Connect with us

Manta Sabo

Abduljabbar Kabara ya dakatar da lauyan da yake kare shi a kotun ɗaukaka ƙara.

Published

on

Babbar kotun jaha ɓangaren ɗaukaka ƙara ta ɗage sauraron ɗaukaka ƙarar da malam Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara ya yi a gabanta.

Hakan ya biyo bayan wata takarda da Abduljabbar ɗin ya aikewa kotun wadda ya sanarwa da kotun cewar ya janye lauyansa daga cikin shari’ar.

Kotun ta ɗage shari’ar har zuwa lokacin da malamin zai gabatar da wani lauyan a gaban ta.

Malam Abduljabbra dai ya ɗaukaka karar ne akan hukuncin kisan da kotun shari’ar muslunci ta kofar kudu ta yanke masa a baya bisa samun sa da laifi.

Babbar kotun shari’ar Muslunci ta kofar kudu ta yankewa Abduljabbar hukunci kisa ta hanyar rataya sakamakon kama shi da laifin batanci, sai dai kasancewar malamin bai yadda da hukuncin ba hakan yasa ya ɗaukaka ƙararar.

Yayin zaman Kotun na yau Laraba 15-05-2024 karkashin jagorancin Mai Shari’a Nasir Saminu, an gabatar da takardar dakatar da lauyan wadda Malamin ya sanya wa hannu a ranar 10-05-2024.

Sai dai lauyoyin Gwamnati sun nemi kotu ta kori neman, da bukatar gyara a kan bayanan da Kotun baya ta yi amfani da su wajen yanke masa hukuncin kisa.

Sai dai kuma kotun ba ta karbi rokon lauyoyin Gwamnatin ba, kamar yadda wakilinmu na Kotu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito.

Manta Sabo

Zaɓen ƙananan hukumomi: Kotu ta dakatar da hukumar Zaɓe ta Kano daga karɓar kuɗin Form ɗin da ta saka.

Published

on

Wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Abuja ta dakatar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano Kanseic, daga karɓar Naira milyan goma a matsayin kuɗin sayar da Form ɗin tsayawa takarar shugabancin ƙaramar hukuma, da kuma Naira miliyan biyar a matsayin na Kansiloli a jihar nan.

Wannan ya biyo bayan yadda jamiyyun APP da ADP, da kuma SDP na jihar Kano, suka shigar da hukumar kara a gaban babbar kotun tarayyar, suna kararta da ta dakatar da karɓar kudin har sai an kammala jin karar.

Da yake yiwa Dala FM Kano ƙarin bayani kan ƙarar, sakataren jam’iyyar ADP, mai kula da jamiyyar a arewacin kasar nan Tijjani Lawan Kofar Wambai, ya ce sun shigar da ƙarar ne bisa yadda kuɗaɗen da hukumar ta saka suka yi yawa, kasancewar karbar kudin ka iya bude hanyar cin hanci da rashawa.

A ranar 15 ga watan Agustan 2024, ne dai hukumar zaɓen ta jihar Kano, ta sanya Naira miliyan goma a matsayin kuɗin sayan Form na tsayawa takarar shugabancin ƙaramar hukuma, yayin da ta ce za’a biya Naira miliyan biyar a matsayin na Kansiloli, inda za’a gudanar da zaɓen a ranar 26 ga watan Oktoban 2024.

Continue Reading

Manta Sabo

Wasu ƴan mata sun tayar da bori a kotu bayan an tsalala musu Bulala

Published

on

Kotun majistret mai lamba 51 ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Hajara Safiyo Hamza, ta hori wasu ƴan mata da ɗaurin watanni 6, ko kuma zabin tarar dubu tamanin-tamanin kowanne su, da kuma karin bulala shida-shida haɗi da sharar banɗaki ta sati uku.

Tunda fari Ƴan Sanda ne suka gurfanar da ƴan matan bisa zargin su da yawan banza, da tayar da hankalin al’umma, da kuma laifin Shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.

Yayin da aka karantawa ƴan matan ƙunshin tuhumar da ake yi musu sun amsa laifin nasu har guda goma sha Shida.

A yayin zaman kotun ta tambaye su dalilin da ya sanya suke yawon banza, inda suka bayyana mata cewar suna fitowa ne daga gaban iyayensu idan sun kammala yawace-yawacen sai su koma gida.

Mai Shari’a Hajara Safiyo ta kuma umarci ƴan matan da su zama mutanen kirki idan sun gama zaman gidan gyaran halin.

Wakilin Dala FM Kano Yusuf Nadabo ya ruwaito cewar, jim kaɗan bayan kammala hukuncin sai ƴan matan suka fara koke-koke hadda hawa bori a kotun, bisa shiga furgicin da suka yi kan hukuncin.

Continue Reading

Manta Sabo

Zargin Karuwanci: Kotu ta aike da wasu ƴan Mata su 17 gidan gyaran hali

Published

on

Kotun Majistret mai lamba 51 ƙarƙashin mai Shari’a Hajara Safiyo Hamza, da ke jihar Kano, ta aike da wasu ƴan mata gidan ajiya da gyaran hali.

Tunda fari ƴan matan aƙalla su kimanin 17 an kama su ne a unguwar Sabon gari da ke jihar Kano, suna yawon ta zubar da kuma karuwanci.

Ƴan matan waɗanda aka gabatar da su a gaban kotun a wani yanayi na rashin kyan gani, sun bayyanawa kotun shekarunsu waɗanda suka kama daga shekara 18, zuwa 19, an kuma karanta musu zarge zargen da ake yi musu na yawan banza da karuwanci da kuma tayar da hankalin al’umma da shaye-shaye, inda suka amsa nan take.

Mai gabatar da ƙara Haziel, ya roƙi kotun da ta sanya wata rana dan a yi musu hukunci, domin iyayensu su bayyana a gaban kotun.

Kotun ta aike dasu gidan gyaran hali zuwa ranar 16 ga watan nan dan iyayensu su bayyana a gaban kotu, inda nan da nan suka ruɗe da Kuka

Wakilin Dala FM Kano, Yusuf Nadabo ya ruwaito cewar, yayin zaman wasu samari sun cika kotun da zummar su biya musu tara, sai dai kasancewar ba’a sanya su a hannun belin ba, a nan ne jami’in gidan gyaran hali Nasiru Dogarai ya tisa ƙeyarsu zuwa gidan gyaran hali.

Continue Reading

Trending