Connect with us

Labarai

Ciwon kansar yara karuwa yake yi yanzu a Kano – CMD AKTH

Published

on

Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya shawarci mahukunta da su kara himma wajen samar da hanyoyin wayar da kan al’umma ta yadda za’a samu damar kawar da cuttuuka masu yaduwa.

Sarkin ya bayyana hakan ne ta bakin wakilcin da ya samu na sarkin shanun Kano Alhaji Shehu Muhammad, yayin taron wayar da kai a wani bangare na bikin ranar kansar yara ta duniya, da sashin kula da yara na Asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano, hadin gwiwa da gidauniyar tallafawa yara masu ciwon kansar ta Kano Childhood Cancer Foundation suka gudanar a harabar Asibitin yau Laraba.

Sarkin ya kuma ce akwai yadda ciwon kansar ke matukar damun yara a halin yanzu, akwai bukatar masu ruwa da tsaki su tashi tsaye wajen magance ciwon.

Da yake nasa jawabin shugaban asibitin koyarwa na Aminu Kano Farfesa Abdulrahman Abba Shehe, ya ce kasancewar yanzu haka kansar yaran karuwa take yi akwai bukatar al’umma su kara himma wajen taimakawa yaran da suke dauke da ciwon dan kawar da ita.

“Ciwon kansar yakan iya kama kowanne irin nau’in jinsi da kuma nau’in shekaru maban-ban ta a dan haka da zarar an lura da ciwon ayi gaggawar zuwa Asibiti domin samun agajin gaggawa daga likitoci domin duba saboda gudun galabaita, “in ji Farfesa Sheshe”.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa yayin taron wayar da kai din ga ciwon kansar yaran, masu ruwa da tsaki da yaran da kuma iyayen su da dama ne suka samu damar halarta.

Labarai

Kisan gillar Edo: A gaggauta nemawa mutanen da aka kashe haƙƙin su, ko mu ɗauki Mataki bisa doka – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Rights Network, ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta Kano da kuma ta jihar Edo, da gaggauta neman haƙƙin Mafarautan nan ƴan asalin jihar Kano waɗanda aka yi wa kisan gilla a garin Uromi na jihar Edo.

Daraktan ƙungiyar na ƙasa Kwamared Gambo Madaki shi ne ya bayyana wa tashar Dala FM Kano, hakan a ranar Litinin, lokacin da yake tsokaci kan kisan sama da Mafarauta 16 a jihar Edo, waɗanda suka taho daga jihar Ribas za su dawo gida Kano.

Ya ce baya ga ɗaukar matakin lalubo waɗanda suka aikata rashin imanin, akwai buƙatar a ɗauki mummunan mataki akan su don daƙile afkuwar irin hakan a gaba.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ɓatabgari ne su ka damke wadanda abin ya shafa a Uromi da ke karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas ta Jihar Edo, inda su ka ga bindigogin farauta, sai kawai su ka yanke cewa ai masu garkuwa da mutane ne, inda suka kona su da ransu a ranar Alhamis.

Lamarin dai ya jawo cece-ku-ce, inda ‘yan Najeriya da dama ke zargin gwamnati da gazawa wajen dakile irin wannan ɗaukar doka a hannu.

A cewar Gambo Madaki, baya ga batun kafa kwamiti da gwamnatin Kano ta yi akan wannan batun, ya kamata gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙara bibiyar lamarin da kan sa, don ganin an ɗauki matakin da ya dace akan kisan gillar ko kuma su ɗauki mataki bisa doka.

Continue Reading

Labarai

Mun baza jami’an mu lungu da saƙo don samar da tsaro yayin bikin Sallah a Kano – Anty Snaching Phone

Published

on

Rundunar tsaron nan da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen Waya da kuma dakile Shaye-shayen kayan maye, ta Anty Snaching Phone, ta ce ta baza jami’an ta kusan dubu ɗaya da za su shiga lungu da saƙo na jihar nan, domin samar da tsaro a yayin bukukuwan ƙaramar Sallah.

Kwamandan rundunar a nan Kano Inuwa Salisu Sharaɗa ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Freedom Radio, ya kuma ce jami’an su za su yi duk mai yiyuwa wajen daƙile ayyukan ɓata garin da ke shirin tayar da hankalin al’umma yayin bikin sallar.

“Daga cikin jami’an mu da za su samar da tsaron akwai na cikin kayan mu da kuma na farin kaya, kuma sun fara bazama guraren da mu ka tura su tun cikin kin daren Asabar ɗin nan kuma za su yi aiki cikin ƙwarewa kamar yadda suka samu horo, “in ji Inuwa”.

Sharaɗa, ya kuma ce hakan na cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar Kano ƙarkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa kulawar shugaban kwamitin karta-kwana da ke yaƙi da miyagun ɗabi’u da gwamnan ya kafa ƙarkashin Dakta Yusuf Ƙofar Mata.

Wannan dai na zuwa ne yayin da za’a gudanar da sallar Idi, ta ƙaramar Sallah a ranar Lahadin nan a Najeriya, da Jamhuriyyar Nijar da ƙasar Saudiyya, da ma wasu ƙasashen Duniya.

Continue Reading

Labarai

Za a cika Azumin Ramadan na shekarar 1446 guda 30 – Masani

Published

on

Wani masanin ilmin Taurari da ke jihar Kano a arewacin Najeriya, Mallam Nasir Falaki Al-Kanawi, ya ce za a cika Azumin Ramadan na shekarar 1446 guda 30 saboda watan Shawwal ba zai ganu ba a ranar Asabar, don da ƙarfe 11:58 na safe za a haifi jinjirin watan kuma zai faɗi 06:48 na Yamma.

Mallam Nasiru Alfaki Al-Kanawi ya bayyana hakan ne a wani taƙaitaccen jawabi da ya yi wa gidan rediyon Dala FM Kano a ranar Juma’a 28 ga watan Maris ɗin shekarar 2025.

Alfalaki ya kuma ce watan zai faɗi ne da ƙarfe 6:48 na yamma mintuna kasa da 10 kenan bayan faduwar Rana, kasancewar ranar ƙarfe 6:37 na yamma za ta fadi.

Ya ci gaba da cewa to wannan dalilin ne zai sa watan ba zai ganu ba, ko da kuwa da Na’ura ne kasancewar bai samu wadataccen hasken da zai ɗosana daga ranar ba, wanda aƙalla yana buƙatar awanni 13 zuwa 16 daga haifeshi kafin ace an iya ganinsa, Allah shi ne mafi sani Mai iko akan komai.

Continue Reading

Trending