Manta Sabo
Na amince zan bai wa Sanata Hanga haƙuri – Ɗahiru Mai Huddadu
Kotun majistret mai lamba 19 mai zaman ta a Nomansland a Kano, ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Binta Galadanci, ta sanya ranar 10 ga watan gobe dan ci gaba da sauraron ƙarar da ƴan sanda suka shigar suna ƙarar Ɗahiru Ahmad mai Huddadu bisa tuhumar ɓata suna.
Tun da fari ƴan sanda ne suka gurfanar da Mai Huddadu a gaban kotun bisa zargin bata suna.
Ƙunshin zargin ya bayyana cewar Mai Huddadun ya bata sunan sanatan Kano ta tsakiya wato Sanata Rufa’i Sani Hanga, inda ya bayyana sanatan a matsayin Ɗan sharholiya, koda yake ya musanta zargin da ake masa.
A zaman kotun na yau an zauna dan a fara sauraron shaidu, sai dai mai Huddadun ya bai wa sanatan hakuri inda shi kuma ya bayyana cewar zai haƙura amma sai mai Huddadun ya shiga kafar yaɗa labarai ya janye wancan kalaman da ya yi.
Wakilinmu na Kotu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa, Mai Huddadun ya bayyana cewar zai janye kalaman nasa kamar yadda sanatan ya bukata ta kafar yaɗa labarai.
Manta Sabo
Kotun ta umarci jami’an tsaro da su ƙauracewa zaben ƙananan hukumomin da za’a gudanar a Kano
Babbar kotun tarayya mai zamanta a Kano karkashin jagorancin mai Shari’a Simon Amobeda, ta rushe shugabancin hukumar zabe ta jahar Kano Kanseic.
Kotun dai ta ɗauki wannan mataki ne bisa dogaro da hujjojin da áká gabatar mata na rashin cancantarsu, kasancewarsu ƴan Siyasa kuma suna ɗauke da katin Jam’iyyar NNPP.
Cikin wata kara wadda Aminu Aliyu Tiga da Jam’iyyar APC suka shigar suna rokon kotun da ta rushe su.
Kotun ta kuma umarci jami’án tsaro da su ƙauracewa zaben ƙananan hukumomin da za’a gudanar tare da umartar hukumar zabe ta kasa INEC, da kada ta bayar da kayan zaben.
A ranar Asabar ne dai 26 ga watan Oktoban 2024, za’a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar Kano.
Manta Sabo
Iyalan Marigayi Sharu Ilu sun sake samun nasara akan Aminu Ɗantata a Kotu
Kotun ɗaukaka kara da ke zamanta a sakatariyar Audu Bako, ta sake tabbatar da hukuncin kotun kasa na mallakawa iyalan marigayi Sharu Ilu wani rami da ke unguwar Gwammaja, da suke shari’a da Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata sama da shekaru huɗu.
Kotun ɗaukaka ƙarar da ke nan Kano mai alƙalai uku, wanda mai shari’a, Justice Ugo ya jagoranci zaman, ta sake tabbatar da hukuncin kotun kasa bayan da ɓangaren Alhaji Aminu Ɗantata suka nemi kotun ta basu izinin tafiya kotun koli domin sake ɗaukaka ƙara.
Akan roƙon da suka ɗin dai kotun ta ce sun makara bisa yadda tuni wa’adin ɗaukaka ƙarar ya ƙare, kamar yadda tashar Dala FM Kano, ta rawaito.
Manta Sabo
Zaɓen ƙananan hukumomi: Kotu ta dakatar da hukumar Zaɓe ta Kano daga karɓar kuɗin Form ɗin da ta saka.
Wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Abuja ta dakatar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano Kanseic, daga karɓar Naira milyan goma a matsayin kuɗin sayar da Form ɗin tsayawa takarar shugabancin ƙaramar hukuma, da kuma Naira miliyan biyar a matsayin na Kansiloli a jihar nan.
Wannan ya biyo bayan yadda jamiyyun APP da ADP, da kuma SDP na jihar Kano, suka shigar da hukumar kara a gaban babbar kotun tarayyar, suna kararta da ta dakatar da karɓar kudin har sai an kammala jin karar.
Da yake yiwa Dala FM Kano ƙarin bayani kan ƙarar, sakataren jam’iyyar ADP, mai kula da jamiyyar a arewacin kasar nan Tijjani Lawan Kofar Wambai, ya ce sun shigar da ƙarar ne bisa yadda kuɗaɗen da hukumar ta saka suka yi yawa, kasancewar karbar kudin ka iya bude hanyar cin hanci da rashawa.
A ranar 15 ga watan Agustan 2024, ne dai hukumar zaɓen ta jihar Kano, ta sanya Naira miliyan goma a matsayin kuɗin sayan Form na tsayawa takarar shugabancin ƙaramar hukuma, yayin da ta ce za’a biya Naira miliyan biyar a matsayin na Kansiloli, inda za’a gudanar da zaɓen a ranar 26 ga watan Oktoban 2024.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su