Connect with us

Labarai

Alhazan Najeriya 30 ne suka rasu a aikin hajjin 2024 – NAHCON

Published

on

Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON, ta tabbatar da cewa kimanin Alhazan Najeriya 30, ne suka rasu a lokacin gudanar da ibadar aikin Hajjin da ya gagabata na shekarar 2024.

Shugaban hukumar Malam Jalal Ahmad Arabi, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Ya kuma ce wasu Alhazan Najeriya biyar sun rasu ne saboda tsananin zafin ranar da akeyi a kasar Saudi Arebia, a yayin da sauran Alhazan Najeriya suka rasu a dalilin rashin lafiya daban-daban.

Jalal Arabi ya kara da cewa babbar matsalar da suka fuskanta a lokacin gudanar da ibadar aikin Hajjin da ya gabata, bai wuce matsalar tashin farashin Dalar Amurka ba, wanda hakan yasa farashin kuɗin kujerar aikin Hajjin da ya gabata yayi tashin gauron zabi.

Shugaban na NAHCON, Malam Jalal Arabi ya kuma yabawa gwamnatin shugaba Tunibu bisa irin yadda ya yi ƙoƙari wajen tallafawa Alhazan Najeriya.

Hukumomin kasar Saudi Arebia sun ce sama da Alhazai dubu daya da dari biyar ne suka rasu a aikin Hajjin da ya gabata a fadin duniya, wasu saboda zafin rana wasu kuma saboda rashin lafiya a yayin da wasu kuma sun rasu ne ta hanyar haɗarin ruguzowar gini a ƙasar.

Labarai

Rashin kishin al’umma ne ya sa wasu Ƴan Majalisun Arewa suka amince da ƙudirin dokar gyaran Haraji – Human Right

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network, ta ƙalubalanci ƴan majalisun ƙasa, waɗanda suka amince da ƙudirin dokar gyaran haraji da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aike wa zauren majalisar domin amincewa da shi.

Shugaban gudanarwar ƙungiyar na Ƙasa Kwamared Tasi’u Idris Idris (Soja) shi ne ya bayyana hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano, a ranar Lahadi, ya ce duba da tsananin rayuwar da al’ummar ƙasar nan musamman ma na Arewa suke ciki, sam bai kamata shugabannin Arewan su amince da dokar gyaran harajin ba.

A ranar Alhamis ne dai ƙudirin dokar gyaran harajin ya tsallake karatu na biyu a zauren Majalisar Dattawa ta Najeriya, al’amarin da ke ci gaba da janyo cece-kuce a tsakanin al’umma, kuma daga cikin waɗanda suka nuna rashin amincewar su da dokar harajin har da sanatan Borno ta Kudu Ali Ndume, da gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zullum.

A cewar sa, “Ko kusa ko alama bai kamata ƴan majalisar Dattawa da na Wakilai su amince da ƙudirin gyaran dokar harajin ba, domin hakan ka ƙara kassara al’amuran Al’ummar arewacin ƙasar; muna kira ga shugabannin mu su kaucewa amincewa da dokar harajin domin ceto yankin su daga ƙangin ƙuncin rayuwa, “in ji Tasi’u Soja”.

Shugaban gudanarwar ƙungiyar ya kuma ce abin kunya ne da rashin kishin al’umma, kan yadda mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Barau I Jibril, da sanatan Kano ta tsakiya Rufa’i Sani Hanga, da wasu shugabannin Arewa suka amince da ƙudirin dokar, domin ba abu ne da zai haifar wa Arewa Ɗa mai ido ba.

Tasi’u Soja, ya kuma yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tunibu, da dukkanin shugabanni a Najeriya, da su dakatar da batun gyaran dokar harajin bisa yadda zai iya haifar da matsala a ƙasar.

Continue Reading

Labarai

Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya naɗa Ɗan Sa a matsayin Chiroman Kano.

Published

on

Mai martaba sarkin Kano Dakta Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya buƙaci dukkanin hakimansa da ke faɗin jihar nan da su mayar da hankali wajen gudanar da aikin su bisa gaskiya da riƙon Amana.

Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, kuma babban ɗan fadar Sarki, yau Juma’a a fadar sa.

Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya ce ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, ne bisa cancanta da zuminci da kuma gogewarsa akan aikinsa na ƴan sanda, tare kuma da taimakawa al’umma da yake yi a koda yaushe.

Mai martaba sarkin ya kuma taya Chiroman Kano, murna bisa wannan naɗin da aka yi masa, tare da fatan zai zamo jakada na gari musamman wajen samar da cigaban Al’umma da kuma masarautar Kano.

Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa taron naɗin ya samu halartar gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da sarakunan gargajiya daga wasu daga cikin jahohin ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Za mu magance matsalolin da hukumar Hisbah ta Dala ke fuskanta – Shugaban ƙaramar hukumar Dala

Published

on

Ƙaramar hukumar Dala ta ce za ta yi bakin ƙoƙarin ta wajen magance matsalolin da hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala ke fuskanta, domin ƙara ƙarfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukan al’umma.

Shugaban ƙaramar hukumar Suraj Ibrahim Imam ne ya bayyana hakan, a lokacin da jami’an hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala, suka ziyarce shi a ofishinsa, domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da suka yi, tare da sanar dashi halin da hukumar Hisbar ke ciki a halin yanzu.

“Daga cikin ƙalubalen da zan yi ƙoƙarin magance wa akwai samar da ruwa da wutar lantarki da kuma samar wa hukumar kayan aiki, bisa yadda suke fama da rashin su, “in ji Suraj Imam”.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Dala Sura ya kuma yi kira ga babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da ya ƙara kulawa da walwalar hukumar ta ƙaramar hukumar Dala bisa ƙalubalen da suke fuskanta.

Da yake nasa jawabin kwamandan hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala Mallam Umar Bala Muhammad, ya ce sun ziyarci shugaban ƙaramar hukumar ne domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da kuma sanar da shi halin da hukumar ke ciki, domin haɗa ƙari da ƙarfe wajen magance ƙalubalen da suke fuskanta.

Wakiliyarmu Hadiza Balanti ta rawaito cewa Mallam Umar Bala ya kuma ƙara da cewa a shirye hukumar hisbar ta ƙaramar hukumar Dala take wajen gudanar da ayyukan al’umma babu gajiyawa.

Continue Reading

Trending