Connect with us

Labarai

Zamu baza jami’an mu a cikin unguwanni domin kakkaɓe ɓata gari yayin tafiya sallar Tarawi a Kano – Ƙungiyar Bijilante

Published

on

Yayin da ake cikin Azumin watan Ramadan na tara a yau Talata, Ƙungiyar sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano, ta buƙaci haɗin kan al’ummar gari, domin samun damar kakkaɓe bata garin da suke addabar mutane a cikin unguwanni lokacin da ake tafiya sallar dare ta Tarawi, wato Asham.

Jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar Bijilanten a matakin jahar Kano, kuma kwamandan ta na ƙaramar hukumar Fagge Usman Muhammad Ɗan Daji, ne ya bayyana hakan yayin zantwarsa da gidan rediyon Dala FM, ya ce za su ƙara baza jami’an su, domin samar da tsaro ga al’umma a cikin unguwanni dan ganin an kawar da ɓata garin da suke damun jama’a.

“Mun samu ƙorafe-ƙorafe daga wajen al’umma musamman ma a ƙananan hukumomin birnin Kano, kan yadda ake samun wasu matasa suna amfani da lokacin tafiya sallar Tarawi, (Asham) suna yiwa mutane sace sace a cikin gidaje; zamu ɗauki tsauttsauran mataki akan masu damun mutane, “in ji Ɗan Daji”.

Wakilin tashar Dala FM Kano, ya rawaito cewa, Usman Ɗan Daji, ya kuma shawarci al’umma cewar duk lokacin da suka ga faruwar wani baƙin al’amari su sanar da jami’an tsaro, da kuma ofishin ƴan ƙungiyar Bijilanten, domin sanarwa wajen ganin an ɗauki matakin da ya dace.

Labarai

Wahalar Fetur: Fadar shugaban ƙasa kiyi wani abu dan mutane su samu sauƙi – Ƙungiyar Nothern Concern Soliderity

Published

on

Yayin da al’umma ke ci gaba da fuskantar wahalar man fetur a ƙasar nan, ƙungiyar da ta damu da abubuwan da suka shafi arewacin ƙasar nan ta Northern Concern Soliderity, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi abinda ya dace dan ganin mutane sun samu wani sauƙi.

Babban jami’in gudanarwar ƙungiyar, kuma sakataren riƙo na zauren gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya, Kwamared Saddat Usman Maiyaƙi, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, lokacin da yake nuna takaici kan irin wahalar da al’ummar ƙasa suke sha wajen shan man Fetur a gidajen man.

Ya ce duba da halin matsin rayuwar da al’umma suka samu kansu a ciki, akwai buƙatar shugabanni da masu ruwa da tsaki su kawo ƙarshen wahalar man Fetur ɗin da aka fama da ita.

Kwamared Saddat Maiyaƙi, ya kuma haƙurƙurtar da al’ummar ƙasar nan kan halin ƙuncin rayuwar da suka samu kai a ciki, inda ya yi fatan komai ya zo karshe cikin ƙanƙanen lokaci.

Continue Reading

Labarai

Abin takaici ne yadda ake fuskantar ƙarancin ruwan Sha a sassan jahar mu – Gwamnan Kano.

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya nuna rashin jin daɗin sa bisa yadda ake samun ƙarancin Ruwan Sha, a wasu daga cikin sassa jihar Kano.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai, a lokacin a ya kai ziyarar gani da ido, matatar Ruwa da ke Tamburawa a yammacin yau Juma’a, a ƙokarin sa na na gyara ɓangaren ruwan a cikin garin Kano.

Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kuma sha alwashin tabbatar wa al’umma cewar, gwamnatin sa za ta yi aiki ba dare ba rana domin tabbatar da isasshen ruwan Sha ga al’ummar jihar Kano.

Gwamnan ya ƙara da ce a lokacin da suka zo ba sufi mako biyu ba suka samar da ingantaccen Ruwan sha, wanda ya rinƙa shiga cikin lunguna da Sako na sassan jihar.

Continue Reading

Labarai

Ƙaramar hukumar Tofa ta dakatar da sayar da Burtalai a wasu garuruwan ta

Published

on

Biyo bayan kokawar da wasu Fulani Makiyaya suka yi kan yadda wasu suka gididdiba burtalai yayin da aka siyarwa Manoma, a garuruwan Yanoko da Gajida da kuma Dindere, yanzu haka ƙaramar hukumar Tofa ta dakatar da taɓawa, ko kuma sayar da dukkanin Burtalan kiwon shanun ba tare da ɓata lokaci ba.

Shugaban riƙon ƙaramar hukumar ta Tofa Abubakar Sulaiman Mai Rogo, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da aka aikowa Dala FM Kano, a ranar Alhamis.

Mai Rogo, ya kuma ce ƙaramar hukumar ba ta da hannu a kan taɓa dukkan guraren, a dan haka sun dakatar da dukkanin yunƙurin taɓa Burtalan har sai shugabanni na kwamitin ƙasa sun kammala bincike wanda yanzu haka ake ci gaba da yi.

Da yake nuna jin daɗin sa kan matakin dakatarwar, amadadin Fulanin garuruwan, shugaban ƙingiyar Funali Makiyaya ta Gan Allah, Ahmad Shehu Gajida, yabawa gwamnatin jihar Kano, da kuma ƙaramar hukumar ta Tofa ya yi, bisa karɓar koken su da suka akai.

A baya-bayan nan ne dai a zantawar Dala FM Kano, da wasu Funalani Makiyaya mazauna garuruwan Yanoko da Gajida da kuma Dindere, suka koka kan yadda aka gididdiba burtalan a yankunan nasu aka siyarwa manema, lamarin da suka ce ka iya sawa su rasa guraren da za suyi kiwon shanun su wanda hakan babbar barazana ce a gare su.

Continue Reading

Trending