Connect with us

Manyan Labarai

Gwamnatinmu tayi tanadi mai kyau domin tallafawa al’umma : Abba Kabir Yusif

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta ce tayi tanadi mai kyau domin tallafawa al’umma a cikin watan Azumin nan da muke ciki.

Gwamnan Kano Engr Abba Kabir Yusif ne ya bayyana hakan yayin taron walimar shan ruwa da Gwamnan ya jagoranta tare da ma’aikatan fadar Gwamnatin Kano a daren Asabar din nan.

Engr Abba Kabir Yusif ya ce, suna sane da halin da al’umma ke ciki na matsin halin rayuwa, hakan yasa Gwamnatin ta himmatu wajen tallafawa al’umma da kayan abinci kamar yadda aka fara rabawa kananan hukumomi 44 da suke a fadin jihar ta Kano.

Abba Kabir Yusif ya kara da cewa, a ranar Lahadin nan ma’aikatan fadar Gwamnatin na Kano zasu rabauta da rabon kayan abinci da suka hadar da Shinkafa, Taliya, Mai na Girki da kudade duk domin tallafawa ma’aikatan fadar Gwamnatin Kano don ciyar da iyalan su.

Wakilinmu na fadar Gwamnatin Kano Abba Haruna Idris ya rawaito cewar, Gwamnan Kano Engr Abba Kabir Yusif yayi kira ga ma’aikatan fadar Gwamnatin Kano da su ci gaba da bawa Gwamnati hadin kai wajen gudanar da aiki kamar yadda suka saba.

Baba Suda

Gwamnatin Kano ta musanta labarin da ke cewa za ta saka kafar Wando daya da Sojojin Baka

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo na cewa za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishinan yada labaran jihar Kwamred Ibrahim Waiya shi ne ya bayyana hakan lokacin wani taron karawa juna sani da hukumar kula da kafafen yada labarai NBC ta shirya a yau Alhamis.

 

Yace gwamnatin Kano za ta hada kai da Yan siyasa masu magana a Rediyo da aka fi Sani da Sojojin Baka, domin tsaftace harkokin siyasar Kano.

 

Haka kuma kwamishinan ya musanta labarin da ke cewa Gwamnatin Kano za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishina Waiya ya kuma ce za su hada kai da kafafen yada labarai domin Kara kawo tsafta a harkokin siyasar Kano.



Continue Reading

Manyan Labarai

Da Ɗumi-Ɗumi! Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar Rivers da mataimakin sa da ƴan majalisar jihar na watanni 6.

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara, da mataimakiyar sa Mrs. Ngozi Odu, har na tsawon watanni 6.

Shugaba Tinubu ya bayyana daukar matakin ne a cikin wani taƙaitaccen jawabin sa da ya gabatar a cikin daren Talatar nan, ya ce ya yi amfani da damar da kundin tsarin mulki ya ba shi wajen sanya wannan doka wacce ta kwace mulkin jihar daga hannun gwamnan jihar Siminalayi Fubara da mataimakin sa har sai lamura sun dawo dai-dai a jihar.

Kazalika, shugaba Tinubu ya kuma bayyana dakatar da dukkanin ƴan majalisar dokokin jihar suma na tsawon watanni shidan, tare da sanya dokar ta ɓaci a jihar.

Wannan dai na zuwa ne biyo bayan rikicin siyasar da ya daɗe da kunno kai a tsakanin gwamna Fubara da ministan birnin tarayya Abuja Nyesome Wike, al’amarin da ya janyo takun saƙa tsakanin sa da ƴan majalisar dokokin jihar.



Continue Reading

Manyan Labarai

Isra’ila ta kashe sama da mutane 200 bayan karya yarjejeniyar tsagaita Wuta a Gaza

Published

on

Isra’ila ta keta yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, tare da ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Falasdinawa.

Jaridar TRT Hausa ta ruwaito cewa, aƙalla Isra’ila ta kashe fiye da mutum 200 tare da jikkata ɗaruruwa a yayin da ake ci gaba da kai gawawwaki asibiti, kamar yadda majiyoyin wani asibiti a yankin Gaza suka bayyana.



Continue Reading

Trending