Connect with us

Manyan Labarai

An yi jana’izar 9 daga cikin mutane 15 da wata babbar mota ta ture a Kano

Published

on

Yanzu haka an yi jana’izar mutane 9 daga cikin kusan 15 da wata babbar mota ta hallaka yayin da Direban motar yake gudun wuce kima, jim kadan da idar da sallar jumu’ar yau, a garin Imawa da ke ƙaramar hukumar Kura a jihar Kano.

A zantawar wakilinmu Mu’azu Musa Ibrahim, da wani daga cikin mazauna yankin, ya ce, Direban babbar motar ya ture mutanen ne bayan da aka idar da sallar juma’a, al’amarin da al’ummar yankin da abin ya shafa suka rufe babbar hanyar ta Kano zuwa Zaria ba shiga babu fita.

Bayan kulle hanyar mutanen sun kafa sharaɗin cewar ba za su buɗe hanyar ba har sai an kammala yin jana’izar dukkanin waɗanda suka rasu.

Mutumin ya kuma ƙara da cewa daga bisani motar ta faɗa cikin wani rami, inda aka nemi direba da yaron motar aka rasa sun gudu.

A cewar sa, “an tabbatar da mutuwar mutane 9, yayin da ya kasance ƴan cikin garin tara baki kuma su huɗu, inda sauran mutanen suka samu raunuka, “in ji shi”

Shima wani shaidar gani da ido ya ce, lokacin da babbar motar tazo wucewa ta wajen ana tsaka da bayar da hannu ne, lamarin da motar ta ture aƙalla mutane 15 da misalin ƙarfe 02:15 na yau Juma’a.

Manyan Labarai

Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu ya naɗa Hakimai Shida

Published

on

Mai martaba sarkin Kano Dakta Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya naɗa hakimai shida da safiyar Juma’ar nan tun bayan dawo da shi a matsayin Sarki.

Sarkin ya naɗa Alhaji Abba Yusuf baffan gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a matsayin Ɗan Makwayon Kano, da Alhaji Auwalu Mudi Yakasai, shi kuma Ɗan Malikin Kano, da Abdulƙadir Muhammad Balarabe a matsayin Zannan Kano.

Sauran sune Alhaji Muhktar Ibrahim Bello da Sarkin ya naɗa shi a matsayin Falakin Kano, sai kuma Alhaji Aminu Abdullahi Nasidi a matsayin Galadiman Kano.

Wakilin Dala FM Kano Yakubu Ibrahim Doragarai ya ruwaito ya ruwaito cewa, tuni hakiman da aka naɗa suka yi gaisuwa ga Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu.

Continue Reading

Manyan Labarai

Jam’iyyar NNPP ta dakatar da sakataren gwamnatin Kano da wani Kwamishina

Published

on

Jam’iyyar NNPP ta jihar Kano ta bayyana dakatar da sakataren gwamnatin jihar Dakta Abdullahi Baffa Bichi, da Kwamishinan Sufuri na jihar Kano Muhammad Diggwal, daga cikin jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar NNPP a Kano Dakta Hashim Sulaiman Dungurawa ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da aka aikowa Dala FM Kano, a cikin daren yau Litinin.

Hashim Dungurawa, ya ce dakatar da ƙusoshin gwamnatin jihar Kano su biyu ya biyo bayan zargin keta alfarmar jagoranci, da ta Jam’iyya, da kuma keta alfarmar gwamnati, a don haka ne suka ɗauki matakin ba tare da yin wasa ba akai.

“Jagorancin shugabancin jam’iyyar mu na ƙananan hukumomin da mutane biyun suka fito sun gabatar mana da ƙorafe-ƙorafe kan ƙusoshin gwamnatin biyu, akan zarge-zarge da ake musu ya sa muka ɗauki matakin dakatar da su, har sai mun gama bincike, “in ji Dungurawa”.

Sulaiman ya ƙara da cewar dakatar da Abdullahi Baffa Bichi da Muhammad Diggwal ta fara aiki ne daga ranar Litinin 14 ga watan Oktoban 2024, kamar yadda jam’iyyar ta samu ingantattun shawarwari akan zargin da ake musu.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ku tallafawa mazauna Asibitin masu lalurar Ƙwaƙwalwa na Ɗorayi bisa halin da suke ciki – Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam 

Published

on

Ƙungiyar wayar da kan jama’a da kare haƙƙin ɗan adam da tallafawa mabuƙata, ta Awareness for Human Right and Charity Foundation, ta tallafawa mazauna Asibitin masu lalurar Ƙwaƙwalwa da ke unguwar Ɗorayi, da dafaffen abinci, domin rage musu wata damuwa.

Ƙungiyar dai ta rabawa masu lalurar Ƙwaƙwalwar abincin ne da yammacin Asabar 12 ga watan Oktoban 2024, tare da ziyartar wata makarantar tsangaya da ke unguwar Ɗorayi, inda ɗalibai 1,000 suka rabauta da tallafin dafaffen abincin.

Da yake yiwa Dala FM Kano, ƙarin bayani daraktan ƙungiyar ta Awareness for Human Right and Charity Foundation, Kwamared Auwal Usman, ya ce rahotannin da suka samu kan yadda mazauna Asibitin da kuma makarantun tsangayar ke fuskantar ƙalubalen abinci ya sa suka kai musu tallafin domin rage musu wani raɗaɗi.

 

Wasu daga cikin masu lalurar Ƙwaƙwalwar da suka fara samun sauƙi, sun nemi ɗaukin gwamnatin jihar Kano wajen magance ƙalubalen da suke fuskanta na rashin kyawun wuraren da suke kwana da sauran matsaloli, ko sa samu wani sauƙi.

Da yake nasa jawabin mai kula da Asibitin da ake kula da masu lalurar Ƙwaƙwalwar na Ɗorayi a Kano, Munnir Ɗahiru Kurawa, ya miƙa godiyar sa ga tawagar ƙungiyar bisa kaɓakin alkhairin da ta saukewa masu taɓin hankalin.

Wannan dai na zuwa ne makwanni kaɗan da gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ziyarci Asibitin masu lalurar Ƙwaƙwalwar na Ɗorayi, har ma ya bada umarnin aje a gyara shi, sai dai kawo yanzu hakan bata samu ba kamar yadda wata majiya ta bayyana.

Continue Reading

Trending