Connect with us

Manyan Labarai

Tsadar Rayuwa: Mutane miliyan 18 za su samu tallafin biliyoyi daga gwamnatin tarayya

Published

on

Gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmad Tinubu, za ta rinka rabon kudi kowane wata ga wadanda suke cikin fatara.

Ministan kudi da tattalin arziki na kasa Mista Wale Edun, ne ya sanar da haka a garin Uyo.

Ministan tattalin arzikin Najeriya, Wale Edun ya shaida haka a wajen wani taro da ma’aikatarsa ta shiya a garin Uyo dake Akwa Ibom.

Da yake bayanin a ranar Laraba, Wale Edun ya ce za su samu shugaban kasa da nufin ya amince a dawo da tsarin rabon kudi a kasar.

Zuwa yanzu dai akwai mutane kusan miliyan uku da suke amfana da irin wadannan tsare-tsare da gwamnatin tarayya ta saba fito da su.

Sai dai hauhawar farashin kaya da kunci ya sa ba a jin tasirin kokarin da gwamnati take yi, wannan ya jawo zanga-zanga a Uyo.

Ya kara da cewa yanzu gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta shirya kara yawan wadanda su ke amfana da tsarin, za a tallafi wasu marasa hali, kamar yadda jaridar Legit Hausa ta rawaito.

Akalla talakawa miliyan 12 za a rika bi har gida a raba masu kyautar tsabar kudi kai-tsaye, yunkurin da mutane suka soka kwanaki.

Manyan Labarai

Gwamnan Kano ya ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa ta Ɗan Agundi

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa da za’ayi a mahaɗar Ɗan Agundi, da ke ƙaramar hukumar Birni, domin samarwa al’ummar jihar saukin zirga-zirga a yankin.

Da yake ƙaddamar da aikin a yammacin yau gwamnan ya ce, gwamnatin Kano za ta sanya idanu wajen ganin an kammala aikin cikin ƙanƙanen lokaci, hakan yasa yanzu gwamnatin ta tanadi duk wasu kayan aiki da ake buƙata domin gudanar da aikin cikin nasara.

Har ila yau, gwamnan Abba Kabir, ya kuma ce an samar da hanyoyin da al’umma za su bi, domin samun saukin zirga-zirga har zuwa lokacin da za’a kammala aikin baki ɗaya.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce, an samo kanfani mai inganci wanda zai yi aikin cikin ƙanƙanen lokaci, domin ci gaba da gudanar da zirga-zirga akan lokaci.

Continue Reading

Manyan Labarai

Za mu duba yiyuwar ƙarawa ma’aikatan shara kuɗin alawus ɗin su dan kyautata rayuwar su – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta duba yiyuwar ƙarawa ma’aikatan shara kuɗin alawus ɗin da ake biyan su, domin kyautata rayuwar su kasancewar abin da ake basu bai taka kara ya karya ba.

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana haka yayin ganawa da ma’aikatan kwashe shara a dakin taro na Coronation da ke gidan gwamnati jihar a yau.

Gwamna Abba ya bayyana damuwarsa bisa ƙorafe-ƙorafen da ma’aikatan shara suka yi na tsaikon da ake samu wajen biyansu kudin alawus din su tsawon watanni.

“Gwamnati za ta yi bincike domin gano inda matsalar tsaikon biyan ma’aikatan kwashe shara take da nufin magance ta cikin gaggawa, “in ji Gwamnan”.

Ya kuma ƙara tabbatar wa da ma’aikatan cewa, gwamnati za ta tabbatar kowane ma’aikacin shara an tura shi aiki kusa da gidan sa domin sauƙaƙa musu kashe kudi a wajen sufuri.

Wakilinmu na fadar gidan gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamna Abba Kabir, ya bai wa ma’aikatan tabbacin gwamnati za ta biyasu dukkanin basukan da suke bi, tare da duba yiwuwar ƙara musu kudin alawus nan bada daɗewa ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ba harkar siyasa ce ta ƙare mini ba nake yin waƙoƙin su Fatima Mai Zogale da A’isha Humaira- Rarara

Published

on

Fitaccen mawaƙin siyasar nan kuma ɗan masana’antar Kannywood Dauda Adam Kahutu Rarara, ya ce batun da wasu suke yaɗawa cewar ya yiwa Fatima mai Zogale kyautar Mota, lamarin ba gaskiya ba ne.

Dauda Rarara ya bayyana hakan ne ta cikin shirin daga Kannywood na tashar Freedom Radio da ya gudana a daren jiya Juma’a, ya kuma ce duk wanda ya bai wa kyautar Mota, Babur ko Kuɗi, ba shi ne ya ke cewa suyi hoto da mutum ba, “A,a wanda na bai wa ne da kan sa ya ke cewa mu ɗauka”.

Ko da aka yi masa tambaya akan ko yana neman muƙami ne a gwamnatin tarayya, Rarara, ya ce, Ba Muƙami yake nema a siya ba, domin inda ace muƙamin yake nema da tuni ya samu.

Har ila yau, Rarara ya ƙara da cewa ba harkar siyasa ce ta kare masa ba ya ke yin waƙoƙin su Aisha Humaira da Fatima Mai Zogale ba, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Dala FM Kano ta rawaito.

Continue Reading

Trending