Manyan Labarai
Mun sauya salon Zanga-zangar tsadar rayuwar da muka shirya gudanar wa a Kano – War Against Injustice
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam da yaƙi da rashin adalci da kuma bibiyar al’amuran da suka shafi shugabanci na gari, ta War Against Injustices, ta ce yanzu haka ta sauya salon gudanar da zanga-zangar lumanar tsadar rayuwa, daga fita kan titi zuwa shirya taron manema labarai da masu ruwa da tsakin ƙungiyar.
Daraktan ƙungiyar a nan Kano Kwamared Umar Ibrahim Umar, ne ya bayyana hakan a zantwarsa da gidan rediyon Dala FM, a ranar Litinin 29 ga watan Yulin 2024.
Ya ce, sun yanke shawarar shirya taron manema labarai ne su sanar da gwamnati, da sauran shugabanni halin matsin rayuwar da al’umma suka samu kan su a ciki, bisa yadda suka samu bayanan sirri kan yadda wasu ke yunƙurin amfani da zanga-zangar wajen tada hankalin al’umma, da kuma rufar wa kadarorin gwamnati.
“Abinda ya sa muka ce ba zamu yi zanga-zangar tsadar rayuwar a kan tituna ba saboda mu banbanta kan mu daga ɓata garin da suke yunƙurin tayar da hankalin al’umma wajen ƙone-ƙone da farwa kayayyakin gwamnati da na al’umma, “in ji shi”.
Kwamared Umar Ibrahim, ya ƙara da cewa burin su shine gwamnatin tarayya ta dawo da tallafin man Fetur, da cire ƙarin kuɗin wutar lantarkin da aka yiwa ƴan Najeriya, da kuma rage kuɗin karatun Ɗaliban jami’o’i, da matsalar tsaro, tare da sauƙaƙa wa al’ummar ƙasa.
“Dokar ƙasa sashi na 39, da na 40, ya bai wa kowanne ɗan ƙasa damar gudanar da zanga-zangar lumana, domin sanar da gwamnati damuwar su, a don haka ne ma muka ƙudirin aniyar gudanar da zanga-zangar a baya, amma saboda gujewa kai din ɓata gari, ya sa muka sauya salon ta zuwa taron manema labarai, “in ji kwamared Umar”.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya ruwaito cewa, kwamared Umar Ibrahim ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da tsaro ga al’umma, da dai-dai al’amura domin ganin al’ummar Najeriya sun samu sauƙi.
Idan za’a iya tunawa wasu dandazon matsa sun ƙudiri gudanar da zanga-zangar lumana ne daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Yulin 2024, domin nusartar da gwamnatin tarayya halin matsin rayuwar da aka samu kai yanzu a ciki, dan ganin an magance matsalolin al’umma su samu sauƙi.
Manyan Labarai
Wata Sabuwa: Lauya ya nemi kotu ta kama kwamishinan Shari’a na jihar Kano
Wani lauya mai zaman kan sa a jihar Kano Barista Haruna Musa Muhammad, ya yi ƙorafi a gaban babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar, akan ta kama kwamishinan Shari’a na jihar Kano Barista Haruna Isah Dederi, da wasu manyan mukarraban gwamnatin jihar.
Lauyan wanda yake wakiltar mai kara Nura Bashir Ahmad, ya bayyana cewar gwamnatin jihar Kano ta rushe wa Nura gida duk da cewar ya samu hukunci a babbar kotun tarayya akan kada a rushe masa gidan.
Cikin wata ƙunshin Shari’a mai lamba FHC/KN/CS/240/2023, mai Shari’a Simon Amobida, ya ayyana cewar kotun tarayya ta gamsu da takardun mallaka da mai ƙara Bashir Ahmad ya gabatar mata, don haka ne ma ta ayyana cewar gidan mallakinsa ne.
Kotun dai tun a ranar 13 ga watan biyu na shekarar da ta gabata ta 2024, ta zartas da hukuncin akan batun.
Mai karar Bashir ta bakin lauyansa Barista Haruna Musa, sun bayyana cewar sun rubuta koke zuwa gaban kotun da ta yi hukuncin tun da dai suna zargin waɗanda ake ƙarar sun raina wannan hukunci kamar yadda ya bayyana a zantawar sa da wakilin Dala FM Kano.
Akan wannan batu ne wakilin namu ya tuntuɓi kwamishinan Shari’a na jihar Kano Barista Haruna Isah Dederi, ta wayar salula, sai dai bai samu damar ɗaa wayar ba, ya kuma aike masa da gajeren saƙon kar ta kwana nan ma bai bada amsa ba, amma yana dakon sa.
Manyan Labarai
Budurwa ta mutu yayin wata Gobara da ta kama cikin gidan su a Kano
Wata Gobara da ta tashi a wani gida ta yi sanadiyyar rasuwar wata budurwa a unguwar Ja’en Sabere da ke ƙaramar hukumar Gwale a Kano da ke arewacin Najeriya, tare da ƙonewar wasu sassan gidan.
Mamallakin gidan da lamarin ya faru mai suna Saminu Abba ne ya tabbatar wa tashar Dala FM faruwar lamarin a ranar Alhamis, 16 ga watan Janairun 2025.
Ya ce gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe ɗaya na daren jiya Laraba, lamarin da jami’an hukumar kashe Gobara ta jihar Kano da ma ƴan Bijilanten yankin da sauran al’umma suka kai ɗauki.
“Muna cikin Bacci muka ji wata ƙara da ihun mutanen unguwa, da muka tashi muka ga Gobara ce ta tashi a wasu sassan gidan mu kuma wutar ta tare hanyar da za mu fita gashi tana ci ba ƙaƙƙautawa, “in ji Saminu”.
Ya ci gaba da cewa, “Bayan jami’an hukumar kashe Gobara da ƴan Bijilanten yankin, da sauran al’umma sun kawo musu ɗauki, ne aka fasa Gini ta gidan maƙotan su inda su shida suka fita daga gidan sai dai ƴar su budurwa mai shekaru 18 mai lalurar Sikila ta rasu”.
Mallam Saminu Abba ya ƙara da cewa, kayayyakin su na sawa da wasu tarin kayayyaki da dama ne suka ƙone ƙurmus, lamarin da ya nemi ɗaukin mahukunta da su kai musu ɗauki bisa halin da suka samu kan su a ciki.
Manyan Labarai
Ba kan ta: An sace birkin jirgin sama guda 80 a Kano
Kotun majistret mai lamba 70 da ke jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Faruk Ibrahim Umar, ta aike da wasu mutane gidan ajiya da gyaran hali bisa zargin su da haɗa baki da Sata.
Ƙunshin zargin da ake yi wa mutanen ya ayyana cewar, a ranar 11 ga watan 12 na shekarar da ta gabata ta 2025, wani mutum mai suna Otaru Bashir ma’aikaci a kamfanin sifirin jiragen sama na Azman, ya yi ƙorafi cewar mai gadin kamfanin nasu ya haɗa baki da wasu mutane sun sace musu birkin jirgin sama guda 80.
Ana dai zargin mutanen ne da sace waɗannan barakun wato birkin jirgin sama guda tamanin a filin jirgin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano.
Mutanen da ake zargin sun hadar da Nuhu Auwalu da Yakubu Bala da Emanuel Luka, sai kuma safiyanu Abdullahi.
Ko da aka karanta wa mutanen ƙunshin zargin da ake yi musu dukkaninsu sun musanta, a nan ne kotun ta aike da mutanen gidan gyaran hali tare da sanya ranar 11 ga watan gobe dan sauraron shaidu akan shari’ar.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewar, yayin zaman kotun an ambata cewar, binciken ƴan sanda ya bayyana cewar kimar kayan ya kama Naira miliyan dari da arba’in, sai dai yayin bincike an gano birkin jirgin guda uku a hannun wanda ake zargi na uku mai suna Yakubu Bala.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su