Addini
Ku guji ɓatawa iyayen ku rai domin gujewa fushin Allah S.W.T – Mal. Muhktar Faragai

Malamin addinin musuluncin nan dake jihar Kano Malam Muhktar Abdullahi Faragai, ya shawarci al’umma da su kasance masu yiwa iyayen su biyayya musamman ma uwa ko da kuwa ta rasu ne bisa mahimmancin da take da shi.
Mallam Muhktar Faragai ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Duniya Labari Ce, da ya gudana yau Asabar a tashar Dala FM Kano, ya ce kasancewar Ma’aiki S.A.W. ya umarci a yiwa mahaifiya biyayya har sau uku sannan mahaifi, a dan haka akwai buƙatar ƴaƴa su rinƙa yiwa mahaifiyar su biyayya ba tare da saɓa mata ba.
Ya kuma shawarci iyaye da su kara ƙoƙari wajen sauke nauyin ƴaƴan su da Allah S.w.t. ya ɗora musu, domin ganin rayuwar ƴaƴan ta zama abar koyi a tsakanin al’umma.
“Ku guji ɓatawa iyayen ku rai domin fushin su a kan ku ka iya sanyawa ku fuskanci fushin Allah S.W.T, “in ji Mal. Muhktar”.
Ya ci gaba da cewa, “Matakin farko a biyayya shine yiwa Allah S.W.T, biyayya, da kuma Ma’aiki S.A.W, sannan biyayya ga iyaye, wanda gujewa yin hakan babbar matsala ce ga rayuwar al’umma”.
Malam Muhktar Faragai ya kuma shawarci iyaye da su guji yin fushi da ƴaƴan su, tare da kaucewa riƙe su a cikin zuciyar su saboda sun yi musu wani abu, inda ya ce mai-makon hakan yafi dacewa su yi haƙuri tare da rinƙa yi musu addu’a.

Addini
Hajji2025: Maniyyatan Najeriya 16,182, sun sauka a Saudiyya – NAHCON

Hukumar kula da Alhazai ta Najeriya, NAHCON, ta ce izuwa yanzu aƙalla maniyyatan ƙasar su 16,182, ne suka sauka a ƙasar Saudiyya, domin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2025.
Hukumar ta NAHCON, ta bayyana hakan ne da yammacin Alhamis ɗin nan a shafinta na Facebook, ta ce aƙalla jirage 40, ne suka yi jigilar maniyyatan, daga ranar juma’ar da ta gabata, da aka fara kai maniyyatan zuwa ƙasa mai tsarki.
NAHCON, ta ƙara da cewa, jirgi na ƙarshe da ya sauka a Madinah, shi ne jirgin UMZA, mai lamba UMZ3412, da ya tashi ɗauke da maniyyatan jihar Kaduna su 299, Maza 229, mata kuma 70, sai wasu na musamman su 9.

Addini
Hajjin2025: Maniyyatan Najeriya 3,644, sun sauka a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON, ta ce zuwa yanzu Maniyyatan ƙasar nan su dubu 3,644, ne suka sauka a ƙasa mai tsarki, domin sauke Farali a aikin hajjin bana, na shekarar 2025.
Kazalika, hukumar ta ce aƙalla jirage Tara ne suka yi jigilar maniyyatan, biyo bayan saukar maniyyatan jihar Oyo su 550, Maza 302, Mata kuma 248, wanda jirgin ya sauka da misalin ƙarfe 05:54 na yammacin yau Asabar.
A ranar Juma’a 09 ga watan Mayun 2025, ne dai mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shateema, da shugaban hukumar Alhazai na ƙasa NAHCON, Farfesa Abdullahi Sale Usman, da gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma, suka ƙaddamar da tashin Maniyyatan a birnin Owerri na jihar Imo.

Addini
Harsuna 20 da za’a fassara huɗubar Arfah ta 2025, ciki har da Hausa a Saudiyya.

Hukumar kula da aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya, ta ce za’a fassara huɗubar Arfah, ta shekarar 2025/1446, zuwa harsuna guda 20.
Shafin sada zumunta na Inside the Haramain Sharifai, ne ya wallafa hakan, yana mai cewa harsunan da za a fassara huɗubar ta Arfah, sune kamar haka.
1. Turanci
2. Faransanci
3. Malay
4. Urdu
5. Farisa/Farsi
6. Sinanci
7. Turkanci
8. Rashanci
9. Hausa
10. Bengali.
Sauran harsunan sune kamar haka.
11. Harshen mutanen Sweden
12. Harshen mutanen Espanya
13. Swahili
14. Amharic
15. Italiyanci
16. Fotigal
17. Bosniya
18. Malayalam
19. Harshen Filifino
20. Jamusanci.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su