Manyan Labarai
Akwai rashin adalci kan dakatar da Sanata Abdul Ningi, zamu bibiyi al’amarin – Human Rights

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta ƙasa da ƙasa ta International Human Rights Commission, ta soki lamirin majalisar dattawan ƙasar nan, kan dakatar da sanatan Bauchi ta Tsakiya Sanata Abdul Ahmed Ningi, har na tsawon watanni uku.
Daraktan ƙungiyar a ƙasar nan Kyaftin Abdullahi Bakoji Adamu mai ritaya, ne ya bayyana hakan a yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano, a yammacin Asabar ɗin nan, ya ce akwai rashin adalci a fagen dakatar da Sanata Ningi, a dan haka ne ma suke kira da’a dawo da shi kan kujerar sa.
Idan dai ba’a manta ba tun a ranar Talata 12 ga watan Maris da muke ciki na shekarar 2024, ne majalisar dattawan ƙasar nan ta dakatar da Sanata Abdul Ahmed Ningi, daga ayyukan majalisar har zuwa watanni uku masu zuwa, biyo bayan zargin sa da zubar da kimar majalisar.
Sanata Abdul Ningi, dai ya zargi majalisar da yin cushe a kasafin kuɗin 2024, a hirar sa da sashen Hausa na BBC, lamarin da bai yiwa majalisa daɗi ba inda har ta kafa wani kwamiti, a ranar gabatar da sakamakon binciken kwamitin ne ma sanatocin suka kaɗa ƙuri’ar dakatar da Ningi.
Kyaftin Abdullahi Bakoji mai ritaya, ya kuma ce hedikwatar ƙungiyar su ta basu wa’adin kwanaki biyar da su bibiyi abinda majalisa suka yi akan dakatar da Sanata Ningi, daga bisani su rubuta su sanar da sakamakon binciken su ga hedikwatar ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ɗin.
“Mun fashimci cewar akwai rashin adalci kan dakatar da Ningi, saboda ya faɗi gaskiya wanda hakan ya nuna cewar ba wanda ya yi laifi ake hukunta wa ba, face wanda ya gano laifin wanda hakan babban kuskure ne da ba zai haifar wa da Najeriya Ɗa mai ido ba, “in ji Bakoji”.
Wakilin gidan rediyon Dala FM Kano ya rawaito cewa, Bakoji ya ci gaba da cewa, matuƙar irin hakan ya ɗore babu makawa Najeriya tana shirin wargajewa ke nan.

Manyan Labarai
Ba za mu amince da yadda ake yawan kai wa jami’an mu hari ba a Kano – KAROTA

Hukumar kula da zirgar-zirgar ababen Hawa ta jihar Kano, KAROTA, ta ce ba za ta lamunta da yadda ake yawan kai wa jami’anta farmaki ba, na ba gaira babu dalili yayin da suke gudanar da ayyukan su.
Shugaban Hukumar KAROTA, a Kano, Injiniya Faisal Mahmud Kabir, ne ya yi wannan gargaɗin ta cikin sanarwar da kakakin hukumar Abubakar Ibrahim Sharada ya aikowa tashar Dala FM Kano, a ranar Laraba 09 ga watan Afrilun 2025.
“Hakan na zuwa ne biyo bayan wani mummunan hari da wasu mutane da ke cikin baburin Adai-daita sahu suka kai wa jami’an na mu yayin da suke tsaka da aikinsu a titin da ke dab da gidan Buhari kan hanyar zuwa Gidan Zoo, “in ji shi“.
Sanarwar ta ce, tunda farko an tsayar da wani mai baburin Adai-daita Sahu ne inda yaƙi tsayawa, sai kawai aka hango mai ɗan sahun ya naushi jami’in karotar.
Sai dai a ta bakin Shugaban kungiyar ‘Yan Adai-daita Sahu a jihar Kano, ya ce waɗannan mutane ba halattattun ‘Yan Adai-daita Sahu ba ne, sun dai fake da sana’ar su dan aikata ta’addanci.
Daga bisani dai jami’n hulɗa da jama’a na Hukumar Koratar, Abubakar Ibrahim Sharada, ya ce hukumar za ta ɗauki tsattsauran mataki akan lamarin, don kare afkuwar irin hakan a gaba.
Hukumar ta ce duk wanda ya ga faruwar wani abu da ya shafe ta, ko kuma ƙorafe-ƙorafe, zai iya kiran waɗannan lambobin domin sanar da ita, da suka haɗar da 09015709449 ko 08059689422 ko kuma 08067311520.

Manyan Labarai
Ɗan Bijilante ya rasa ransa bisa arangamar su da wasu ƴan Daba a Kano

Ƙungiyar sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamandan ta Ubale Barau Muhammad Badawa, ta tabbatar da rasuwar guda daga cikin jami’in ta mai suna Suraj Rabi’u mazaunin Jaba da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar, sakamakon arangama da ƴan Daba.
Mai magana da yawun ƙungiyar Bijilante na jihar Kano, kuma Kwamandan ta na ƙaramar hukumar Fagge, Usman Muhammad Ɗan Daji, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM Kano a ranar Lahadi.a
“Jami’in Bijilanten namu ya rasa ran nasa ne sakamakon arangama da suka yi da wasu Ƴan Daba yayin gudanar aikinsu a ranar Idin ƙaramar Sallah, inda ƴan dabar suka soke shi da Ɗanbida a Ƙirji da bayansa, wanda ya yi sanadiyar rasuwarsa, “in ji Usman”.
Ya kuma ce, an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi mai suna Usman Sharif mazaunin ƙaramar hukumar Dala, kuma tuni aka miƙa shi hannun jami’an tsaro.
Usman Ɗan daji, ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan jami’in nasu ya gafarta masa.

Manyan Labarai
An ga watan ƙaramar Sallah a Najeriya – Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya, inda za a yi karamar Sallah gobe Lahadi.
Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a yayin jawabin da ya gabatar a cikin daren Asabar ɗin nan, ya ce sun samu rahotannin ganin watan ne daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce daga cikin guraren da aiko musu da ganin jinjirin watan na Shawwal akwai Zazzau, da kuma daga Sarkin Dutse, da Arugungu, da kuma Shehun Borno, da dai sauran gurare daban-daban na Najeriya.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su gabatar da bikin sallar cikin kwanciyar hankali, tare da taimaka wa mabuƙata.
Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, biyo bayan sanarwar fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, ya kasance ranar Lahadi take 1 ga watan Shawwal na shekarar 1446, wato ranar ƙaramar Sallah.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su