Connect with us

Labarai

Hukumar gidajen gyaran hali ta Kano ta gargaɗi ƴan Film ɗin da suke nuni da cin mutumcin ta

Published

on

Hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali na jihar Kano, ta ce ba za ta lamunci yadda wasu masu shirya Fina-finai suke amfani da kayan ta ko kuma wani ɓangare nata ba, kuma ba tare da ambasu umarni ba, wanda a wasu lokutan suke nuni da ɓatanci ga hukumar.

Mai magana da yawun hukumar SC Musbahu Lawan Ƙofar Nassarawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa gidan rediyon Dala FM, a ranar Laraba 31 ga watan Yulin 2024.

Ya ce ko kusa ko alama ba za su zuba idanu kan yadda wasu masu shirya Fina-finai suke amfani da kakin ta ko kuma wani ɓangare na gidajen ana cin mutumcin ta ba, yana mai cewa zasu rinƙa ɗaukar mataki akan irin hakan.

“Dukkanin waɗanda za su yi amfani da kayan hukumar mu ko kuma wani ɓangaren mu su rinƙa tuntuɓar mu, domin basu ƙa’idojin dokar hukumar, domin gujewa abinda ka iya zuwa ya dawo, “in ji SC Musbahu”.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya ruwaito cewa, SC Musbahu Lawan Ƙofar Nassarawa, ya kuma miƙa godiyar su ga al’umma bisa yadda suke bata haɗin kai tare da tallafawa mazauna gidajen gyaran halin.

Labarai

Komawa makaranta: Ya kamata Gwamnatin Kano ta wadata motocin jigilar ɗalibai – Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Rights Network, ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano, da ta ƙara wadata motocin ɗaukar ɗalibai a faɗin jihar, domin taimakawa ɗalibai wajen jigilar su zuwa makarantn su, domin samun dama wajen zuwa makaranta akan lokaci.

Babban jami’in gudanarwar ƙungiyar a matakin ƙasa Tasi’u Idris Idris (Soja) ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, a ranar Talata 17 ga watan Satumban 2024.

Ya ce ƙara wadata motocin daga ɓangaren gwamnatin jihar Kano, ka iya taimakawa ɗalibai wajen zuwan su makaranta akan lokaci ba tare da makara ba, musamman ma bisa la’akari da yadda wasu masu baburan adai-dai ta sahu suke ƙauracewa ɗaukar su bisa tsadar fan Fetur.

“Muna kira ga matuƙa baburan Adai-dai ta sahu da ke jihar Kano, da su rinƙa ɗaukar ɗaliban da suka fito domin zuwa makaranta, domin taimakawa karatun su, “in ji Tasi’u”.

Sai dai jami’ar da ke kula da harkokin ilmin Ƴaƴa Mata a ma’aikatar ilimi ta jihar Kano, Amina Kasim, ta ce tun kafin a koma makaranta ma’aikatar Ilmi ta yi shiri wajen inganta motocin da za su yi jigilar ɗalibai zuwa makarantun su.

Amina Kasim ta ci gaba da cewa, “Tun da safiyar wannan rana motocin mu suka fara zirga-zirga suna ɗaukar ɗalibai ana kai su makaranta, waɗanda aka gani jibge a bakin hanya irin waɗanda suka raina motocin gwamnati ne suke cewa wai ta sada ce, “in ji ta”.

Wannan dai na zuwa ne yayin da daliban makarantun Sakandire da na Firamare suka koma makarantun su bayan dogon hutun da suka sha, domin fara karatu zangon farko na shekara ta 2024/2025.

Continue Reading

Labarai

Za’a fara yiwa ɗalibai gwajin Ƙwaya kafin su shiga kwaleji a Kano

Published

on

Kwalejin fasaha ta jihar Kano, Poly Technic, za ta fara gwajin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ga ɗaliban da za su nemi gurbin karatu a shekara mai zuwa ta 2025.

Shugaban kwalejin Dakta Abubakar Umar Faruk, ne ya bayyana hakan yau Asabar, a yayin taron wayar da kan ɗalibai illar Shan miyagun ƙwayoyi domin kare kai daga cin zarafin Jinsi, da ƙungiyar ɗaliban kwalejin ta shirya.

Taron ya gudana ne a ɗakin taro na Farfesa Hafiz Abubakar, da ke reshen kwalejin na matan fada, da ke jihar Kano.

Shugaban kwalejin wanda maga-takardar makarantar Muhktar Ibrahim Bello, ya wakilta, ya ƙara da cewar matakin gwajin ta’ammali da miyagun ƙwayoyin hakan zai taimaka wajen yaƙi da miyagun kwayoyi a kwalejin da ma jihar Kano.

Da yake na sa jawabin akan dabarun kaucewa Shaye-shaye kwamandan hukumar NDLEA ta ƙasa reshen jihar Kano, Abubakar Idris Ahmad, wanda mataimakiyar sa Hajjiya Aisha Hamidu,ta wakilta, ya ce ta hanyar wayar da kai ne ɗalibai da matasa za su gane illar amfani da miyagun ƙwayoyi.

A nasa ɓangaren shugaban kungiyar ɗaliban ƴan asaln jihar Kano, da suka shirya taron Abdurrazak Nasiru Ahali, ya ce sun shirya taron ne domin wayar da kan ɗalibai akan illar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, ta yadda za su kaucewa amfani da su.

Taron faɗakar da ɗaliban illar miyagun kwayoyin yasamu halartar malamai,masu rike da sarautar gargajiya da sauran masana a fannin Ilimi da lafiya.

Continue Reading

Labarai

Mun ƙaddamar da kwamitin karta-kwana da zai kawo ƙarshen cutttuka masu yaɗuwa a Kano – Abba Kabir Yusuf

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da kwamitin kar-ta kwana da zai dunga shiga lungu da saƙo na jihar, domin yin riga-kafin cututtuka don kare jihar daga barazanar kamuwa da cutuka masu yaɗuwa.

Kwamitin dai an kafashi ne ƙarƙashin jagorancin mataimakin Gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda zai jagoranta.

Da yake ƙaddamar da kwamitin a ranar Alhamis gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da cewa kwamitin da aka ƙaddamar zai gudanar da aikin sa ne yadda ya kamata, ta yadda za’a dunga shiga lungu da saƙo na jihar domin magance duk wasu cututtuka masu yaɗuwa a faɗin jihar.

“Muna kuma kira ga dukkanin waɗanda aka naɗa a wannan Kwamitin da su tabbatar da cewa sun gudanar da aikin su yadda ya kamata wajen riƙe gaskiya da amana, “in ji gwamnan”.

Da yake jawabi a matsayin shugaban kwamitin mataimakin Gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya tabbatar wa da gwamnan cewa za su gudanar da aikin su yadda ya kamata domin ciyar da Kano gaba da kare ta daga barazanar cututtuka masu yaɗuwa.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, an samarwa da kwamitin baburan hawa guda 88 inda aka karrama masu maganin gargajiya da lambar girmamawa yayin taron ƙaddamar da kwamitin.

Continue Reading

Trending