Manyan Labarai
Dubun mai sayar da kayan Miya ta cika bayan da aka tsinci ramin gawarwakin mutanen da suka ɓata a gidansa

Al’ummar garin Dawakin Kudu tare da jami’an tsaro, sun taru a gidan wani mai sayar da kayan miya ana zakulo gawarwakin ƴan garin da akai zargin ya jima yana kashewa, idan ya yi garkuwa dasu ya nemi kudin fansa ba’a bashi ba ya kashe su.
A zantawar wakilinmu Tijjani Adamu da wani daga cikin mazauna garin mai suna Umar Tukur, ya shaida cewa, an daɗe ana sace mutane a yankin wanda yanzu haka akayi lissafin an ɗebe mutane kusan guda biyar.
Ya ci gaba cewa, A daren jiya Lahadi ne ballin mutumin ta tashi abinda jami’an tsaron Ƴan Sanda suka cafke shi, al’amarin da zuwa yau aka samu kusan gawar-wakin sama da mutane shida a cikin gidan mutumin da ake zargin ya kashe.
Shima da yake yiwa gidan rediyon Dala FM, ƙarin bayani, wani matashi da ya ganewa idanun sa al’amarin, ya ce da suka shiga cikin gidan sun ga yadda aka ɗaukko gawar wani mutu a cikin Masai, da ta wasu matattu, tare da wasu sassan jikin ɗan adam, a cikin gidan.
Ya kuma ce wasu sassan gawar-wakin sai zuba su aka rinƙa yi a cikin Leda, kasancewar sassan jikinsu sun ruɓe, al’amarin da ya tayar da hankalin al’ummar garin na Dawakan Kudu, da ke jihar Kano.
“An rinƙa jiyo wari a yankin da gidan mutumin yake al’amarin da yasa aka buge kwaɗon gidan inda aka rinƙa ganin gawarwaki a guraren daban-daban a cikin gidan, “in ji wani mazaunin garin”.
Wani mazaunin yankin ya shaidawa wakilinmu Mu’azu Musa Ibrahim cewa, mutumin da ake zargin mai suna Abdul-azi, ya tare a unguwar ne bayan da yaje almajirci, inda yake sana’ar sayar da kayan Miya a garin na Dawakin Kudu, kuma an zargi daga cikin gawarwakin akwai wani abokin sa da akayi garkuwa dashi kusan shekaru huɗu da suka gabata.
Akan al’amarin ne wakilin mu ya yi duk mai yiyuwa domin ji daga ɓangaren rundunar ƴan sandan jihar Kano, sai dai Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai samu damar ɗaga wayar sa ba.

Manyan Labarai
Ɗan Bijilante ya rasa ransa bisa arangamar su da wasu ƴan Daba a Kano

Ƙungiyar sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamandan ta Ubale Barau Muhammad Badawa, ta tabbatar da rasuwar guda daga cikin jami’in ta mai suna Suraj Rabi’u mazaunin Jaba da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar, sakamakon arangama da ƴan Daba.
Mai magana da yawun ƙungiyar Bijilante na jihar Kano, kuma Kwamandan ta na ƙaramar hukumar Fagge, Usman Muhammad Ɗan Daji, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM Kano a ranar Lahadi.a
“Jami’in Bijilanten namu ya rasa ran nasa ne sakamakon arangama da suka yi da wasu Ƴan Daba yayin gudanar aikinsu a ranar Idin ƙaramar Sallah, inda ƴan dabar suka soke shi da Ɗanbida a Ƙirji da bayansa, wanda ya yi sanadiyar rasuwarsa, “in ji Usman”.
Ya kuma ce, an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi mai suna Usman Sharif mazaunin ƙaramar hukumar Dala, kuma tuni aka miƙa shi hannun jami’an tsaro.
Usman Ɗan daji, ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan jami’in nasu ya gafarta masa.

Manyan Labarai
An ga watan ƙaramar Sallah a Najeriya – Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya, inda za a yi karamar Sallah gobe Lahadi.
Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a yayin jawabin da ya gabatar a cikin daren Asabar ɗin nan, ya ce sun samu rahotannin ganin watan ne daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce daga cikin guraren da aiko musu da ganin jinjirin watan na Shawwal akwai Zazzau, da kuma daga Sarkin Dutse, da Arugungu, da kuma Shehun Borno, da dai sauran gurare daban-daban na Najeriya.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su gabatar da bikin sallar cikin kwanciyar hankali, tare da taimaka wa mabuƙata.
Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, biyo bayan sanarwar fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, ya kasance ranar Lahadi take 1 ga watan Shawwal na shekarar 1446, wato ranar ƙaramar Sallah.

Manyan Labarai
Shugaba Tinubu da Sifeton Ƴan Sanda ku bi wa mutanen mu da aka yi wa kisan gilla hakƙin su – Rt. Hon. Rurum

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Rabo, Kibiya da Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum, ya bayyana kaɗuwar sa bisa kisan gillan da aka yi wa wasu Mafarauta su kusan 16, a garin Uromi da ke jihar Edo, a lokacin da suke hanyar su ta komawa Kano daga jihar Rivers.
Honarable Kabiru Rurum, ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da aka aikowa Dala FM Kano a ranar Asabar, ya ce daga cikin mutanen da aka ƙona akwai mutum 11 da suka fito daga mazaɓun yankin sa na Kibiya da Bunkure, inda wasu 6 suka samu muggan raunuka suna karɓar Magani yanzu haka a jihar Edo.
A cewar Ɗan Majalisar, “Wannan abu da matasan garin Uromi a jihar Edo, suka yi ya saɓa da dokar kasa, kuma mummunan laifi ne, a don haka za mu bi kadin hakƙin mutanen mu da aka kashe a kuma waɗanda aka jikkata, “in ji shi“.
Kabiru Rurum, ya ce a matsayinsa na wakilin mutanen da aka kashe a majalisar Wakilai ta ƙasa, yana kira ga shugaban Najeriya Bola Tinubu, da babban Sifeton ƴan sanda, da su yi duk mai yiyuwa wajen ganin an kamo waɗanda suka yi wannan aika-aikar tare da hukunta su, da kuma biyan diyya ga iyalan waɗanda suka rasu da kula da waɗanda suka jikkata.
“Kasancewar wannan bashi ne na farko da ake samun wasu ɓata gari na tare matafiya akan hanya da basu ji ba basu gani ba su kashe su, a don haka muna fatan wannan karon gwamnati da sauran hukumomin tsaro za su ƙaddamar da ƙwaƙƙwaran bincike don ɗaukae mataki kamar yadda dokar kasa ta tanada, “in ji Rurum”.
Ɗan majalisar ya kuma jajantawa dukkanin al’ummar jihar Kano musamman Iyalan waɗanda suka rasu, tare da addu’ar Allah ya gafarta musu yasa Jannatul Firdausi makomar su, su kuma waɗanda suka jikkata Allah ya basu lafiya.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su