawa al’umma – Babban Limamin Kano

Published

on

Babban limamin Kano, kuma wanda ya jagoranci sallar idi a babban masallacin idin na Kofar Mata a nan Kano, Farfesa Muhammed Sani Zaharaddin, ya ja hankalin shugabanni da su sassautawa al’umma, sakamakon halin matsin rayuwar da ake ciki a yanzu.

Farfesa Muhammed Sani Zaharaddin, yayi jan hankalin ne yayin huɗubar da ya gabatar, bayan kammala sallar idi da ta gudana a yau Laraba, a babban masallacin idin dake unguwar Kofar Mata a Kano.

Ya kara da cewa kasancewar al’umma na cikin mawuyacin hali da kuncin rayuwa, akwai buƙatar shugabanni su yi bakin ƙoƙarin su, domin kawo sauki daga halin matsin halin rayuwar da ake fama dashi.

Yayin sallar Idin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da mataimakin sa Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da sauran al’umma da dama ne suka halarta.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Abba Haruna Idris ya rawaito cewa, Farfesa Muhammed Sani ya kuma ja hankalin al’umma, da su koma ga Allah Subhanahu wata’ala domin samun dacewa a Duniya da gobe Ƙiyama.

Continue Reading

Addini

Ku fara duban watan Sallah daga gobe Litinin – Fadar Sarkin Musulmi

Published

on

Yanzu haka kwamitin ganin wata na Fadar mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya buƙaci al’ummar musulmin ƙasar nan da su fara duban jinjirin watan Shawwal, daga gobe Litinin, 8 ga watan Afrilun, 2024 da ake ciki.

Bayanin hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar a yammacin yau Lahadi a jihar Sokoto.

Sanarwar ta ce, duk wanda ya ga watan Shawwal, ya sanarwa Mai Gari ko Hakimi mafi kusa wanda kuma zai sanar har zuwa fadar Sarkin Musulmi.

Har ila yau, fadar Sarkin musulmin ta kuma bayar da lambobin waya waɗanda mutane za su yi amfani da su wajen ba da rahoton ganin watan Sallah ga fadar Sarkin musulmin, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta BBC ta rawaito.

Continue Reading

Addini

Iyaye ku kula da tarbiyyar ƴaƴan ku – Malama Fatima Tsakuwa

Published

on

Malamar addinin musulunci dake nan Kano Malama Fatima Ahmad Tsakuwa, ta shawarci mata da su ƙara himma wajen kula da tarbiyyar ƴaƴansu, tare da kuma zaburar da su mahimmancin yin addu’a a cikin wannan wata na Ramadana, domin rabauta da rahamar Ubangiji S.W.T.

Malama Fatima Ahmad Tsakuwa, ta bayyana hakan ne yayin taron bita ta musamman da gidauniyar Bango Charity Foundation ƙarƙashin Malama Fatima Yusif Mai tama, wanda gidauniyar ta shirya wa Mata, da bitar ta shafi watan Azumin Ramadana, akan yadda iyaye matan za su kula da ƴaƴan su, da ya gudana a ofishin ƙungiyar dake unguwar Sharaɗa a Kano.

Wakiliyar tashar Dala FM Kano, ta rawaito cewa malama Fatima Tsakuwa ta ce akwai buƙatar iyayen su ƙara lura da tarbiyyar ƴaƴansu, tare da yawaita karatun Al-kur’ani mai girma domin rabauta da falala a wajen Allah S.W.T.

Continue Reading

Trending