Connect with us

Manta Sabo

Abduljabbar Kabara da lauyansa sun ƙauracewa zaman kotu kan ɗaukaka ƙarar da ya yi

Published

on

Babbar kotun jaha a ɓangaren ɗaukaka ƙara ta ci gaba da sauraron ɗaukaka ƙarar da Abduljabbar Nasir Kabara ya yi, yana ƙalubalantar hukuncin kisan da babbar Kotun shari’ar Muslunci ta ƙofar Kudu, ta yanke masa a baya.

A zaman kotun na yau lauyan Abduljabbar da shi kansa Abduljabbar ɗin basu halarci zaman kotun ba.

Lauyan gwamnati Barista Bashir Sale ya roki kotun da ta faɗaɗa musu lokaci domin suyi suka akan rokon da Abduljabbar din ya yi.

A baya dai Abduljabbar ya yi suka akan cewar kwafin shari’ar da kotun kofar Kudu ta bayar bai cika ba.

A yau lauyan gwamnati ya roki a bashi dama yayi martani akan wacan roko kotun kuma kotun ta amince da rokonsa an kuma abince da a bawa lauyoyin gwamnati kwafin sharia kotun ta sanya ranar 14 ga wannan watan dann ci gaba

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Manta Sabo

Abduljabbar Kabara ya dakatar da lauyan da yake kare shi a kotun ɗaukaka ƙara.

Published

on

Babbar kotun jaha ɓangaren ɗaukaka ƙara ta ɗage sauraron ɗaukaka ƙarar da malam Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara ya yi a gabanta.

Hakan ya biyo bayan wata takarda da Abduljabbar ɗin ya aikewa kotun wadda ya sanarwa da kotun cewar ya janye lauyansa daga cikin shari’ar.

Kotun ta ɗage shari’ar har zuwa lokacin da malamin zai gabatar da wani lauyan a gaban ta.

Malam Abduljabbra dai ya ɗaukaka karar ne akan hukuncin kisan da kotun shari’ar muslunci ta kofar kudu ta yanke masa a baya bisa samun sa da laifi.

Babbar kotun shari’ar Muslunci ta kofar kudu ta yankewa Abduljabbar hukunci kisa ta hanyar rataya sakamakon kama shi da laifin batanci, sai dai kasancewar malamin bai yadda da hukuncin ba hakan yasa ya ɗaukaka ƙararar.

Yayin zaman Kotun na yau Laraba 15-05-2024 karkashin jagorancin Mai Shari’a Nasir Saminu, an gabatar da takardar dakatar da lauyan wadda Malamin ya sanya wa hannu a ranar 10-05-2024.

Sai dai lauyoyin Gwamnati sun nemi kotu ta kori neman, da bukatar gyara a kan bayanan da Kotun baya ta yi amfani da su wajen yanke masa hukuncin kisa.

Sai dai kuma kotun ba ta karbi rokon lauyoyin Gwamnatin ba, kamar yadda wakilinmu na Kotu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito.

Continue Reading

Manta Sabo

Wata Kotu a Kano ta ci gaba da sauraron ƙarar da aka shigar da ƙaramar hukumar Gwale da wani mutum

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 15 da ke zamanta a Mila Road a jihar Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Sunusi Ado Ma’aji, ta ci gaba da saurarar karar da al’ummar unguwar Dorayi Baba unguwar jakada suka shigar da karamar hukumar Gwale, da wani mutun mai suna Alhaji Ibrahim Ƴan Shana.

Tunda fari dai mutanan unguwar sun shigar da karar ne suna zargin karamar hukumar ta Gwale, da cefanar wa Ibrahim ‘yan Shana wani fili mallakin al’ummar unguwar na makaranta, lamarin da su garzaya gaban kotun tun a shekarar 2023, a lokacin shugabancin ƙaramar hukumar da ya shuɗe, suna rokon da ta dawo musu da shi domin a gida makaranta a yankin nasu.

Sai dai a zaman kotun na yau bangaren wadanda ake kara na daya wato karamar hukumar Gwale sun gaza gabatar da martanin su akan karar, inda suka roki kotun da ta sanya wata ranar domin gabatar da martanin nasu.

Wakilimmu Mu’az Musa Ibrahim ya rawaito cewa mai shari’ar ya sanya ranar 5 ga watan Yunin shekarar 2024 domin ci gaba da shari’ar.

Continue Reading

Manta Sabo

Kotu ta aike da matashin da ake zargi da kashe matar sa gidan yari a Kano

Published

on

Kotun majistret mai lamba 29 karkashin jagorancin mai Shari’a Talatu Makama, ta aike da wani matashi gidan gyaran hali.

Matashin mai suna Adamu Ibrahim ana zargin sa ne da laifin hallaka mai ɗakinsa ta hanyar kwantara mata dutsen Guga, a fuskarta a can garin kwanar ɗan gora.

Ƙunshin tuhumar ya bayyana cewar, tun a ranar 9 ga watan 4, wani mai suna Idris Adamu yaje caji ofishin ƴan sanda inda ya shigar da kara akan cewar Adamu Ibrahim ya kashe mai ɗakinsa wadda kuma kanwa ce a wajen mai ƙarar Idris Adamu.

Bayan fitowa daga kotun ne wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’ila, ya zanta wanda ake zargi wanda ya ce tsautsayinya sanya shi aikata hakan.

Shima dan uwan marigayiyar ya bayyana matsayarsu, inda ya roƙi kotun da ta yi musu adalci a shari’ar.

Kotun dai ta sanya ranar 17 ga watan gobe dan a kara gabatar da shi a gaban ta domin ci gaba da shari’ar.

Continue Reading

Trending