Labarai
Sanar da gwamnati ƙuncin rayuwar da ake ciki ta shafukan sada zumunta yafifita zanga-zanga – Human Rights
Shugaban ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Sustainable Growth Initiatives for Human Rights Deplolopment ta kasa, kwamared Abubakar Musa Abdullahi, ya ce mai-makon masu shirya zanga- zangar tsadar rayuwa su fito kan tituna da kwalaye ko kuma riƙe Makami, yafi dacewa su mayar da hankali kan rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta, domin nusar da gwamnati damuwar su.
Daraktan kungiyar a nan Kano Kwamared Abubakar Musa Abdullahi ne ya bayyana hakan yayin zantwar sa da gidan rediyon Dala FM Kano, a ranar Talata,
Ya ce gujewa hawa kan titunan yayin zanga-zangar tsadar rayuwar ka iya taimakawa wajen gujewa lalata kadarorin gwamnati da ma dukiyoyin al’umma.
Da yake nasa jawabin mai magana da yawun kungiyar sintirin Bijilante ta jihar Kano Usman Muhammad Ɗan-daji shawartar matasa ya yi, da su guji daukar makamai ko kuma karya doka yayin zanga-zangar lumanar da ake shirin gudanarwa, domin gujewa yin dana sani wanda ka iya janyo musu faɗawa hannun jami’an tsaro.
“Ƙungiyar mu ƙarƙashin jagorancin kwamandan ta Ubale Barau Muhammad Badawa, yanzu haka ta shirya tsaf wajen baza jamai’an mu a lungu da sakunan Kano, domin samar da tsaro a tsakanin al’umma, musamman a lokutan zanga-zangar, “in ji Ɗan-daji”.
Wannan dai na zuwa ne yayin da wasu mutane musamman ma Matasa suka shirya gudanar da zanga-zangar lumana akan tsadar rayuwar da aka samu kai a ciki, bayan da suka sanya ranar 1 zuwa 10 ga watan Augusta mai kamawa, domin gudanar da ita don sanar da gwamnatin tarayya halin matsin rayuwar da ake ciki.
Labarai
Ku guji tada hankalin al’umma yayin zaɓen ƙananan hukumomi a Kano – Human Right
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network, ta buƙaci al’umma musamman ma Matasa da su kasance masu bin doka da oda tare kuma da gujewa tayar da hankalin jama’a a yayin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin da za ayi a yau Asabar.
Shugaban gudanarwar ƙungiyar na Ƙasa Kwamared Tasi’u Idris Idris (Soja) ya bayyana wa tashar Dala FM Kano, hakan a safiyar Asabar.
Ya kuma ce bai kamata al’umma su kasance masu taka doka ba, domin bin doka shi ne wayewa.
“Muna kuma kira ga jami’an tsaro da su bada gudunmawar su yayin zaɓen domin ganin an gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin cikin kwanciyar hankali, “in ji Tasi’u”.
Da yake nasa jawabin daraktan ƙungiyar Kwamared Gambo Madaki, kira ya yi ga dukkanin ƴan ƙungiyar su na ƙananan hukumomin Kano 44, da ku guji sanya kayan ƙungiyar su yayin gudanar da zaɓen kasancewar ba sa cikin masu aikin zaɓen ko kuma sanya ido, domin gujewa fuskantar matsala.
Tuni dai hukumar zaɓe ta jihar Kano Kanseic, ta ce za’a fara kaɗa ƙuri’a ne da misalin ƙarfe takwas na safiyar yau Asabar.
Labarai
Sarkin Kano ya ɗaga likkafar Alhaji Abbas Ɗalhatu daga Ƴan Daka, zuwa Bauran Kano, da naɗa hakimai 10
Mai martaba sarkin Kano Dakta Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya naɗa Alhaji Abbas Ɗalhatu shugaban rukunin gidajen Freedom Radio da Dala FM, a matsayin Bauran Kano, bayan da ya ɗaga likkafar sa daga Ƴan Ɗakan Kano.
Sarkin ya naɗa hakiman ne da safiyar yau Juma’a, inda ya kuma naɗa hakimai goma a matakai daban-daban, daga cikin su akwai Kacallan Kano, da Dan Adalan Kano, da mai unguwar Munduɓawa kuma hakimin Gezawa, da sauransu.
Da yake jawabi jim kaɗan da ɗin hakiman da kuma ɗaga likkar Alhaji Abbas Ɗalhatu zuwa Bauran Kano, mai martaba Sarkin Kano Dakta Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya ce an naɗa hakiman ne bisa jajirecewar su da taimaka wa al’umma da kuma biyayya ga masarautar Kano.
Sarkin na Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya kuma hori dukkanin hakiman da su mayar da hankali akan samar da ci gaban al’ummar jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.
Wakilinmu Yakubu Ibrahim Doragarai ya ruwaito cewa a yayin naɗin al’umma da dama ne suka samu damar halarta daga ciki da wajen ƙasar nan.
Labarai
Ya kamata a gaggauta isar da tallafin da aka samu ga iyalan waɗanda iftila’in tankar Mai ya rutsa da su a Jigawa – Human Right
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network, ta yi kira ga gwamnatin jihar Jigawa, da ta gaggauta isar da tallafin da gwamnatoci da kuma wasu manyan mutane suka bayar ga waɗanda iftila’in fashewar tankar dakon man fetur ya rutsa da su a garin Majia da ke ƙaramar hukumar Jigawa, al’amarin da ya shafi sama da mutane 250.
Shugaban gudanarwar ƙungiyar na ƙasa Kwamared Tasi’u Idris Idris (Soja) ne ya bayyana hakan yayin zanatawar sa da tashar Dala FM Kano, a ranar Lahadi 20 ga watan Oktoban 2024.
A ranar Talatar da ta gabata ne dai wata babbar motar dakon man ta samu haɗari a garin Majia da ke jihar ta Jigawa, inda ta kama da wuta da hakan ya yi sanadiyyar rasuwar kusan mutane 170, yayin da fiye da mutum 100, ke kwance a Asibitoci daban-daban da suke karɓar kulawar likitoci bisa ƙonewar da sassan jikin su ya yi.
Tasi’u Idris ya kuma jajanta wa gwamnati da dukkanin al’ummar jihar Jigawa, kan faruwar al’amarin inda ya kuma miƙa ta’aziyyar su da jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa dasu.
A cewar sa, “Muna kira ga gwamnatin jihar Jigawa da ta gaggauta gyara wurin da motar dakon man ta yi haɗari bisa yadda titin yake haddasa haɗari tare da asarar rayuka da kuma dukiyoyin al’umma a wurin domin daƙile faruwar irin hakan a gaba, “in ji Soja”.
Rahotanni sun bayyana cewar yanzu gwamnoni da manyan ƴan kasuwa da ƴan siyasa da dama ne suka bayar da gudunmawar su domin ragewa iyalan waɗanda lamarin ya shafa wani raɗaɗi, inda zuwa yanzu aka samu sama da tallafin Naira Miliyan dubu ɗaya.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su