Connect with us

Manyan Labarai

Mun shiga damuwa kan kwashe motocin da suke aikin hanyar mu – Mazauna garin Kara Gwarzo a Kano

Published

on

Al’ummar garin Kara da ke karamar hukumar Gwarzo a jihar Kano, sun jaddada rokon su kan magance musu matsalar rashin ruwan Sha da ta karancin Likitoci a asibitin yankin su, da ta lalacewar ajujuwa a makarantu, da kuma ta lalacewar hanyar su, al’amarin da ke damun su.

A zantawar wakilin Dala FM, Hassan Mamuda Ya’u da sakataren kungiyar Matasa ta samar da ci gaban garin na Kara da ke karamar hukumar Gwarzo, Khalid Sale, ya ce a baya-bayan nan gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ya ƙaddamar da gyaran hanyar tasu, amma yanzu haka sun ga an kwashe motocin da suke aikin ba tare da sun san dalilin hakan ba.

Ya ci gaba da cewa, a don haka ne suke kira ga gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da dukkanin shugabannin yankin su, da su kai musu ɗaukin da ya dace dan magance musu matsalolin da suke addabar su.

“Tsayawar aikin gyara hanyar tamu da ta tashi daga bakin titin Gwarzo ta wuce zuwa unguwannin Kara, da Sabon layin Kara, ta wuce Ɗalangashi, har zuwa jihar Katsina, yanzu haka tayi matuƙar lalacewar da idan akayi ruwan sama muna shiga cikin Damuwa, “in ji Khalid”.

Ya kuma ƙara da cewa suna fama da matsalar rashin ruwan Sha, da ta ƙarancin Likitocin a Asibitin yankin su, da kuma ta lalacewar ajujuwa a makarantun su, amma ta lalacewar hanyar tafi yankin nasu tafi damun su.

A cewar sa, “Mun yi farin ciki da miƙa godiyar mu ga gwamnan Kano, bisa yadda ya ƙaddamar da gyara hanyar garin mu na Kara da ke ƙaramar hukumar Gwarzo, amma dai bamu ji daɗin kwashe motocin da akayi ba, domin yanzu haka aikin ya tsaya cak, “in ji shi”.

Akan al’amarin ne wakilin namu ya tuntubi shugaban riko na ƙaramar hukumar ta Gwarzo Mani Tsoho Zango, ta wayar tarho, sai dai a lokacin ya ce ya bashi lokaci kasancewar a lokacin da aka kirashin yana tsaka da wani uziri.

Idan ba’a manta ba al’ummar yankin sun daɗe da shaidawa Dala FM Kano, halin damuwar da suke cikin kan rashin al’amuran more rayuwa a yankin nasu.

Manyan Labarai

Tirƙashi: Wasu Matasa sun bankawa Dai-dai ta Sahu wuta a Kano

Published

on

An yi zargin wasu fusatattun matasa sun bankawa wani baburin Adai-daita Sahu Wuta, tare da yunƙurin saɓawa masu baburin kamanni, domin huce haushin su akan su.

Tunda fari dai an zargi masu baburin ɗan sahun (keke Napep) da satar dabbobin mutane a Maƙabartar unguwar Maikalwa da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano, lamarin da fusattun matasan suka ɗauki mummunan matakin akan su.

Wasu shaidun gani da ido sun shaidawa wakilinmu Nasir Khalid Abubakar cewar, an ƙona baburin ne a yammacin Asabar, tare da yunƙurin far wa masu babur ɗin daga bisani jami’an tsaro suka kai ɗauki tare da tafiya da matasan da ake zargi da satar dabbobin.

Wakilin tashar Dala FM Kano, ya ruwaito cewa, bayan faruwar lamarin ne kuma wasu matasa a yankin suka yi ƙoƙarin kashe wutar da ke ci a baburin Adai-dai Sahun, da zummar idan ta mutu su ɗebi kayayyakin da basu ƙone ba a matsayin Ganima, sai dai jami’an ƴan sanda suka tarwatsa su.

Akan batun mu so jin ta ɓangaren rundunar ƴan sandan jihar Kano, sai dai haƙar mu bata cimma ruwa ba, amma za aji mu da ita da zarar ta magantu.

Continue Reading

Manyan Labarai

Kitumurmurar da gwamnatin Tinubu take shiryawa jihar mu ba za ta yi tasiri ba – Gwamantin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce babu wata matsalar tsaro a ko kuma shirin tayar da hargitsi a jihar, da aka rinƙa yadawa cewar za a iya samu a jihar.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar cikin daren juma’ar nan ta 24 ga watan Janairun 2025.

Ya ce rahotannin da ake yaɗawa cewar za a iya samun tayar da hargitsi daga wasu ƴan ta’adda a jihar, gwamnatin jihar Kano bata da masaniya akan batun, kuma lamarin bashi da tushe ballantana makama.

“An zo an jibge jami’an tsaron ƴan sandan gwamnatin tarayya a mashigar filin wasa na Sani Abacha Stadium, da sunan za a hana Maulidin da aka saba gabatarwa duk shekara, wanda aka shirya gudanarwar a gobe Asabar, inda jami’an tsaron ke neman hanawa, kuma ba zamu mu amince da hakan ba, “in ji Waiya”.

A cewar sa, Kitumurmurar da gwamnatin shugaba Bola Tinubu take shiryawa jihar Kano ba za ta yi tasiri ba.

Wanan dai na zuwa ne bayan da rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta bakin kakakin ta SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta sanar da cewar, ta samu bayanan sirri kan yadda wasu ɓata gari ke shirin tarayyar da tarzoma jihar Kano, al’amarin da gwamantin jihar ta musanta.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mun samu bayanan sirri kan ƴan ta’addan da ke shirin tayar da hankali jama’a a Kano – Jami’an Tsaro

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta ce ta shirya tsaf haɗin gwiwa da sauran jami’an tsaro domin daƙile ayyukan wasu ɓata gari da ta samu rahoton sirri akan su da suke shirin tayar da hankalin jama’a a jihar.

Kakakin rundunar ƴan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM a ranar Juma’a 24 ga watan Janairun 2025.

SP Kiyawa, ya ce akwai buƙatar al’umma su ƙara sanya idanu a unguwanni su da ma wuraren harkokin su na yau da kullum tare a sanin mutanen da ke shiga cikin su, don taimaka wa wajen magance matsalar tsaron.

“Ga dukkanin wanda ya ga faruwar wani baƙon al’amari zai iya sanar da ofishin ƴan sanda mafi kusa don ɗaukar matakin da ya dace cikin gaggawa, ko kuma ya kira waɗannan lambobin wayar 08032419754, ko 09029292926, ko kuma 08123821575, “in ji SP Kiyawa”.

Har ila yau, Kiyawa ya ce Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano CP Salman Dogo Garba, tuni ya bada umarni aka baza jami’an taron ƴan sanda domin samar da tsaro a faɗin jihar Kano, tare da daƙile ayyukan ɓata garin.

Continue Reading

Trending