Connect with us

Manyan Labarai

Yadda aka gudanar da sallar Alƙunutu tare da addu’o’i akan matsin rayuwa da rashin tsaro a Kano

Published

on

Da safiyar Larabar nan ne al’ummar unguwar Ja’en bakin Diga, da kewaye, da ke yankin ƙaramar hukumar Gwale a Kano, suka gudanar da sallar Alƙunutu tare da yin addu’o’i, domin neman sauƙi a wajen Ubangiji S.W.T, daga tsadar rayuwar da suka samu kan su a ciki, a Najeriya.

Yayin gangamin sallar Alƙunutun da addu’o’in al’ummar yankin na Ja’en bakin Diga maza da mata, manya da yara, ne suka samu damar halarta, domin nuna goyon bayan su akan al’amarin.

Guda daga cikin jagororin malaman da suka jagoranci sallar Alƙunutun da addu’o’in, Mallam Aminu Datti Liman, ya shaidawa Dala FM Kano, cewa, bayan gudanar da sallar sun kuma gudanar da addu’o’i domin neman sauƙi a wajen Allah Maɗaukakin sarki, daga halin ƙuncin rayuwar da aka samu kai a ciki.

A cewar sa, “Ko a ranar Litinin 5 ga watan Agustan 2024, mun yi irin wannan taruwa, kuma ranar Juma’a ma zamu ƙara gabatarwa, domin daga ranar Litinin da muka fara gudanarwa mun fara ganin sauyi duba da saukar ruwan sama da aka rinƙa yi kuma zamu ci gaba, “in ji Mallam Aminu”.

Ya kuma ƙara da cewa, akwai buƙatar al’umma musamman ma Matasa su kaucewa tayar da hankalin al’umma, da kuma gujewa satar kayayyakin Mutane da na gwamnati, domin Allah S.W.T., baya yafe haƙƙin wani akan wani.

Mallam Aminu Datti, ya kuma ci gaba da cewa, Matasan da suka ɗebi kayayyakin gwamnati da na al’umma yayin gudanar da zanga-zangar lumana akan tsadar rayuwa, za su iya mayar wa ko kuma su bayar a mayar a wuraren da suka ɗebo, domin gujewaa fushin Ubangiji S.W.T.

Wannan dai na zuwa ne bayan da wasu dandazon Matasa suka ɗauki gaɓarar gudanar da zanga-zangar lumana akan tsadar rayuwa, wanda suka fara daga ranar 1 ga watan Agustan 2024, da suka ce zasu shafe kwanaki goma suna gudanarwa, inda ake ranar ta shida a yau.

Manyan Labarai

Ɗan Bijilante ya rasa ransa bisa arangamar su da wasu ƴan Daba a Kano

Published

on

Ƙungiyar sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamandan ta Ubale Barau Muhammad Badawa, ta tabbatar da rasuwar guda daga cikin jami’in ta mai suna Suraj Rabi’u mazaunin Jaba da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar, sakamakon arangama da ƴan Daba.

Mai magana da yawun ƙungiyar Bijilante na jihar Kano, kuma Kwamandan ta na ƙaramar hukumar Fagge, Usman Muhammad Ɗan Daji, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM Kano a ranar Lahadi.a

“Jami’in Bijilanten namu ya rasa ran nasa ne sakamakon arangama da suka yi da wasu Ƴan Daba yayin gudanar aikinsu a ranar Idin ƙaramar Sallah, inda ƴan dabar suka soke shi da Ɗanbida a Ƙirji da bayansa, wanda ya yi sanadiyar rasuwarsa, “in ji Usman”.

Ya kuma ce, an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi mai suna Usman Sharif mazaunin ƙaramar hukumar Dala, kuma tuni aka miƙa shi hannun jami’an tsaro.

Usman Ɗan daji, ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan jami’in nasu ya gafarta masa.

Continue Reading

Manyan Labarai

An ga watan ƙaramar Sallah a Najeriya – Sarkin Musulmi

Published

on

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya, inda za a yi karamar Sallah gobe Lahadi.

Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a yayin jawabin da ya gabatar a cikin daren Asabar ɗin nan, ya ce sun samu rahotannin ganin watan ne daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce daga cikin guraren da aiko musu da ganin jinjirin watan na Shawwal akwai Zazzau, da kuma daga Sarkin Dutse, da Arugungu, da kuma Shehun Borno, da dai sauran gurare daban-daban na Najeriya.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su gabatar da bikin sallar cikin kwanciyar hankali, tare da taimaka wa mabuƙata.

Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, biyo bayan sanarwar fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, ya kasance ranar Lahadi take 1 ga watan Shawwal na shekarar 1446, wato ranar ƙaramar Sallah.

Continue Reading

Manyan Labarai

Shugaba Tinubu da Sifeton Ƴan Sanda ku bi wa mutanen mu da aka yi wa kisan gilla hakƙin su – Rt. Hon. Rurum

Published

on

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Rabo, Kibiya da Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum, ya bayyana kaɗuwar sa bisa kisan gillan da aka yi wa wasu Mafarauta su kusan 16, a garin Uromi da ke jihar Edo, a lokacin da suke hanyar su ta komawa Kano daga jihar Rivers.

Honarable Kabiru Rurum, ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da aka aikowa Dala FM Kano a ranar Asabar, ya ce daga cikin mutanen da aka ƙona akwai mutum 11 da suka fito daga mazaɓun yankin sa na Kibiya da Bunkure, inda wasu 6 suka samu muggan raunuka suna karɓar Magani yanzu haka a jihar Edo.

A cewar Ɗan Majalisar, “Wannan abu da matasan garin Uromi a jihar Edo, suka yi ya saɓa da dokar kasa, kuma mummunan laifi ne, a don haka za mu bi kadin hakƙin mutanen mu da aka kashe a kuma waɗanda aka jikkata, “in ji shi“.

Kabiru Rurum, ya ce a matsayinsa na wakilin mutanen da aka kashe a majalisar Wakilai ta ƙasa, yana kira ga shugaban Najeriya Bola Tinubu, da babban Sifeton ƴan sanda, da su yi duk mai yiyuwa wajen ganin an kamo waɗanda suka yi wannan aika-aikar tare da hukunta su, da kuma biyan diyya ga iyalan waɗanda suka rasu da kula da waɗanda suka jikkata.

“Kasancewar wannan bashi ne na farko da ake samun wasu ɓata gari na tare matafiya akan hanya da basu ji ba basu gani ba su kashe su, a don haka muna fatan wannan karon gwamnati da sauran hukumomin tsaro za su ƙaddamar da ƙwaƙƙwaran bincike don ɗaukae mataki kamar yadda dokar kasa ta tanada, “in ji Rurum”.

Ɗan majalisar ya kuma jajantawa dukkanin al’ummar jihar Kano musamman Iyalan waɗanda suka rasu, tare da addu’ar Allah ya gafarta musu yasa Jannatul Firdausi makomar su, su kuma waɗanda suka jikkata Allah ya basu lafiya.

Continue Reading

Trending