Connect with us

Manyan Labarai

Zamu bibiyi hakkin matashiyar da dan kasar waje ya turawa Kare ya yi kaca-kaca da jikinta a Kano – Human Right

Published

on

Wata matashiya mai suna Messi Ageyo, ta nemi daukin mahukunta bisa yadda take zargin wani dan kasar waje da take aiki a gidansa ya sakar mata karensa a cikin gidan har ta kai ga ya yi kaca-kaca da jikinta, lamarin da yasa ba ma ta iya mota jikin nata yadda ya kamata.

A zantawar gidan rediyon Dala FM Kano, da matashiyar ta ce, lamarin ya faru ne tun a daren Larabar da ta gabata, inda bayan ta koma gidan ne cikin dare mai gidan ya rufe ta da fada kan fitar da ta yi, inda ta ce ya sakar mata karen lamarin da ya sa horarren karen ya yayyage mata jiki ta ko ina wanda jini ya rinka fita daga jikin nata.

Ta ci gaba da cewa, yanzu haka ba ta jin dadin jikinta bisa raunukan da karen ya ji mata, a dan haka ne suka je ofishin kungiyar kare hakkin dan adam ta Global Community for Human Rights Network dake jihar Kano, don ta shige mata gaba wajen nema mata hakki, inda ta ce tana neman diyyar Naira mulyan goma domin yin maganin jikin nata.

Josep, dan uwa ne ga matashi Messi, ya ce tun da mutumin dan kasar wajen ya kai ‘yar uwar ta su Asibiti aka dawo da ita Gida bai kara wai-wayar su ba, hakan ya sa suke neman daukin mahukunta da a nema mata hakkin ta.

Kasancewar ‘yan uwan matashiyar sun shigar da koken su ne a ofishin kungiyar kare hakkin dan adam ta Global Community for Human Rights Network dake Kano, daraktan kungiyar Alhaji Gambo Madaki, ya ce sun rubuta takarda tare da hada mutanen da jami’ansu domin zuwa Asibitin don duba lafiyar matashiyar tare da duba matakin da za su dauka na gaba.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya yi duk mai yiyuwa don ji daga bangaren dan kasar wajen mai suna Salom Samual kan al’amarin, sai dai yaki bada dama a nadi muryarsa, amma dai ya musanta sakarwa matashiyar karen, inda ya ce tama saba da karen, amma dai dai yi duk mai yiyuwa akan samun lafiyarta.

Manyan Labarai

Lauya ya nemi a biya Abduljabbar Kabara Naira miliyan 20 saboda ɓata masa lokaci da aka yi.

Published

on

Babbar kotun jaha a ɓangaren ɗaukaka ƙara ƙarƙashin masu Shari’a Aisha Mahamud, da Nasir Saminu, sun sanya ranar 9 ga wannan watan da ake ciki dan ci gaba da sauraron daukaka karar, da Abduljabbar Nasir Kabara ya shigar.

A zaman kotun na yau lauyan Abduljabbar, Barrista Yusuf Sadik, ya shaidawa kotun cewar a shirye suke a fara sauraron daukaka karar.

Sai dai lauyan gwamnati ya bayyana cewar basu shirya ba dan haka a sanya wata ranar.

Lauyan Abduljabbar ya shaidawa kotun cewar sun bai wa lauyoyin gwamnati takardun bayaninsu tun a watan 2 da ya gabata, dan haka a biya Abduljabbarun Naira miliyan 20 saboda ɓata masa lokaci da aka yi.

Sai dai lauyan gwamnati ya yi suka an kuma duba lokacin da aka bada takardun a watan uku ne dan haka wannan lauya ya janye rokonsa.

Daga nan ne kotun ta sanya ranar 9 ga watan nan na Mayu da ake ciki, an kuma umarci lauyan gwamnati da ya yi martani idan yana da shi kafin wannnan rana.

Wakilinmu na Kotu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa, Abduljabbar Nasir Kabara dai ya daukaka karar ne dan kalubalantar hukuncin kutun shari’ar muslunci ta kofar kudu, wadda ta yanke masa hukuncin kisa ta hanya rataya bisa samunsa da laifin ɓatanci.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gobara ta ƙone tarin kayayyaki a gidan tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau

Published

on

Wata Gobara ta tashi a Gidan Tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau dake Mudubawa a yankin Karamar hukumar Nassarawa, inda ta ƙone wasu kayayyaki a ɗakin matar sa waɗanda zuwa yanzu ba’a ƙayyade ba.

Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta faro ne daga ɗakin Girki na matar tsohon gwamnan Hajiya Halima Shekarau, tun yammacin jiya Lahadi.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, mai magana da yawun tsohon Gwamnan Malam Sule Ya’u Sule, ya ce gobarar ta shafi iya daki ɗaya ne a cikin gidan dake Munduɓawa.

A nasa ɓangaren kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, PFS Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce da zarar sun kammala tattara alƙaluma da bincike, zai magantu a nan gaba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamnan Kano ya ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa ta Ɗan Agundi

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa da za’ayi a mahaɗar Ɗan Agundi, da ke ƙaramar hukumar Birni, domin samarwa al’ummar jihar saukin zirga-zirga a yankin.

Da yake ƙaddamar da aikin a yammacin yau gwamnan ya ce, gwamnatin Kano za ta sanya idanu wajen ganin an kammala aikin cikin ƙanƙanen lokaci, hakan yasa yanzu gwamnatin ta tanadi duk wasu kayan aiki da ake buƙata domin gudanar da aikin cikin nasara.

Har ila yau, gwamnan Abba Kabir, ya kuma ce an samar da hanyoyin da al’umma za su bi, domin samun saukin zirga-zirga har zuwa lokacin da za’a kammala aikin baki ɗaya.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce, an samo kanfani mai inganci wanda zai yi aikin cikin ƙanƙanen lokaci, domin ci gaba da gudanar da zirga-zirga akan lokaci.

Continue Reading

Trending