Connect with us

Manyan Labarai

Sarkin Kano ya ja hankalin kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa

Published

on

Mai martaba sarkin kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi kira ga ‘yan kwallon kafa da su yi koyi da kyawawan halayen kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles Ahmed Musa, wajen taimakawa al’umma musamman ma masu karamin karfi, domin rage musu wani radadin rayuwa da ke damunsu a yanzu.

Sarkin ya yi wannan kiran ne a lokacin da kyaftin din Super Eages din da takwaransa Shehu Abdullahi, bisa jagorancin Ibrahim Buba Galadima suka ziyarce shi a yau Laraba a fadar sa.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana farin cikinsa bisa wannan ziyara tare da shawartar dan wasan kwallon kafar Ahmed Musa, da ya rinka amfani da irin kayan sawar Hausawa, domin nuna al’adar Bahaushen, dan ganin ‘yan baya sun yi koyi da shiga ta kamala.

A nasa jawabin kyaftin din ‘yan wasan kwallon kafar ta kasa Super Eagles Ahmed Musa, ya ce ya je fadar sarkin ne domin neman tabarrakin sarkin, da kuma neman addu’a kan abubuwan alherin da ya sanya a gaba.

Ahmed Musa, ya ce nan bada dadewa ba zai taimakawa kananan hukumomi arba’in da hudu dake jihar nan musamman a bangaren lafiya, ta hanyar kai musu magunguna domin taimakawa al’umma.

Wakilinmu na masarautar kano, Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa, mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma karbi bakunci mai martaba sarkin Ringim dake jihar Jigawa Alhaji Sayyadi Muhmud yau a fadar sa.

Manyan Labarai

Gwamnan Kano ya ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa ta Ɗan Agundi

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa da za’ayi a mahaɗar Ɗan Agundi, da ke ƙaramar hukumar Birni, domin samarwa al’ummar jihar saukin zirga-zirga a yankin.

Da yake ƙaddamar da aikin a yammacin yau gwamnan ya ce, gwamnatin Kano za ta sanya idanu wajen ganin an kammala aikin cikin ƙanƙanen lokaci, hakan yasa yanzu gwamnatin ta tanadi duk wasu kayan aiki da ake buƙata domin gudanar da aikin cikin nasara.

Har ila yau, gwamnan Abba Kabir, ya kuma ce an samar da hanyoyin da al’umma za su bi, domin samun saukin zirga-zirga har zuwa lokacin da za’a kammala aikin baki ɗaya.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce, an samo kanfani mai inganci wanda zai yi aikin cikin ƙanƙanen lokaci, domin ci gaba da gudanar da zirga-zirga akan lokaci.

Continue Reading

Manyan Labarai

Za mu duba yiyuwar ƙarawa ma’aikatan shara kuɗin alawus ɗin su dan kyautata rayuwar su – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta duba yiyuwar ƙarawa ma’aikatan shara kuɗin alawus ɗin da ake biyan su, domin kyautata rayuwar su kasancewar abin da ake basu bai taka kara ya karya ba.

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana haka yayin ganawa da ma’aikatan kwashe shara a dakin taro na Coronation da ke gidan gwamnati jihar a yau.

Gwamna Abba ya bayyana damuwarsa bisa ƙorafe-ƙorafen da ma’aikatan shara suka yi na tsaikon da ake samu wajen biyansu kudin alawus din su tsawon watanni.

“Gwamnati za ta yi bincike domin gano inda matsalar tsaikon biyan ma’aikatan kwashe shara take da nufin magance ta cikin gaggawa, “in ji Gwamnan”.

Ya kuma ƙara tabbatar wa da ma’aikatan cewa, gwamnati za ta tabbatar kowane ma’aikacin shara an tura shi aiki kusa da gidan sa domin sauƙaƙa musu kashe kudi a wajen sufuri.

Wakilinmu na fadar gidan gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamna Abba Kabir, ya bai wa ma’aikatan tabbacin gwamnati za ta biyasu dukkanin basukan da suke bi, tare da duba yiwuwar ƙara musu kudin alawus nan bada daɗewa ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ba harkar siyasa ce ta ƙare mini ba nake yin waƙoƙin su Fatima Mai Zogale da A’isha Humaira- Rarara

Published

on

Fitaccen mawaƙin siyasar nan kuma ɗan masana’antar Kannywood Dauda Adam Kahutu Rarara, ya ce batun da wasu suke yaɗawa cewar ya yiwa Fatima mai Zogale kyautar Mota, lamarin ba gaskiya ba ne.

Dauda Rarara ya bayyana hakan ne ta cikin shirin daga Kannywood na tashar Freedom Radio da ya gudana a daren jiya Juma’a, ya kuma ce duk wanda ya bai wa kyautar Mota, Babur ko Kuɗi, ba shi ne ya ke cewa suyi hoto da mutum ba, “A,a wanda na bai wa ne da kan sa ya ke cewa mu ɗauka”.

Ko da aka yi masa tambaya akan ko yana neman muƙami ne a gwamnatin tarayya, Rarara, ya ce, Ba Muƙami yake nema a siya ba, domin inda ace muƙamin yake nema da tuni ya samu.

Har ila yau, Rarara ya ƙara da cewa ba harkar siyasa ce ta kare masa ba ya ke yin waƙoƙin su Aisha Humaira da Fatima Mai Zogale ba, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Dala FM Kano ta rawaito.

Continue Reading

Trending