Connect with us

Manyan Labarai

Za’a ɗauki mataki akan duk wanda yake da hannu Gini ya ruftawa mutane a Kuntau – Ƙaramar hukumar Gwale.

Published

on

Yayin da wani ginin Bene mai hawa biyu ya danne aƙalla sama da Leburori goma a unguwar Kuntau kusa da KEDCO, a safiyar yau Juma’a, Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Gwale Abubakar Mu’azu Mojo, ya ce za’a ɗauki mataki akan dukkan wanda aka samu da laifi har al’amarin ya faru.

Abubakar Mu’azu Mojo, ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da manema labarai, yayin da ya ziyarci gurin da lamarin ya faru lokacin da ake ci gaba da aikin ceto mutanen.

Mojo, ya kuma ce babu makawa za’a ɗauki matakin doka akan duk wanda aka samu da hannu akan faruwar lamarin, kama daga ɗan kwangilar da aka bai wa aikin ginin, zuwa kuma mamallakin gidan.

Rahotanni sun bayyana cewa zuwa tsakar ranar yau aƙalla mutane bakwa aka ciro daga ƙasan ginin shida daga cikin su basa iya motsa jikin su, yayin da hukumomi suka ci gaba da gudanar da aikin ceto sauran mutanen da ginin ya danne.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Manyan Labarai

Gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan dokar gwajin lafiya kafin aure

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu a kan dokar da za ta wajabta yin gwajin lafiya gabanin aure a faɗin jihar ta kano baki ɗaya.

A cikin wata sanarwa da ta samu sa hannu kuma ta fito daga ofishin babban daraktan yada labarai na gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa, ta ce an bijiro da dokar gwajin lafiya ne kafin aure, domin rage yawan yaran da ake haihuwa ɗauke da wasu cututtuka da ake iya ɗauka ko kuma gadonsu daga iyaye, kamar irin cutar Sikila da HIV da kuma ciwon hanta.

Rahotanni sun bayyana cewa, hakan na nufin cewa daga yanzu babu wani aure da za’a ɗaura a jihar har nan sai an gabatar da takardar sakamakon gwajin ƙwayoyin halittun gado, da na cutar hanta (Hepatitis B da C), da na ƙwayar cuta mai karya garkuwar jiki wato (HIV).

Gwamna Abba Kabir ya sanya hannu kan dokar ne, bayan kwashe mako guda da majalisar dokokin jihar ta amince da ita.

Sannan kuma dokar ta haramta tsangwamar mutane masu fama da cuta mai karya garkuwar jikin ɗan adam wato HIV, ko kuma cutar amosanin Jini Sikila, ko cutar Hanta, da sauran su.

Har ila yau, sanarwar ta ce dokar za ta fara aiki ne, daga ranar 13 ga watan Mayu na shekarar 2024 da ake ciki.

Continue Reading

Manyan Labarai

Lauya ya nemi a biya Abduljabbar Kabara Naira miliyan 20 saboda ɓata masa lokaci da aka yi.

Published

on

Babbar kotun jaha a ɓangaren ɗaukaka ƙara ƙarƙashin masu Shari’a Aisha Mahamud, da Nasir Saminu, sun sanya ranar 9 ga wannan watan da ake ciki dan ci gaba da sauraron daukaka karar, da Abduljabbar Nasir Kabara ya shigar.

A zaman kotun na yau lauyan Abduljabbar, Barrista Yusuf Sadik, ya shaidawa kotun cewar a shirye suke a fara sauraron daukaka karar.

Sai dai lauyan gwamnati ya bayyana cewar basu shirya ba dan haka a sanya wata ranar.

Lauyan Abduljabbar ya shaidawa kotun cewar sun bai wa lauyoyin gwamnati takardun bayaninsu tun a watan 2 da ya gabata, dan haka a biya Abduljabbarun Naira miliyan 20 saboda ɓata masa lokaci da aka yi.

Sai dai lauyan gwamnati ya yi suka an kuma duba lokacin da aka bada takardun a watan uku ne dan haka wannan lauya ya janye rokonsa.

Daga nan ne kotun ta sanya ranar 9 ga watan nan na Mayu da ake ciki, an kuma umarci lauyan gwamnati da ya yi martani idan yana da shi kafin wannnan rana.

Wakilinmu na Kotu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa, Abduljabbar Nasir Kabara dai ya daukaka karar ne dan kalubalantar hukuncin kutun shari’ar muslunci ta kofar kudu, wadda ta yanke masa hukuncin kisa ta hanya rataya bisa samunsa da laifin ɓatanci.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gobara ta ƙone tarin kayayyaki a gidan tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau

Published

on

Wata Gobara ta tashi a Gidan Tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau dake Mudubawa a yankin Karamar hukumar Nassarawa, inda ta ƙone wasu kayayyaki a ɗakin matar sa waɗanda zuwa yanzu ba’a ƙayyade ba.

Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta faro ne daga ɗakin Girki na matar tsohon gwamnan Hajiya Halima Shekarau, tun yammacin jiya Lahadi.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, mai magana da yawun tsohon Gwamnan Malam Sule Ya’u Sule, ya ce gobarar ta shafi iya daki ɗaya ne a cikin gidan dake Munduɓawa.

A nasa ɓangaren kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, PFS Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce da zarar sun kammala tattara alƙaluma da bincike, zai magantu a nan gaba.

Continue Reading

Trending