Manyan Labarai
Takutaha: Mun baza jami’an mu 600 domin samar da tsaro a Kano – Rundunar Anti Snaching Phone
Rundunar da ke yaƙi da ƙwacen Waya da faɗan Daba da kuma magance shaye-shaye ta Anti Snaching Phone, da ke jihar Kano, ta ce ta baza jami’an ta kusan 600, domin samar da tsaro ga masu fita bikin Takutaha a sassan jihar.
Kwamandan rundunar, kuma mashawarci na musamman ga gwamnan Kano akan harkokin tsaro Inuwa Salisu Sharaɗa, ne ya shaidawa Dala FM Kano, hakan a ranar Lahadi.
Inuwa Sharaɗa, ya kuma ce jami’an su na farin kaya da ma masu sanye da Kaki za su shiga lungu da saƙo a jihar Kano, domin ganin an gudanar da bikin Takutahar cikin kwanciyar hankali.
A cewar sa “Mun samu rahoto tare da sunayen wasu daga cikin ɓata gari da suke shirin aiwatar da mummunar ɗabi’ar da bata dace ba wajen tayar da hankalin al’umma, kuma zamu yi duk mai yiyuwa wajen ganin mun daƙile aniyar su ba tare da sun samu nasara ba, “in ji Inuwa”.
Ya ƙara da cewa duk wani wuri da aka san akwai ɓata gari a sassan jihar Kano, za su yi duk mai yiyuwa wajen ganin an ɗauki matakin da ya dace domin ƙara wanzuwar zaman lafiya a faɗin jihar Kano.
“Tuni gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bamu umarni domin mu daƙile duk wani abu da ka iya tayar da hankalin al’umma, musamman wajen daƙile, faɗan Daba, ƙwace waya, da sauran Laifuka, kuma a shirye muke domin magance matsalolin, “in ji shi”
Inuwa Sharaɗa ya ce duk wanda ya ga faruwar wani abu da ka iya haifar da matsalar tsaro zai iya sanar da su ta wannan lambar 08137261928, domin kai ɗaukin gaggawa.
A ranar Lahadin nan ne dai ake bikin Takutaha, wanda ɗumbin al’umma a sassan jihar Kano suke zagayen wurare daban-daban tare da ziyarce-ziyarce, har ma da zuwa kan Dutsen Dala, wuri mai ɗumbin Tarihi, a wani ɓangare na murnar zagayowar ranar sunan Ma’aiki Sallallahu alaihi Wasallama.
Manyan Labarai
Wani Matashi ya rasu bayan da aka zargi ya rataye kan sa a Kano
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce waní matashi rnai suna Umaro Garba ɗan unguwar Jar-Kuka mai shekaru 32 a Duniya, an yi zargin ya rataye kan sa da wani tsumma a sama al’amarin da ya yi sanadiyyar rasuwar sa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar wa Dala FM faruwar al’amarin a ranar Talata 10 ga watan Satumban 2024.a
Ya ce sun samu rahoto ne daga wani mutum daga unguwar Jar-Kuka, da ya ce sun ga ƙanen sa rataye a sama da Tsumma a ranar 8 ga watan Satumban 2024, lamarin da Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano CP Salman Dogo Garba, ya bai baturen ƴan sandan na Mariri umarni domin kai ɗaukin gaggawa, inda suka garzaya unguwar da al’amarin ya faru tare da sakko da shi daga saman da ake zargin ya rataye kan nasa.
A cewar sa, “Bayan da jami’an namu suka sakko da matashin suka kai shi babban Asibitin Sir. Muharnnadu Sunusi lamarin da Likata ya tabbatar da rasuwar sa, “in ji Kiyawa”.
Abdullahi Haruna ya ƙara da cewa tuni suka miƙa gawar marigayin ga ƴan uwansa kuma suka yi jana’izar sa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Majiyar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, SP Kiyawa ya kuma ce yanzu haka sun dukufa wajen faɗaɗa bincike akan dalilan da suka sanya matashin ya rataye kan nasa har ya rasu.
Kiyawa ya kuma shawarci al’umma, da idan suka lura da wani baƙon al’amari akan ɗan uwan su musamman ma na keɓancewa a wuri guda, ko alamun suna cikin damuwa, da su rinƙa jan su a jiki domin gujewa ta’addar kashe kai daga wasu suke yi, saboda wani dalili nasu.
Manyan Labarai
Mun bai wa DSS, wa’adin awa ɗaya su saki shugaban mu ko aga matakin da zamu ɗauka – NLC
Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC, ta bai wa hukumar tsaron farin kaya ta DSS wa’adin awa guda da su saki shugaban su na ƙasa Joe Ajearo, ko kuma aga matakin da zai biyo baya daga gareta.
Sakataren tsare-tsaren ƙungiyar ta NLC, a matakin ƙasa Kwamared Nasir Kabir, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da aka aikowa Dala FM a yammacin Litinin ɗin nan.
Ya kuma ce a lokacin da jami’an DSS, suka kama shugaban nasu a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, a dai-dai lokacin da zai tafi ƙasar Ingila, babu wata takardar umarnin kamu da suke tare da ita, kuma ƙungiyar ba za ta zuba ido ana zaluntar ƴan ƙasa su zuba idanu su ƙyale ba.
Kwamared Nasir Kabir ya kuma ƙara da cewa yanzu haka sun shiga wata tattaunawar gaggawa, domin samar da matsaya kan kamun da aka yiwa shugaban nasu.
Ƙungiyar ta kuma umartarci mambobin su da su kasance a cikin shirin ko ta kwana kan mataki da za su ɗauka matuƙar ba’a saki shugaban nasu ba, inda ya bukaci kada ƴan Najeriya suji haushin su kan matakin da za aga sun ɗauka bisa zalunci da aka yiwa ƴan ƙasa.
“Yanzu haka mun sanarwa dukkanin mambobin mu na jahohi 36 da Abuja, da su kasace cikin shirin ko ta kwana, da kuma duk manyan ƙungiyogin mu da suka shafi wutar lantarki, da na man Fetur, da makarantu da sauransu, “in ji shi”
Da safiyar Litinin ɗin nan ne dai jami’an tsaron farin kaya na DSS suka kama shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC, Joe Ajearo, a lokacin da yake shirin barin ƙasar domin tafiya ƙasar Ingila, don halartar taron da aka gayyaceshi na inganta rayuwar ma’aikata da sauran abubuwan more rayuwar su.
Manyan Labarai
Gwamnatin Kano ta ɗage komawar ɗalibai makarantu Firamare da na Sakandire
Gwamnatin jihar Kano ta ɗage komawa makarantun Firamare da na Sakandire daga ranar Lahadi da Litinin, har zuwa wani lokaci da za a saka a nan gaba.
Kwamishinan Ilmi na jihar Kano Umar Haruna Doguwa, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da aka aikowa Dala FM Kano, a cikin daren yau Asabar 07 ga watan Satumban 2024.
Doguwa ya kuma ce gwamnatin ta yi niyyar buɗe makarantun kwana ne daga gobe Lahadi, yayin da na jeka ka dawo kuma ana kuɗiri aniyar buɗewa daga ranar Litinin, amma sakamakon wani abu na gaggawa da ya taso ya sanya aka ɗage komawa makarantun zuwa wani lokaci da za’a saka a nan gaba.
Kwamishinan Ilmin ya kuma bai wa iyayen yara haƙuri bisa jinkirin komawa makarantar da aka samu, wanda ya ce an yi hakan ne domin cikar daraja da mutumtakar ƴaƴan su, da kuma ƙara shiri akai.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
You must be logged in to post a comment Login