Manyan Labarai
Idan zanga-zanga ta zama dole ku gujewa tada hankalin al’umma – Zauren haɗin kan Malamai na Kano
Zauren haɗin kan malamai na jihar Kano ya ja hankalin masu yunƙurin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa kan cewa matuƙar ta zama dole suyi, to su gujewa tayar da hankalin al’umma da kuma kaucewa yin abinda ka iya jawo cutar da jama’a.
Shugaban zauren haɗin kan malaman na Kano Farfesa Musa Muhammadu Borodo, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da aka aikowa Dala FM, a daren Larabar nan, ya ce halin da ake ciki na matsi da rashin tsaro, hali ne da yake damun al’umma, amma dai ayi duba na tsanaki akan fita zanga-zangar idan ya zama dole ayi.
“Mutane subi hanyoyin da za’a zauna lafiya tare da tattara wajen tabbatar da cewa an samu tsaro na tare da an bari zanga-zangar ta haifar da tashin hankali ba, “in ji shi”.
Farfesa Musa Burodo, ya kuma ƙara da cewa, yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi abinda ya dace dan ganin al’umma sun samu sauƙi daga cikin halin ƙuncin rayuwar da al’umma suka samu kan su yanzu a ciki.
A cewar sa, “Jama’a su sani a wannan ƙasa tamu tarihin zanga-zanga da aka sha yi a ƙasar bai zamana alkhairi a gurin mu ba, kullum cuta ake samu daga jama’a a dukiyoyi, bayan a aka gudanar akan san rai, “Cewar Farfesa Borodo”.
Majiyar Dala FM Kano, ta rawaito cewa, hakan na zuwa ne bayan da wasu matasa suka shirya gudanar da zanga-zangar lumana akan tsadar rayuwar da aka samu kai a ciki, domin sanar da gwamnatin tarayya halin da suke ciki dan ɗaukar mataki.
Manyan Labarai
Wata Sabuwa: Lauya ya nemi kotu ta kama kwamishinan Shari’a na jihar Kano
Wani lauya mai zaman kan sa a jihar Kano Barista Haruna Musa Muhammad, ya yi ƙorafi a gaban babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar, akan ta kama kwamishinan Shari’a na jihar Kano Barista Haruna Isah Dederi, da wasu manyan mukarraban gwamnatin jihar.
Lauyan wanda yake wakiltar mai kara Nura Bashir Ahmad, ya bayyana cewar gwamnatin jihar Kano ta rushe wa Nura gida duk da cewar ya samu hukunci a babbar kotun tarayya akan kada a rushe masa gidan.
Cikin wata ƙunshin Shari’a mai lamba FHC/KN/CS/240/2023, mai Shari’a Simon Amobida, ya ayyana cewar kotun tarayya ta gamsu da takardun mallaka da mai ƙara Bashir Ahmad ya gabatar mata, don haka ne ma ta ayyana cewar gidan mallakinsa ne.
Kotun dai tun a ranar 13 ga watan biyu na shekarar da ta gabata ta 2024, ta zartas da hukuncin akan batun.
Mai karar Bashir ta bakin lauyansa Barista Haruna Musa, sun bayyana cewar sun rubuta koke zuwa gaban kotun da ta yi hukuncin tun da dai suna zargin waɗanda ake ƙarar sun raina wannan hukunci kamar yadda ya bayyana a zantawar sa da wakilin Dala FM Kano.
Akan wannan batu ne wakilin namu ya tuntuɓi kwamishinan Shari’a na jihar Kano Barista Haruna Isah Dederi, ta wayar salula, sai dai bai samu damar ɗaa wayar ba, ya kuma aike masa da gajeren saƙon kar ta kwana nan ma bai bada amsa ba, amma yana dakon sa.
Manyan Labarai
Budurwa ta mutu yayin wata Gobara da ta kama cikin gidan su a Kano
Wata Gobara da ta tashi a wani gida ta yi sanadiyyar rasuwar wata budurwa a unguwar Ja’en Sabere da ke ƙaramar hukumar Gwale a Kano da ke arewacin Najeriya, tare da ƙonewar wasu sassan gidan.
Mamallakin gidan da lamarin ya faru mai suna Saminu Abba ne ya tabbatar wa tashar Dala FM faruwar lamarin a ranar Alhamis, 16 ga watan Janairun 2025.
Ya ce gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe ɗaya na daren jiya Laraba, lamarin da jami’an hukumar kashe Gobara ta jihar Kano da ma ƴan Bijilanten yankin da sauran al’umma suka kai ɗauki.
“Muna cikin Bacci muka ji wata ƙara da ihun mutanen unguwa, da muka tashi muka ga Gobara ce ta tashi a wasu sassan gidan mu kuma wutar ta tare hanyar da za mu fita gashi tana ci ba ƙaƙƙautawa, “in ji Saminu”.
Ya ci gaba da cewa, “Bayan jami’an hukumar kashe Gobara da ƴan Bijilanten yankin, da sauran al’umma sun kawo musu ɗauki, ne aka fasa Gini ta gidan maƙotan su inda su shida suka fita daga gidan sai dai ƴar su budurwa mai shekaru 18 mai lalurar Sikila ta rasu”.
Mallam Saminu Abba ya ƙara da cewa, kayayyakin su na sawa da wasu tarin kayayyaki da dama ne suka ƙone ƙurmus, lamarin da ya nemi ɗaukin mahukunta da su kai musu ɗauki bisa halin da suka samu kan su a ciki.
Manyan Labarai
Ba kan ta: An sace birkin jirgin sama guda 80 a Kano
Kotun majistret mai lamba 70 da ke jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Faruk Ibrahim Umar, ta aike da wasu mutane gidan ajiya da gyaran hali bisa zargin su da haɗa baki da Sata.
Ƙunshin zargin da ake yi wa mutanen ya ayyana cewar, a ranar 11 ga watan 12 na shekarar da ta gabata ta 2025, wani mutum mai suna Otaru Bashir ma’aikaci a kamfanin sifirin jiragen sama na Azman, ya yi ƙorafi cewar mai gadin kamfanin nasu ya haɗa baki da wasu mutane sun sace musu birkin jirgin sama guda 80.
Ana dai zargin mutanen ne da sace waɗannan barakun wato birkin jirgin sama guda tamanin a filin jirgin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano.
Mutanen da ake zargin sun hadar da Nuhu Auwalu da Yakubu Bala da Emanuel Luka, sai kuma safiyanu Abdullahi.
Ko da aka karanta wa mutanen ƙunshin zargin da ake yi musu dukkaninsu sun musanta, a nan ne kotun ta aike da mutanen gidan gyaran hali tare da sanya ranar 11 ga watan gobe dan sauraron shaidu akan shari’ar.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewar, yayin zaman kotun an ambata cewar, binciken ƴan sanda ya bayyana cewar kimar kayan ya kama Naira miliyan dari da arba’in, sai dai yayin bincike an gano birkin jirgin guda uku a hannun wanda ake zargi na uku mai suna Yakubu Bala.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su