Connect with us

Manyan Labarai

Zamu sa kulle shafin duk dan Tik-Tok da ke yada badala a Kano – Hukumar Hisbah

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce yanzu haka ta shirya tsaf wajen sanyawa a kulle shafukan duk wasu ‘yan Tik-Tok din da suke yada badala.

Shugaban hukumar Hisbar na Kano Shekih Aminu Ibrahim Daurawa, ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Mahangar Zamani, na BBC Hausa.

Daurawa ya ce yanzu haka an zakulo shafuka 70 a Tik-Tok wadanda ake sanyawa idanu akan su, inda duk wanda aka samu da laifin yada badala shafin nasa ka shiga shiga cikin jerin mutanen da za’a kullewa shafin na Tik-Tok.

Wannan dai na zuwa ne bayan da hukumar Hisbar a baya-bayan nan ta yi dirar mikiya akan wasu masu amfani da shafin na Tik-Tok, wanda har ma ta gurfanar da su a gaban Kotu.

Dala FM Kano ta rawaito kamen dai da hukumae ta rinka yi a baya kama daga ‘yan Tik-Tok zuwa kuma cikin Hotal-hotal ya janyo cece-kuce a tsakanin al’umma musamman ma a shafukan sada zumunta.

Kuma daga cikin wadanda hukumar ta gurfanar a kotun akwai ‘yar Tik-Tok din nan Murja Ibrahim Kunya, da Ramlat Princesss, da dai sauransu, wadanda ta gurfanar da su bisa tuhumarsu da laifin yada badala.

Manyan Labarai

Gwamnan Kano ya ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa ta Ɗan Agundi

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa da za’ayi a mahaɗar Ɗan Agundi, da ke ƙaramar hukumar Birni, domin samarwa al’ummar jihar saukin zirga-zirga a yankin.

Da yake ƙaddamar da aikin a yammacin yau gwamnan ya ce, gwamnatin Kano za ta sanya idanu wajen ganin an kammala aikin cikin ƙanƙanen lokaci, hakan yasa yanzu gwamnatin ta tanadi duk wasu kayan aiki da ake buƙata domin gudanar da aikin cikin nasara.

Har ila yau, gwamnan Abba Kabir, ya kuma ce an samar da hanyoyin da al’umma za su bi, domin samun saukin zirga-zirga har zuwa lokacin da za’a kammala aikin baki ɗaya.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce, an samo kanfani mai inganci wanda zai yi aikin cikin ƙanƙanen lokaci, domin ci gaba da gudanar da zirga-zirga akan lokaci.

Continue Reading

Manyan Labarai

Za mu duba yiyuwar ƙarawa ma’aikatan shara kuɗin alawus ɗin su dan kyautata rayuwar su – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta duba yiyuwar ƙarawa ma’aikatan shara kuɗin alawus ɗin da ake biyan su, domin kyautata rayuwar su kasancewar abin da ake basu bai taka kara ya karya ba.

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana haka yayin ganawa da ma’aikatan kwashe shara a dakin taro na Coronation da ke gidan gwamnati jihar a yau.

Gwamna Abba ya bayyana damuwarsa bisa ƙorafe-ƙorafen da ma’aikatan shara suka yi na tsaikon da ake samu wajen biyansu kudin alawus din su tsawon watanni.

“Gwamnati za ta yi bincike domin gano inda matsalar tsaikon biyan ma’aikatan kwashe shara take da nufin magance ta cikin gaggawa, “in ji Gwamnan”.

Ya kuma ƙara tabbatar wa da ma’aikatan cewa, gwamnati za ta tabbatar kowane ma’aikacin shara an tura shi aiki kusa da gidan sa domin sauƙaƙa musu kashe kudi a wajen sufuri.

Wakilinmu na fadar gidan gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamna Abba Kabir, ya bai wa ma’aikatan tabbacin gwamnati za ta biyasu dukkanin basukan da suke bi, tare da duba yiwuwar ƙara musu kudin alawus nan bada daɗewa ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ba harkar siyasa ce ta ƙare mini ba nake yin waƙoƙin su Fatima Mai Zogale da A’isha Humaira- Rarara

Published

on

Fitaccen mawaƙin siyasar nan kuma ɗan masana’antar Kannywood Dauda Adam Kahutu Rarara, ya ce batun da wasu suke yaɗawa cewar ya yiwa Fatima mai Zogale kyautar Mota, lamarin ba gaskiya ba ne.

Dauda Rarara ya bayyana hakan ne ta cikin shirin daga Kannywood na tashar Freedom Radio da ya gudana a daren jiya Juma’a, ya kuma ce duk wanda ya bai wa kyautar Mota, Babur ko Kuɗi, ba shi ne ya ke cewa suyi hoto da mutum ba, “A,a wanda na bai wa ne da kan sa ya ke cewa mu ɗauka”.

Ko da aka yi masa tambaya akan ko yana neman muƙami ne a gwamnatin tarayya, Rarara, ya ce, Ba Muƙami yake nema a siya ba, domin inda ace muƙamin yake nema da tuni ya samu.

Har ila yau, Rarara ya ƙara da cewa ba harkar siyasa ce ta kare masa ba ya ke yin waƙoƙin su Aisha Humaira da Fatima Mai Zogale ba, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Dala FM Kano ta rawaito.

Continue Reading

Trending