Connect with us

Manyan Labarai

Matsalar Tsaro: Ƴan Daba sun sake kashe mutane biyu a Ɗorayi – Ɗan Fodiyo

Published

on

Wasu matasa da suka addabi unguwar Ɗorayi da faɗan Daba, da sace-sacen kayayyakin jama’a, sun sake lashe aƙalla Mutane biyu bayan da suka hau su da sara da makamai.

Shugaban babban kwamitin Tsaro na unguwar Ɗorayi a jihar Kano Dakta Abdullahi Idris Ɗan Fodiyo, ne ya bayyanawa tashar Dala FM Kano, a ranar Asabar, ya ce, kashe mutane biyun ya biyo bayan yadda wasu tarin matasa suka shiga yankin a daren Alhamis da kuma Juma’ar da suka gabata, riƙe da makamai inda suka rinƙa yin abinda bai kamata ba.

“Lokacin da matasan suka shigo yankin namu riƙe da muggan makamai sun shiga shagon wani mai canji Waya inda suka kwashe Wayoyi guda 115 na mutane da suka kai masa Caji suka gudu dasu kuma har yanzu basu dawo dasu ba, “in ji Ɗan-Fodiyo”.

Malamin ya kuma ce matuƙar ana so a kawo ƙarshen matsalar tsaron da ke addabar unguwar ta Ɗorayi, sai kowa ya bada gudunmawar sa, suma masu shaguna a yankin sai sun rinƙa ajiye makaman da za su rinƙa kare kan su daga matasan da suke addabar su.

Ɗan Fodiyo, ya ƙara da cewa akwai buƙatar a ƙara yawan jami’an tsaro a yankin na Ɗorayi, domin ganin an magance matsalar tsaron da taƙi ci taƙi cinyewa a unguwar.

Majiyar Dala FM Kano, ta rawaito cewa wannan na zuwa ne bayan da wasu tarin matasa suka addabi al’ummar unguwar Ɗorayi da kewaye da faɗa Daba, gami da sace-sacen kayayyaki, al’amarin da ke sanya furgici a zukatan jama’ar yankin.

Manyan Labarai

Wasu ɓata gari sun sace kayan sautin wani masallacin Juma’a a Kano

Published

on

Al’ummar garin Kumbotso a jihar Kano sun wayi gari da ganin yadda wasu ɓata gari suka sace kayayyakin sautin da ake jin ƙarar kiran Sallah, a babban masallacin Juma’ar garin, al’amarin da ya sanya su a cikin damuwa.

Na’ibin limamin masallacin juma’ar mai suna Ibrahim Magaji Bello, ya shaidawa Dala FM Kano cewar, ɓata garin sun shiga masallacin ne a cikin daren Asabar, inda suka yi awon gaba da kayayyakin fitar da sautin bayan da suka farke ƙofar masallacin.

“Daga cikin kayayyakin da ɓata garin suka sace akwai baturan Fitilun da ke amfani da hasken Rana, da na’urar da ke taimaka wa wajen fitar da sauti, da wayar Na’ibin limamin masallacin da dai sauran su, “in ji shi”

Ibrahim Magaji ya kuma ce sace kayayyakin sautin ya sa yanzu haka ta kai ga ba’a jin sautin kiran Sallah, daga unguwanni daban-daban, da suka haɗar da garin na Kumbotso, da Rigafada, da Chalawa, da sauran wasu unguwanni, domin yanzu mutane suna makara sosai idan za su yi Sallah a masallacin.

“Muna kira ga gwamnati, da dukkanin masu hali da su taimaka su kawo mana ɗauki, domin ganin an sayi wasu kayan sautin a sanya a masallacin, domin ƙara ciyar da addinin Musulunci gaba, “in ji Ibrahim”.

Ya kuma ƙara da cewar tun bayan faruwar lamarin ne suke ta cigiyar waɗanda suka yi aika-aikar wajen zuwa su karɓi kayan su da suka manta yayin aikin nasu.

Ya ci gaba da cewa, “Daga cikin kayayyakin da ɓata gari suka manta akwai Pinches, abun da ake cire Ƙusa, ko kuma Kwaɗo, da Filayar su, da wasu kayayyaki, “in ji Na’ibin”.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamnatin Kano ta kulle ofishin kamfanin jiragen sama na Max Air da na Ɗantata and Sawoe a jihar

Published

on

Gamnatin jihar Kano ta rufe ofishin kamfanin sufurin jiragen sama na Max air da na Dantata and Sawoe a nan Kano, sakamakon harajin da take bin kamfanonin.

Shugaban hukumar tattara haraji ta jihar Kano Dakta Zaid Abubakar, ne ya bayyana hakan bayan kulle kamfanonin biyu a ranar Litinin.

Zaid, wanda Daraktan Bibiyar bashi da tursasawa wajen karɓo bashin harajin da Gwamnatin Kano ke bi, Ibrahim Abdullahi ya wakilta, ya ƙara da cewar hukumar ta tattara haraji ta jihar Kano tabi duk matakan da ya kamata kafin daukar wannan matakin.

“Dole ce ta sa hukumar ɗaukar wannan mataki na rufe kamfanonin da wuraren da ke gujewa biyan haraji a jihar Kano, “in ji Ibrahim Abdullahi”.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar hukumar ta ce za ta ci gaba da bun duk matakan doka akan masu ƙin biyan harajin a fadin jihar Kano.

Continue Reading

Manta Sabo

Kotu ta hana duk wata kafar yada labarai yin labarin da ya shafi Auwalu Danladi Sankara da Taslim Baba Nabegu.

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 4 karkashin jagorancin mai Shari’a Usman Na Abba ta yi hani ga duk wasu Jami’an Ƴan sanda ko na duk wata hukuma ta daban daga gayyata ko tsangwama, ko kuma bincike ko kamawa, ta kowace siga ga kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa Auwalu Ɗanladi Sankara.

Wannan dai na zuwa ne bayan da kotu ta wanke Auwalu Sankara daga zargin mu’amala ko alaƙa da juna tsakanin mai ƙara da Taslim Baba Nabegu har zuwa lokacin sauraran ƙarar.

Kotun ta kuma amince da rokon da wani lauya mai suna Barrister I.C Ekpinovi ya yi amadadin mai kara Auwalu Danladi Sankara wanda ya yi karar Nasiru Buba.

Mai karar ta bakin lauyansa ya bayyana wa kotun rokonsa inda ya roki kotun da ta dakatar da wanda ake kara ko dai shi da kansa ko kuma ƴan korensa daga ci gaba da yaɗa wata magana wadda wata babbar kotun Shari’ar Muslunci da ke Kano ta rufe.

Mai Shari’a Usman Na Abba ya ayyana cewar ko dai wanda aka yi kara ko yan korensa ko kuma wasu wakilansa, da a dai na yaɗa waccan magana har zuwa lokacin da kotun za ta saurari kowanne ɓangare.

Kotun ta ayyana cewar ta yi hani ga duk wata kafa ta yada labarai ko dai Rediyo ko Talabijin, ko shafukan sada zumunta da kafar Intanet da duk wata kafa wadda take iya sadar da labarai, daga yaɗa labaran da suka shafi Auwalu Ɗanladi Sankara da Taslim Baba Nabegu.

A ranar Talata ne dai gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar Namadi ya bayyana mayar da Auwalu Ɗanladi Sankara muƙamin sa na Kwamishinan ayyuka na musamman a jihar, bayan da kotu ta wanke shi daga zargin da hukumar Hisbah ta Kano, ta yi masa kan zargin baɗala da wata matar aure.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa kotun ta kuma sanya ranar 28 ga wannan watan na Nuwamba dan sauraron kowane ɓangare akan shari’ar.

Continue Reading

Trending