Connect with us

Manyan Labarai

An zargi Jami’in Soja da barazanar harbe wasu jami’an gidan gyaran hali a Kano

Published

on

Rahotanni daga jihar Kano sun bayyana yadda aka zargi wani Soja, da ya yi barazanar harbe wasu jamipan gidan ajiya da gyaran hali a jihar.

Al’amarin ya faru ne a harabar kotunan majistret da ke unguwar Nomansland a Kano, inda sojan ya je bakin ƙofar ɗakin da ake ajiye waɗanda ake tuhuma ya bai wa wani wanda ake tuhuma kudi, ba tare da sanin jami’an gidan gyaran halin ba.

Yayin da jami’an gidan gyaran halin suka yi masa magana sai ya bayyana musu cewar shi fa Soja ne, kuma idan ba su bishi a hankali ba zai fisge bindigar su ya harbe su a wajen.

Sai dai a lokacin da jami’an gidan gyaran halin suka fuskanci barazanar sai suka damƙe sojan inda suka miƙa shi caji ofishin ƴan sanda na Nomansland, kamar yadda shaidar gani da ido Barista Lawan Lawan Usman ya shaidawa Dala FM Kano.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya tunduɓi mai magana da yawun hukumar gidajen ajiya da gyaran hali ta jihar Kano SC Musbahu Lawan Ƙofar Nassarawa, sai dai ya ce za su binciki yadda batun ya ke.

Manyan Labarai

An samu ƙaruwar cin zarafin mata da ƙananan yara a shekarar 2024 fiye da kowace shekara a Kano – Human Right.

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network, ta ce akwai takaici kan yadda ake ƙara samun cin zarafin mata a mazantakewar aure, da kuma cin zarafin ƙanana yara wajen yi musu Fyaɗe, a Kano, a wannan shekara ta 2024.

Daraktan ƙungiyar na ƙasa Kwamared Gambo Madaki, shi ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da manema labarai yau a Kano, a wani ɓangare na bikin ranar yaƙi da cin zarafin ɗan Adam, da ake gudanarwa a ranar Talata.

Majalisar ɗinkin Duniya ce dai ta ware 10 ga watan Disamban kowacce shekara, domin gudanar da bikin ranar yaƙi da cin zarafin ɗan Adam ta Duniya.

Gambo Madaki, ya shaidawa Dala FM cewar, daga watan Janairun 2024, zuwa yanzu, sun karɓi ƙorafe-ƙorafe na cin zarafi aƙalla sama da 400, kuma mafi yawansu na cin zarafin Mata ne a zamantakewar aure, da kuma cin zarafin ƙananan yara, lamarin da ke ƙara ta’azzara.

“Ya kamata iyaye, da sauran al’umma, da hukumomi su bayar da gudunmawar su wajen ganin an ɗakile cin zarafin Mata da ƙananan yara, musamman ma da ake yi musu Fyaɗe, domin magance matsalolin, “in ji Gambo”.

A faɗin Duniya ne dai ake gudanar da bikin wannan rana ta yaƙi da cin zarafin ɗan adam, domin kiraye-kiraye da ma faɗar da al’umma ta yadda za su san haƙƙoƙin su.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mun shiga damuwa kan jibge jami’an tsaron da aka yi a ƙofar shiga fadar Sarkin Kano – Mazauna yankin

Published

on

Rahotanni na nuni da cewar an jibge jami’an tsaro ciki har da na Ƴan Sanda, a kofar fita daga masarautar Kano da ke Kofar Kudu, a dai-dai lokacin da mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu, ke shirin tafiya garin Bichi don raka sabon hakimin yankin.

Wakilinmu ya ruwaito cewar jami’an tsaron ciki har da na Ƴan Sanda ɗauke da jerin motoci ciki har da tankar ruwan Zafi, sun hana motoci fita sai dai mutum ya fito daga gidan Sarkin a Ƙafa tun safiyar wannan rana.

Sai dai wata majiya ta bayyana cewar daga garin Bichin ma jami’an tsaro sun hana shige da fice a gidan sarautar ƙaramar hukumar ta Bichi da ke jihar Kano.

Wasu mazauna yankin gidan Sarkin Kano, sun shaidawa Dala FM cewar, sun matuƙar shiga damuwa kan yadda suka ci karo da jibge jami’an tsaron na Ƴan Sanda da kuma na DSS, tun a safiyar yau Juma’a.

“Jami’an tsaron da muka gani an jibge mana tamkar wani yaƙi za ayi, duk da bamu san mai yake faruwa ba, kuma al’amarin ya sanya mu a cikin damuwa sosai, “in ji wani Matashi”.

Akan hakan ne wakilinmu Abubakar Sabo ya tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta wayar salula, domin jin ba’asi, sai dai ya ce ya bashi lokaci zai kira daga baya kasancewar a lokacin da ya kira shi yana cikin wani uzuri.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gyaran Hanya: Harkokin Sufuri sun tsaya a sabon titin Fanshekara da ke Kano.

Published

on

Rahotanni na nuni da cewar harkokin sufuri sun tsaya a sabon titin Fanshekara da ke jihar Kano, al’amarin da ya janyo cunkoson ababen hawa tun daga yamma zuwa cikin daren Alhamis ɗin nan.

Wasu shaidun gani da ido sun shaidawa Dala FM Kano, cewar, cunkoson ya haɗu ne sakamakon yadda ma’aikatan hukumar da ke gyaran tituna ta jihar Kano KARMA, suke gyaran wurin da ya lalace a kan titin da ke zuwa Ɗorayi har zuwa ƙofar Famfo.

Sabon titin Fanshekara dai ya yi mahaɗa da yankunan titin Sharaɗa Ja’en, da Fanshekara, da kuma titin Madobi da na Ɗorayi, da suke tsakanin ƙananan hukumomin Kumbotso da Gwale.

A cewar wani Ɗan kasuwa a sabon titin ya ce, kulle titin na Ɗorayi da hukumar ta KARMA, ta yi ya sa mafi yawan masu ababen hawa musamman ma manyan motoci sai kashe su suka yi, biyo bayan yadda suka rasa hanyar wucewa lamarin da ya ci musu tuwo a ƙwarya.

“Masu ƙananan ababen hawa irin su Baburan Adai-dai ta sahu, da Babura masu ƙafa biyu ne kawai ke iya samun damar wucewa suma idan suka yi ratse ta wata hanya da ta shiga yankin Chiranchi inda ake ɓullewa domin samun hanya ko kuma masu tafiya a Ƙafa, “in ji Ɗan kasuwar”.

Masu ababen hawan dai sun kuma yi kira ga hukumar da ke aikin da ta kammala aikin cikin gaggawa kasancewar hanyar babba ce da ababen hawa ke yawan zirga-zirga.

Continue Reading

Trending