Manyan Labarai
Na yi takaici kan rashin kulawa da makarantar Governors College – Gwamnan Kano
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya koka tare da nuna takaicinsa bisa yadda ya sami makarantar Governors College, cikin rashin kulawa, da yadda ɗaliban makarantar suke karatu babu abubuwan zama, da yadda wasu ajujuwan suke cike da ruwa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wannan jawabin da yammacin yau, yayin wata ziyarar bazata da ya kai makarantar, domin ganin yadda aikin ta yake gudana, da kuma tabbatar da anyi mata aiki yadda gwamnati ta tsara.
Gwamna Abba Kabir, ya kuma ƙara da cewa, ya yi tsammanin yadda makarantar take ta waje fesfes a waje, hakan ma zai ga cikin ta amma sai ya tarar da saɓanin hakan.
“Muna kira ga manyan ƴan kasuwa da suke faɗin jihar Kano da su shigo domin tallafa wa harkar ilimi musamman makarantun firamare da na sakandire, domin ciyar dasu gaba, “in ji Abba Kabir”.
Idan ba’a manta ba, Tun a baya Dala FM Kano, ta kawo muku labarin yadda gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya sanya dokar ta ɓaci akan Ilmi a jihar.
Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da magance duk wata matsala da ta shafi fannin ilimi a faɗin jihar Kano.
Manyan Labarai
Majalisar dokokin Kano ta yi karatu na biyu kan kafa rundunar tsaro mallakin jihar
Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da karatu na biyu kan kudurin dokar kafa Rundunar tsaro, da ta hukumar samar da wutar lantarki dukkanin su mallakin gwamnatin Kano.
Da yake karanto ƙudurin dokokin, shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Hussaini Dala, ya ce samar da dokokin domin kafa Ma’aikatun biyu zai inganta tattalin arzikin jihar Kano.
Lawan Hussaini, ya kuma ce idan akayi la’akari da yadda gwamnatocin kudancin Najeriya suka samar da Rundunonin tsaro mallakin su irin su Amotekum domin inganta tsaron cikin gida, ya zama wajibi gwamnatin jihar Kano ma ta samar da nata hanyoyin tsaron.
A cewar sa, “Amincewa da karatu na biyu a kudurin dokar kafa hukumar samar da wutar lantarki mallakin gwamnatin Kano ya biyo bayan sahalewar da gwamnatin tarayya ta yi wa jihohin Najeriya, na su samar da hasken wutar lantarki mallakin su domin haɓaka tattalin arziki, “in ji shi”.
Wakilin mu na majalisar dokokin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewar, majalisar ta ce jami’an rundunar tsaron da za’a samar suna da ikon ɗaukar makamai ƙirar gida domin su kare kansu, sannan suna da ikon kama mai laifi tare da mika shi ga jami’an ƴan sanda domin gurfanarwa a gaban kotu, ba tare da jira ba.
Manyan Labarai
Tirƙashi: Wasu Matasa sun bankawa Dai-dai ta Sahu wuta a Kano
An yi zargin wasu fusatattun matasa sun bankawa wani baburin Adai-daita Sahu Wuta, tare da yunƙurin saɓawa masu baburin kamanni, domin huce haushin su akan su.
Tunda fari dai an zargi masu baburin ɗan sahun (keke Napep) da satar dabbobin mutane a Maƙabartar unguwar Maikalwa da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano, lamarin da fusattun matasan suka ɗauki mummunan matakin akan su.
Wasu shaidun gani da ido sun shaidawa wakilinmu Nasir Khalid Abubakar cewar, an ƙona baburin ne a yammacin Asabar, tare da yunƙurin far wa masu babur ɗin daga bisani jami’an tsaro suka kai ɗauki tare da tafiya da matasan da ake zargi da satar dabbobin.
Wakilin tashar Dala FM Kano, ya ruwaito cewa, bayan faruwar lamarin ne kuma wasu matasa a yankin suka yi ƙoƙarin kashe wutar da ke ci a baburin Adai-dai Sahun, da zummar idan ta mutu su ɗebi kayayyakin da basu ƙone ba a matsayin Ganima, sai dai jami’an ƴan sanda suka tarwatsa su.
Akan batun mu so jin ta ɓangaren rundunar ƴan sandan jihar Kano, sai dai haƙar mu bata cimma ruwa ba, amma za aji mu da ita da zarar ta magantu.
Manyan Labarai
Kitumurmurar da gwamnatin Tinubu take shiryawa jihar mu ba za ta yi tasiri ba – Gwamantin Kano
Gwamnatin jihar Kano ta ce babu wata matsalar tsaro a ko kuma shirin tayar da hargitsi a jihar, da aka rinƙa yadawa cewar za a iya samu a jihar.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar cikin daren juma’ar nan ta 24 ga watan Janairun 2025.
Ya ce rahotannin da ake yaɗawa cewar za a iya samun tayar da hargitsi daga wasu ƴan ta’adda a jihar, gwamnatin jihar Kano bata da masaniya akan batun, kuma lamarin bashi da tushe ballantana makama.
“An zo an jibge jami’an tsaron ƴan sandan gwamnatin tarayya a mashigar filin wasa na Sani Abacha Stadium, da sunan za a hana Maulidin da aka saba gabatarwa duk shekara, wanda aka shirya gudanarwar a gobe Asabar, inda jami’an tsaron ke neman hanawa, kuma ba zamu mu amince da hakan ba, “in ji Waiya”.
A cewar sa, Kitumurmurar da gwamnatin shugaba Bola Tinubu take shiryawa jihar Kano ba za ta yi tasiri ba.
Wanan dai na zuwa ne bayan da rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta bakin kakakin ta SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta sanar da cewar, ta samu bayanan sirri kan yadda wasu ɓata gari ke shirin tarayyar da tarzoma jihar Kano, al’amarin da gwamantin jihar ta musanta.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su