Connect with us

Addini

Ku kara dagewa da karatun Al-kur’ani domin neman falalar Ubangiji S.W.T – Dr Abdulmudallib

Published

on

Wani malamin addinin musulunci dake nan Kano Dalka Abdulmudallib Ahmad, ya ce akwai bukatar al’umma su kara dagewa da neman ilmin karatun Al-kur’ani mai girma, domin neman falalar Allah S.W.T. a nan duniya da gobe Kiyama.

Dakta Abdulmudallib Ahmad ya bayyana hakan ne yayin bikin sauka da haddar Al-kur’ani mai girma karo na farko na makarantar Mus’ab Bin Ummair, na dalibai 36, da ta gudana a cikin unguwar Kwari Chiranci dake karamar hukumar Kumbotso a karshen makon nan.

Dakta Abdulmudallib ta kuma ce yadda littafin Al-kur’ani mai girma yake da tarin mahimmanci, akwai bukatar al’umma su kara himma wajen karanta shi da sauran litattafai.

Da yake nasa jawabin shugaban makarantar Gwani Musa Muhammad Abubakar, ya ce babban kalubalen da makarantar ke fuskanta shine rashin makewayi da kuma rashin zagayeta da Gini, wanda hakan kan haifar musu koma baya, inda ya ce akwai bukatar masu ruwa da tsaki su dage da tallafawa makarantu irin nasu domin rabauta da lada a wajen Allah S.W.T.

“Daga cikin daliban akwai 36 masu hadda, sai kuma masu Izifi 40 da kuma wadanda suka yi Izifi 30, masu kuma mata walima 6, sauran dukkaninsu maza, kuma cikin su akwai ‘yan shekaru sama da 25, da ‘yan shekaru 17, 12 da sauransu, “in ji Gwani Musa”.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa yayin bikin saukar haddar karatun Al-kur’ani mai girman, al’umma da dama ne suka samu damar halarta daga sassa daban-daban na jihar Kano.

Addini

Matsin Rayuwa: Shugabanni ku sassautawa al’umma – Babban Limamin Kano

Published

on

Babban limamin Kano, kuma wanda ya jagoranci sallar idi a babban masallacin idin na Kofar Mata a nan Kano, Farfesa Muhammed Sani Zaharaddin, ya ja hankalin shugabanni da su sassautawa al’umma, sakamakon halin matsin rayuwar da ake ciki a yanzu.

Farfesa Muhammed Sani Zaharaddin, yayi jan hankalin ne yayin huɗubar da ya gabatar, bayan kammala sallar idi da ta gudana a yau Laraba, a babban masallacin idin dake unguwar Kofar Mata a Kano.

Ya kara da cewa kasancewar al’umma na cikin mawuyacin hali da kuncin rayuwa, akwai buƙatar shugabanni su yi bakin ƙoƙarin su, domin kawo sauki daga halin matsin halin rayuwar da ake fama dashi.

Yayin sallar Idin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da mataimakin sa Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da sauran al’umma da dama ne suka halarta.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Abba Haruna Idris ya rawaito cewa, Farfesa Muhammed Sani ya kuma ja hankalin al’umma, da su koma ga Allah Subhanahu wata’ala domin samun dacewa a Duniya da gobe Ƙiyama.

Continue Reading

Addini

Ku fara duban watan Sallah daga gobe Litinin – Fadar Sarkin Musulmi

Published

on

Yanzu haka kwamitin ganin wata na Fadar mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya buƙaci al’ummar musulmin ƙasar nan da su fara duban jinjirin watan Shawwal, daga gobe Litinin, 8 ga watan Afrilun, 2024 da ake ciki.

Bayanin hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar a yammacin yau Lahadi a jihar Sokoto.

Sanarwar ta ce, duk wanda ya ga watan Shawwal, ya sanarwa Mai Gari ko Hakimi mafi kusa wanda kuma zai sanar har zuwa fadar Sarkin Musulmi.

Har ila yau, fadar Sarkin musulmin ta kuma bayar da lambobin waya waɗanda mutane za su yi amfani da su wajen ba da rahoton ganin watan Sallah ga fadar Sarkin musulmin, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta BBC ta rawaito.

Continue Reading

Addini

Iyaye ku kula da tarbiyyar ƴaƴan ku – Malama Fatima Tsakuwa

Published

on

Malamar addinin musulunci dake nan Kano Malama Fatima Ahmad Tsakuwa, ta shawarci mata da su ƙara himma wajen kula da tarbiyyar ƴaƴansu, tare da kuma zaburar da su mahimmancin yin addu’a a cikin wannan wata na Ramadana, domin rabauta da rahamar Ubangiji S.W.T.

Malama Fatima Ahmad Tsakuwa, ta bayyana hakan ne yayin taron bita ta musamman da gidauniyar Bango Charity Foundation ƙarƙashin Malama Fatima Yusif Mai tama, wanda gidauniyar ta shirya wa Mata, da bitar ta shafi watan Azumin Ramadana, akan yadda iyaye matan za su kula da ƴaƴan su, da ya gudana a ofishin ƙungiyar dake unguwar Sharaɗa a Kano.

Wakiliyar tashar Dala FM Kano, ta rawaito cewa malama Fatima Tsakuwa ta ce akwai buƙatar iyayen su ƙara lura da tarbiyyar ƴaƴansu, tare da yawaita karatun Al-kur’ani mai girma domin rabauta da falala a wajen Allah S.W.T.

Continue Reading

Trending