Manta Sabo
Wasu ƴan mata sun tayar da bori a kotu bayan an tsalala musu Bulala

Kotun majistret mai lamba 51 ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Hajara Safiyo Hamza, ta hori wasu ƴan mata da ɗaurin watanni 6, ko kuma zabin tarar dubu tamanin-tamanin kowanne su, da kuma karin bulala shida-shida haɗi da sharar banɗaki ta sati uku.
Tunda fari Ƴan Sanda ne suka gurfanar da ƴan matan bisa zargin su da yawan banza, da tayar da hankalin al’umma, da kuma laifin Shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.
Yayin da aka karantawa ƴan matan ƙunshin tuhumar da ake yi musu sun amsa laifin nasu har guda goma sha Shida.
A yayin zaman kotun ta tambaye su dalilin da ya sanya suke yawon banza, inda suka bayyana mata cewar suna fitowa ne daga gaban iyayensu idan sun kammala yawace-yawacen sai su koma gida.
Mai Shari’a Hajara Safiyo ta kuma umarci ƴan matan da su zama mutanen kirki idan sun gama zaman gidan gyaran halin.
Wakilin Dala FM Kano Yusuf Nadabo ya ruwaito cewar, jim kaɗan bayan kammala hukuncin sai ƴan matan suka fara koke-koke hadda hawa bori a kotun, bisa shiga furgicin da suka yi kan hukuncin.

Manta Sabo
Zargin Kisa: Kotu ta aike da Matashi gidan Yari a Kano

Kotun Majistret mai lamba 16 ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Alkasim Nasib Ɗan Fillo, ta aike da wani matashi gidan gyaran hali bisa zargin sa da laifin kisan kai.
Tunda fari, Ƴan Sanda ne suka gurfanar da matashin suna zargin sa da laifin haɗa baki da fashi da makami, da kuma laifin kisan kai.
Ƙunshin zargin ya bayyana cewar, a ranar 5 ga wannan watan na Mayun 2025, ne matashin mai suna Aliyu Umar, suka haɗa baki da wasu matasa waɗanda a yanzu sun tsere, inda suka shiga gidan wani mutum mai suna Muhammad Shehu.
An yi zargin cewa bayan sun shiga gidan mutumin sun yi amfani da muggan makamai suka yi masa fashin wayar Salula, daga ƙarshe an zargi cewa sun soka masa Wuƙa a Maƙogoro har rai ya yi halinsa.
Yayin da aka karanta wa matashin ƙunshin zargin ya bayyana cewar ya fahimta, daga nan ne kotun ta bayyana cewar bata da hurumin yin shari’ar kisan kai, a don haka za ta jira shawarar lauyoyin gwamnati.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewar, an sanya ranar 26 ga watan gobe don a kara gabatar da matashin a gaban kotu.

Manta Sabo
Kotu ta tura Amarya da Angon ta gidan Yari a Kano

Babbar kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Post Office, a Kano, ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Munzali Tanko Soron Ɗinki, ta aike wata mata da wani mutum gidan gyaran hali zuwa Mako ɗaya, bisa zargin su da Aure akan Aure.
Tunda fari wani magidanci ne ya maka matarsa da wani mutum da ya same shi a ɗakinsa a gaban kotu, ko da dai matar ta ce wai wanda mijin nata ya gani shima mijinta ne.
Lamarin dai ya faru ne a unguwar Tudun Murtala, inda mai ƙarar ya zo gidan matarsa kasancewar yanada wasu matan, sai ya sami wani mutum a kwance akan gadan matar, inda nan take ya tambaye shi waye shi? sai matar ta ce ɗan uwanta ne, hakan ya sa ya gayyato Maƙota su ka zo domin su shaida faruwar lamarin.
Daga bisani ne kuma ya garzaya babbar kotun shari’ar Musulunci da ke Post Office a jihar Kano, ƙarƙashin mai shari’a Munzali Tanko Soron Ɗinki, inda ya yi ƙarar sabon mijin da matar.
Mutumin ya faɗawa kotun cewar shekararsu shida ke nan da Aure a tsakanin su, amma kwatsam sai ya sami wani a ɗakinta, kuma ya ce kwana biyu tsakani ya yi mu’amular Aure da ita.
Sai dai sabon mijin ya ce matar ta faɗa masa bata da Aure, hakan ya sa ya tura wakilansa aka biya dubu ɗari a matsayin sadaki har aka ɗaura musu auren.
Ko da Kotu ta wai-wayi matar ta ce ai babu aurensa a kanta bayan samun magana mai karo da juna, a nan ne mai Shari’a ya tambayi asalin waliyinta, inda shi kuma ya ce bai san ta yi wani auren ba.
Hakan yasa kotu ta bukaci ta rantse akan ya saketa sai dai ta ce Eh, aka tambayeta ko za ta rantse ta ce A’a, akace shi tsohon mijin zai rantse ya ce zai rantse, nan take ta ce ba za ta bari ya rantse ba.
Daga bisani kotun ta buƙaci a turasu wajan yan sanda sannan matar ta ce za ta faɗi gaskiya.
Matar ta faɗawa kotun cewar tabbas ta yi aure akan Aure, a don haka take neman afuwa, a nan ne mai Shari’a ya aike da matar da sabon mijin gidan gyaran hali har zuwa sati daya domin yi mata hukunci, kamar yadda wakilinmu Aminu Abdu Baka Noma ya ruwaito.

Manta Sabo
Kotu ta yi umarnin a kamo wani Dagaci a Kano

Babbar kotun Shari’ar Muslunci da ke zaman ta a Rijiyar Lemo a nan Kano, ta yi umarnin yansanda su kamo mata dagacin garin Iya malam Lawan Ibrahim.
Tun da farko wani mutum ne mai suna Nura Musa Inuwa mazaunin Katsinawa, ya shigar da ƙara yana da’awar cewa ya sayi gona a hannun dagacin amma daga baya ya samu cewar dagacin ya sayar wa da wani mutum daban gonar.
A zaman dai, kotun ta yi umarnin a kamo mata dagacin a karkashin Shari’a mai lamba Cv/373/2024.
Wakilin Dala FM Kano, Yusuf Nadabo Ismail, ya tuntuɓi dagacin ta wayar Salula, amma bai samu damar ɗagawa ba, ya kuma aike masa gajeren saƙo amma har zuwa lọkacin hada wannan labarin ba mu ji daga gare shi ba.

-
Nishadi6 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su