Connect with us

Manyan Labarai

Tsabar rashin abinci sai dai mu dafawa yara ruwan zafi su sha – Magidanci

Published

on

Yayin da al’umma suke ci gaba da fuskantar tsadar rayuwa, wani Magidanci ya ce bisa rashin abincin da suke fama shi ya sa har ruwan zafi suke dafawa ƴaƴan su yanzu su sha.

Magidancin ya bayyana hakan ne a yayin zantwarsa da wakilinmu na ƴan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, a yau Laraba, ya ce bisa halin babu ne ma ya sa yanzu haka suka yi kwanaki biyu ba tare da sun ɗora tukunya ba a gidan su.

Tashar Dala FM Kano, ta rawaito cewa magidabcin na wannan jawabin ne a lokacin da suke bayyana zargin su akan wasu mutane da wani attajiri ya basu kayan abinci su rabawa masu ƙaramin ƙarfi a unguwar Sheka gidan Leda dake ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano, amma a zargin su mutanen sai waɗanda suka zaɓa suke baiwa tallafin kayan abincin, mai-makon dukkan mabuƙata.

Magidancin, ya ce kayan abincin da Attajirin yake bayar wa a rarraba sun haɗar da Masara, da Shinkafa, da kuma Taliya da dai sauransu, lamarin da suka yi kira ga Attajirin da kuma sauran masu hali da su tallafawa masu ƙaramin ƙarfi ta yadda za’a rage musu wani raɗaɗi da yake damun su na ya da kullum.

Manyan Labarai

Zamu ƙone duk kayayyaki marasa inganci da muka kama da zarar an gama shari’u – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta ƙone dukkanin kayayyaki marasa inganci da ta kama, da zarar an kammala dukkanin shari’un da suke a gaban Kotu.

Kwamishinan ma’aikatar ciniki da masana’antu, Adamu Aliyu Kibiya, ne ya tabbatar da hakan, a yayin wata ziyara ta musamman da ya kai hukumar kula da ingancin kayayyaki ta jihar Kano, a yammacin yau Alhamis.

Amadadin Kwamishinan babban sakataren ma’aikatar, Muhammad Yusuf Ɗan-duwa, ya ce, da zarar an kammala Shari’un da masu kayan za’a ƙone su baki ɗaya.

“A bisa al’adar ma’aikatar ciniki da masana’antu, dama duk sabon Kwamishina idan ya zo yana ziyarartar hukumomin da suke da jiɓi da ma’aikatar domin duba irin aikace-aikacen su da sauran abinda ba’a rasa ba, hakan ya sa ma Kwamishinan ya ziyarci hukumar a yau, “in ji Ɗan-duwa”.

 

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, babban sakataren ya ƙara da cewa, ziyarar da Kwamishinan ciniki da masana’antun Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, ya kai hukumar kula da ingancin kayayyakin, itace ta farko.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta ci gaban mai haƙan rijiya ne – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights, ta ce ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta, ci gaban mai haƙan rijiya ne, domin ba zai magancewa ma’aikatan matsalolin su ba.

Daraktan ƙungiyar reshen jihar Kano Alhaji Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da wakilinmu na ƴan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, a yau Laraba, lokacin da yake tsokaci a kan bikin ranar ma’aikata da ake gudanarwa yau a Najeriya.

Ya kuma ce kasancewar ƙarin albashin ba zai ragewa ma’aikatan wata damuwa ba, sai dai ma ya tunzura ma’aikatan, bai kamata ƙungyoyin ƙwadago su amine da tsirarun ƙarin ba.

“Matukar gwamnatin tarayya za ta rinƙa tunzura ma’aikata da irin wannan tsirarun albashin babu makawa zamu gurfanar da ita a gaban kotu, “in ji Galadanci”.

Umar Sani ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta lalubo sabbin hanyoyi da za’a ƙarawa ma’aikatan albashi mai tsoka wanda zai rinƙa magance musu wasu matsalolin su na yau da kullum.

Har ila yau, suma ƙungiyoyin ƙwadago a ƙasar nan, sun yi fatali da ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta da kashi 25 cikin ɗari, da kuma kashi 35 a cikin ɗari.

Ƙungiyoyin ƙwadago da dama na NLC, da TUC, da sauran ƙungiyoyi ne suka gudanar da taron ranar ma’aikan a sassan jahohin ƙasar nan.

Continue Reading

Manyan Labarai

Kayan aikin ginin da ya ruftawa magina a Kuntau ba masu inganci ba ne – Cibiyar masu Taswirar Zane-zanen Muhalli

Published

on

Cibiyar masu tasawirar zane-zanen muhalli ta ƙasa reshen jihar kano, tayi Allah wa dai da kayan da akayi wani ginin Bene da shi mai hawa uku, da ya faɗo akan wasu magina a cikin unguwar Kuntau da ke yankin karamar hukumar Gwale a jihar kano.

Mataimakin shugaban ƙungiyar na kasa Arct Ali Mukhtar, ne ya bayyana hakan a lokacin da cibiyar takai ziyara wajen da al’amarin ya faru.

Ya ce dukkanin kayan da aka yi aikin ginin benen da su ba masu inganci ba ne.

A nasa jawabin shugaban cibiyar a nan nano Arct Bashir Hassan Hanga, kira ya yi ga gwamnatin jihar kano, da ta hana duk masu irin wannan gine-gine ba tare da sahalewar hukumar tsara birane ba wato Knupda, ta kuma ɗauki mataki akan mamallakin wannan gini da ya rushe a kan maginan.

Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa dukkanin tawagar cibiyar tsara gine-ginen, sun ce za su ziyarci asibitin Murtala Muhammad, domin duba mutanen da gini ya fadowa da kuma zuwa ta’aziya gidan waɗanda suka rasu su uku.

Continue Reading

Trending