Connect with us

Wasanni

Kasar Cote D’Ivoire ta yi nasara akan Najeriya 2-1, a gasar nahiyar Afrika ta Afcon 2023.

Published

on

Kasar Ivory Coast ta lashe gasar cin Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) na 2023, bayan doke Najeriya da ci 2 da 1 a wasan karshe na gasar.

Rahotanni dai sun bayyana cewar mai masaukin bakin ta zama zakara ne, bayan ta warware kwallon da Najeriya ta jefa mata kafin tafiya hutun rabin lokaci a raga.

Yayin wasan dai dan wasan bayan Najeriya, Troost Ekoong ne ya fara jefa mata kwallo a minti na 38 a ragar Ivory Coast.

Sai dai kuma bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Ivory Coast ta warware kwallon a minti na 62 ta hannun dan wasan tsakiyarta, Franck Kessie.

Yayin da aka kai munti na 81 Sebastian Haller ya kara wa mai masaukin baki kwallo ta biyu a raga, wanda hakan ya sanya ta zama zakarar AFCON ta 2023.

Yanzu haka dai ana shirye-shiryen bayar da kyauta ga kasar da ta yi nasara, da kuma wadanda aka shirya baiwa kyaututtukan, wanda kuma a wajen yanzu haka akwai mataimakin shugaban kasa Kasheem Shatima, da gwamnan jihar Katsina Umar Dikko Radda, da na jihar Nassarawa Abdullahi Sule, da kuma ministan Wasanni, da sauransu.

Idan ba a manta ba Najeriya ta doke Ivory Coast a wasan rukuni da suka fafata da ci daya ta hannun Troost Ekoong a bugun fanareti, kamar yadda jaridar Aminiya ta rawaito.

Labarai

Real Madrid ta kaddamar da Alexander

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta ƙaddamar da ɗan wasa Trent Alexander Arnold a yau a matsayin ɗan wasan ta

Inda shugaban ƙungiyar Flerontino Perez yace yau suna matuƙar Farin ciki kasancewar sun mallaki babban ɗan wasan baya a duniya.

 

Shima ɗan Wasa Arnold ya bayyana cewa yana cikin farin ciki kuma mafarkin sa ya cika na zama ɗan Wasan Madrid a yau.

Continue Reading

Labarai

Arsenal ba kanwar lasa ba ce – Me tsaron Gidan Real Madrid

Published

on

Me tsaron Gidan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Thibaut Courtois yace sun yi rashin nasara ne a wasan da suka buga a jiya da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, saboda Arsenal din ba kanwar lasa ba ce.

A jiya Laraba ne dai aka fafata wasan kusa da na kusa da na karshe, tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma Arsenal Inda Arsenal ta lallasa Real Madrid da ci 2 da 1.

Continue Reading

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Trending