Connect with us

Manyan Labarai

An kama mutumin da ake zargi da damfarar wasu mata wajen karɓar musu kuɗaɗe da zummar zai samar musu aiki a Kano

Published

on

Rundunar tsaro ta Civil Defense a nan Kano ta kama wani mutum da zargin laifin damfarar wasu mata wajen karɓar kudadensu da sunan zai samar musu aiki a wasu hukumomin gwamnati da na tsaro.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar SC Ibrahim Idris Abdullahi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikowa Dala FM a ranar Laraba.

Ya ce mutumin mai suna Mu’azu Muhammad Ibrahim, da ke unguwar Sagagi sun kamashi ne sakamakon korafe – korafen da suka samu daga wasu mata da suka bayyana musu cewa, ya karbi kudinsu sama da Naira miliyan ɗaya da dubu dari ɗaya da sunan zai nemar musu aiki, duk da bashi da damar hakan.

“A lokacin da jami’an mu suka binciki mutumin ya shaida musu cewa tabbas ya karɓi wadannan kuɗaɗen a wajen matan da summar zai samar musu aikin amma kuma al’amarin ƙarya ne bashi da takardun samar da aiki ko hanyar su, “in ji SC Ibrahim”.

SC Ibrahim ya kuma ƙara da cewa da zarar rundunar ta kammala binciken ta akan wanda ake zargi zata gurfanar dashi a gaban Kotu.

Da yake nasa jawabin mutumin da ake zargin mai suna Mu’az Muhammad Ibrahim, ya tabbatar da karɓar kuɗaɗen sai dai ya ce wasu kuɗaɗen suna hannun wata mata, amma dai ya yi nadama ba zai ƙara ba.

“Aƙalla watanni shida ke nan da fara bayar da kuɗaɗen nasu, abinda muka yi ba dai-dai ba ne kuma muna neman afuwa akai ba zamu sake ba, “in ji mutumin”.

Rundunar Civil Defense ɗin a jihar Kano, ta kuma ja hankalin al’umma da su rinƙa yin taka-tsantan tare da lura da irin mutanen da suka ce za su samar musu aiki, domin gujewa faɗawa komar ɓata gari.

Manyan Labarai

Kwana biyu ya rage mu maka jam’iyyar NNPP a Kotu bisa zargin ƙin adalci yayin fidda ƴan takara a Kano – Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam da wayar da kan jama’a, ta Awareness for Human Right and Charity Foundation ta sha alwashin maka jam’iyyar NNPP ta jihar Kano, a kotu, matuƙar ba’a samu masalaha ba kan ƙorafin da suka samu na zargin da wasu masu sha’awar tsayawa takarar Kansila a mazaɓar Ɗandago da Sani Mai Nagge da ke ƙaramar hukumar Gwale suka yi kan take musu haƙƙi wajen tsayar da ƴan takara a mazaɓun nasu.

Daraktan ƙungiyar a matakin ƙasa Kwamared Auwal Usman Awareness ne ya bayyana hakan, yayin wani taron manema labarai da ƙungiyar ta gudanar ranar Laraba a ofishinta.

Wannan na zuwa ne bayan da mai neman tsayawa takarar Kansila a mazaɓar Ɗandago Hadi Shehu Abubakar, da wasu ƴan takarar Kansila a mazaɓar Sani Mai Nagge su biyu wato Mahfouz Musa da Musa Muhammad, dukka a ƙaramar hukumar Gwale, suka shigar da ƙorafin su a ofishin ƙungiyar.

Masu ƙarar sun zargi cewar jam’iyyar ta NNPP ba ta yi musu adalci ba wajen mayar da su saniyar ware, wajen tsayar da ƴan takarar a mazaɓun nasu.

Kwamared Auwal Awareness, ya kuma ce tun bayan da suka karɓi ƙorafin ne suka rubutawa jam’iyyar takarda mai ɗauke da wa’adin kwanaki biyar kan tayi abinda ya dace ko kuma su gauraya a gaban kotu, wanda ya ce yanzu haka wa’adin nasu ya rage kwanaki biyu.

Da yake jawabi tun da farko tsohon ɗan takarar kansilan a mazaɓar Ɗandago Hadi Shehu Abubakar, amadadin sauran masu ƙorafin ya ce, an umarce su ne da suje su yi sulhu akan tsayar da ƴan takarar a baya, amma bayan sun tafi sai sukaji an sanar da ƴan takarar a mazaɓun nasu, a don haka ne suka yi duk mai yiyuwa amma jam’iyyar ta NNPP ba ta yi komai ba, hakan yasa suka shigar da ƙorafin nasu a ofishin ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ɗin.

Akan wannan ƙorafi ne muka tuntuɓi shugaban jam’iyar NNPP ta jihar Kano, Dakta Hashim Sulaiman Dungurawa ta wayar tarho, wanda ya musanta zargin da tsofaffin ƴan takarar suka yi, inda ya ce damar su ɗaya ce idan ba’a yi musu adalci ba su canza jam’iyya.

Ko a baya-bayan nan dai an samu ƙorafe-ƙorafe daga ɓangaren wasu daga cikin ƴan ƴan takararkari kama daga na shugabancin ƙananan hukumomi zuwa kuma na kansila.

Wataƙila ma wannan ce tasa wasu daga cikin masu riƙe da muƙamai a gwamnatin jihar Kano suka fara ajiye muƙamansu irin su Abdullahi Tanka Galadanchi da ya ajiye muƙamin sa a baya-bayan nan, ko da dai yanzu haka zaben ƙananan hukumomin na ƙara tunkaro wa, wanda za’a gudanar a ranar 26 ga watan Oktoban 2024.

Continue Reading

Manyan Labarai

Kano: An gudanar da taron addu’a da sauke Al-kur’ani sau 82 saboda matsalar sace-sace a wata unguwa

Published

on

Al’ummar garin Dan Hassan da ke ƙaramar hukumar Kura a jihar Kano, sun gudanar da addu’o’i da saukar Alkur’ani sau 82 a rana ɗaya, tare da zagayen garin dukkanin su rataye da Alkur’ani mai girma a jikinsu.

Kazalika, al’ummar garin sun kuma haɗa manyan guma gumai a cikin Wuta domin sanya wasu adadin Allurai duk da biyar Allah, ya kawo musu ɗauki kan sace sacen da ake yi musu a gonakinsu da ma cikin gidajensu a yankin.

A zantawa da tashar Dala FM Kano da wasu daga cikin waɗanda suka halacci taron sun ce, kaɗan daga cikin sace sacen da akeyi musu sun haɗar da satar Masara a gona, da yanke Shinkafa, da farin Wake, tare da sace musu Tukwanen girki a cikin gidajen su, da ma wayoyinsu na hannu.

Shima guda daga cikin manyan Malaman da suka jagoranci wannan sauka dama zagaye Alkur’anin mai suna Malam Musa Bawasa, gargaɗi ya yi ga masu aikata irin wadannan sace cece da masu goya musu baya, da su gane cewa tabbas da gaske suka yi, domin ba za su zuba Ido hakan na ci gaba da faruwa ba a fadin garin Dan-Hassan da kewaye.

Wakilinmu Mu’az Musa Ibrahim ya ruwaito cewa da yake nasa jawabin shugaban shirya taron Malam Rabi’u Abdullahi Sarkin Malaman Dan-Hassan, cewa ya yi shirya al’amarin ya zama dole domin sujawa masu wannan ta’ada kunne duba da yadda suka addabesu da ɗauke ɗauke a yankin.

Continue Reading

Manyan Labarai

Takutaha: Mun baza jami’an mu 600 domin samar da tsaro a Kano – Rundunar Anti Snaching Phone

Published

on

Rundunar da ke yaƙi da ƙwacen Waya da faɗan Daba da kuma magance shaye-shaye ta Anti Snaching Phone, da ke jihar Kano, ta ce ta baza jami’an ta kusan 600, domin samar da tsaro ga masu fita bikin Takutaha a sassan jihar.

Kwamandan rundunar, kuma mashawarci na musamman ga gwamnan Kano akan harkokin tsaro Inuwa Salisu Sharaɗa, ne ya shaidawa Dala FM Kano, hakan a ranar Lahadi.

Inuwa Sharaɗa, ya kuma ce jami’an su na farin kaya da ma masu sanye da Kaki za su shiga lungu da saƙo a jihar Kano, domin ganin an gudanar da bikin Takutahar cikin kwanciyar hankali.

A cewar sa “Mun samu rahoto tare da sunayen wasu daga cikin ɓata gari da suke shirin aiwatar da mummunar ɗabi’ar da bata dace ba wajen tayar da hankalin al’umma, kuma zamu yi duk mai yiyuwa wajen ganin mun daƙile aniyar su ba tare da sun samu nasara ba, “in ji Inuwa”.

Ya ƙara da cewa duk wani wuri da aka san akwai ɓata gari a sassan jihar Kano, za su yi duk mai yiyuwa wajen ganin an ɗauki matakin da ya dace domin ƙara wanzuwar zaman lafiya a faɗin jihar Kano.

“Tuni gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bamu umarni domin mu daƙile duk wani abu da ka iya tayar da hankalin al’umma, musamman wajen daƙile, faɗan Daba, ƙwace waya, da sauran Laifuka, kuma a shirye muke domin magance matsalolin, “in ji shi”

Inuwa Sharaɗa ya ce duk wanda ya ga faruwar wani abu da ka iya haifar da matsalar tsaro zai iya sanar da su ta wannan lambar 08137261928, domin kai ɗaukin gaggawa.

A ranar Lahadin nan ne dai ake bikin Takutaha, wanda ɗumbin al’umma a sassan jihar Kano suke zagayen wurare daban-daban tare da ziyarce-ziyarce, har ma da zuwa kan Dutsen Dala, wuri mai ɗumbin Tarihi, a wani ɓangare na murnar zagayowar ranar sunan Ma’aiki Sallallahu alaihi Wasallama.

Continue Reading

Trending