Connect with us

Labarai

Wasu ne ke daukar nauyin masu Zanga-zanga don su bata mana suna a Kano – Hukumar Remasab

Published

on

Hukumar kwashe shara da tsaftar muhall ta jihar kano (REMASAB), tayi Allah Wadai da yadda wasu marasa kishin jihar kano suke daukar nauyi tare da tunzura waɗanda basu ji ba basu gani ba, wajen yiwa hukumar zanga-zangar bata musu suna akan rashin biyan su hakkokin su.

Shugaban Hukumar na jihar kano Alhaji Ahmadu Haruna Zago ne ya bayyana hakan da yammacin Jiya, a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishin sa.

A cewar Ɗan zago har yanzu bai wuce watanni bakwai da fara Shugabancin hukumar ba, Kuma da zuwan sa ya tantance halattattun ma’aikata tare da biyan su bashin albashin su na watanni 4.

Hakazalika, Dan Zago ya kuma ƙara da cewa, hukumarsa a shirye take wajen ɗaukar dukkan matakan da suka kamata, domin dakile waɗanda suke ƙoƙarin ɓatawa hukumar da gwamnatin jihar kano suna ta hanyar siyasantar da aikin gwamnatin jihar, kamar yadda jaridar GTR Hausa ta rawaito.

A baya-bayan nan ne dai wasu da suka kira kansu da ma’aikatan hukumar suke ta gudanar da zanga-zangar lumana a ofishin hukumar, inda suke zargin shugaban ta Ahmadu Haruna Zago, da cinye musu hakkokin su lamarin da ya sa suke ta zanga-zangar neman hakkin nasu.

Labarai

Ku guji zubar da Shara barkatai a muhallan ku – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi al’umma da su kaucewa zubar da shara a wuraren da ba’a tanade su ba, domin kaucewa yawaitar samun cutuka a tsakanin al’umma, duba da yadda ake ci gaba da tunkarar lokacin Damuna.

Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano Ambasada Ahmadu Haruna Zago, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake sanya ido kan aikin kwashe sharar da ke unguwar Zango hauran gadagi bayan Festival.

Ya ce duba da yadda Damuna ke ci gaba da tunkarowa, akwai bukatar al’umma su fahimci cewa zubar da shara barkatai ka iya haifar da cututtuka daban-daban ga iyalan su, musamman ma kasancewar sharar da ke unguwar ta Zango bayan Festival, tana tsakiyar gidajen al’umma ne da kasuwa da kuma makaranta.

Nazifi Mohammed Usman mai Duniya, da Mohammed Ibrahim wato Halifa mai Gas mazauna unguwar ta Zango ne, sun ce tarin sharar a cikin unguwar su babban ƙalubale ne a gare su, domin kuwa taruwar da tayi har ta kan shiga cikin makarantar yankin su.

Shugaban hukumar kwashe sharar Ahmadu Zago, ya kuma sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen tsafta ce birnin Kano, wajen kwashe shara daga kowane yankin, domin gudun faruwar ambaliyar ruwa sanadin sharar da ka toshe magunan ruwa a jihar Kano.

Continue Reading

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Trending