Connect with us

Addini

Ku fara duban watan Sallah daga gobe Litinin – Fadar Sarkin Musulmi

Published

on

Yanzu haka kwamitin ganin wata na Fadar mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya buƙaci al’ummar musulmin ƙasar nan da su fara duban jinjirin watan Shawwal, daga gobe Litinin, 8 ga watan Afrilun, 2024 da ake ciki.

Bayanin hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar a yammacin yau Lahadi a jihar Sokoto.

Sanarwar ta ce, duk wanda ya ga watan Shawwal, ya sanarwa Mai Gari ko Hakimi mafi kusa wanda kuma zai sanar har zuwa fadar Sarkin Musulmi.

Har ila yau, fadar Sarkin musulmin ta kuma bayar da lambobin waya waɗanda mutane za su yi amfani da su wajen ba da rahoton ganin watan Sallah ga fadar Sarkin musulmin, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta BBC ta rawaito.

Addini

Hajji2025: Maniyyatan Najeriya 16,182, sun sauka a Saudiyya – NAHCON

Published

on

Hukumar kula da Alhazai ta Najeriya, NAHCON, ta ce izuwa yanzu aƙalla maniyyatan ƙasar su 16,182, ne suka sauka a ƙasar Saudiyya, domin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2025.

Hukumar ta NAHCON, ta bayyana hakan ne da yammacin Alhamis ɗin nan a shafinta na Facebook, ta ce aƙalla jirage 40, ne suka yi jigilar maniyyatan, daga ranar juma’ar da ta gabata, da aka fara kai maniyyatan zuwa ƙasa mai tsarki.

 

NAHCON, ta ƙara da cewa, jirgi na ƙarshe da ya sauka a Madinah, shi ne jirgin UMZA, mai lamba UMZ3412, da ya tashi ɗauke da maniyyatan jihar Kaduna su 299, Maza 229, mata kuma 70, sai wasu na musamman su 9.

Continue Reading

Addini

Hajjin2025: Maniyyatan Najeriya 3,644, sun sauka a Saudiyya

Published

on

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON, ta ce zuwa yanzu Maniyyatan ƙasar nan su dubu 3,644, ne suka sauka a ƙasa mai tsarki, domin sauke Farali a aikin hajjin bana, na shekarar 2025.

Kazalika, hukumar ta ce aƙalla jirage Tara ne suka yi jigilar maniyyatan, biyo bayan saukar maniyyatan jihar Oyo su 550, Maza 302, Mata kuma 248, wanda jirgin ya sauka da misalin ƙarfe 05:54 na yammacin yau Asabar.

A ranar Juma’a 09 ga watan Mayun 2025, ne dai mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shateema, da shugaban hukumar Alhazai na ƙasa NAHCON, Farfesa Abdullahi Sale Usman, da gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma, suka ƙaddamar da tashin Maniyyatan a birnin Owerri na jihar Imo.

Continue Reading

Addini

Harsuna 20 da za’a fassara huɗubar Arfah ta 2025, ciki har da Hausa a Saudiyya.

Published

on

Hukumar kula da aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya, ta ce za’a fassara huɗubar Arfah, ta shekarar 2025/1446, zuwa harsuna guda 20.

Shafin sada zumunta na Inside the Haramain Sharifai, ne ya wallafa hakan, yana mai cewa harsunan da za a fassara huɗubar ta Arfah, sune kamar haka.

1. Turanci
2. Faransanci
3. Malay
4. Urdu
5. Farisa/Farsi
6. Sinanci
7. Turkanci
8. Rashanci
9. Hausa
10. Bengali.

Sauran harsunan sune kamar haka.

11. Harshen mutanen Sweden
12. Harshen mutanen Espanya
13. Swahili
14. Amharic
15. Italiyanci
16. Fotigal
17. Bosniya
18. Malayalam
19. Harshen Filifino
20. Jamusanci.

Continue Reading

Trending