Labarai
Maukibi: Mun ba za jami’an mu 1,000 domin samar da tsaro a Kano – Rundunar Anti Snaching Phone

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen waya da kuma magance harkokin Shaye-shaye ta Anty Snaching Phone da ke jihar Kano, ta ce ta shirya samar da tsaro a yayin taron Maukibin da za a gudanar a gobe Asabar.
Kwamandan rundunar Inuwa Salisu Sharaɗa ne ya bayyana hakan yayin zanatawar sa da tashar Dala FM Kano, a ranar Juma’a.
Inuwa Sharaɗa ya kuma ce sun samu rahoton sirri kan wasu bata gari da ke shirin yin abinda bai dace ba, kuma sun shirya tsaf domin daƙile dukkan wani yunƙurin ɓata garin da ke neman tada hankalin al’umma a sassan jihar.
“Tuni gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bamu umarnin daƙile mummunar aniyar ɓata gari, kuma mun baza jami’an mu aƙalla 800 zuwa 1000, don su shiga lungu da saƙo na jihar Kano domin ganin an gudanar da Maukibin lafiya, “in ji Inuwa Sharaɗa”.
Rundunar ta kuma sha alwashin kakkaɓe dukkan ɓata garin da ke damun al’umma ta hanyar faɗan Daba da sauran miyagun ayyuka a sassan jihar Kano, tare ƙoƙari wajen ganin gwamnatin jihar ta samar wa Matasa ayyukan yi domin su dogara da kan su.

Baba Suda
NNPP:- Kwankwaso ya sulhunta rikicin jamiyyar

Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da jagoran kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wani zama da Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado, Tofa da Dawakin Tofa, Wato Honorable Abdulkadir Jobe, da kuma Daraktan yada labaran Gwamnan Kano Honorable Sunusi Bature Dawakin Tofa.
Ganawar wadda ta gudana a yammacin wannan Alhamis ta kawo karshen Jan Zaren dake faruwa tsakanin Dan majalisar da kuma Sunusi Bature.
A baya bayan nan dai an kai ruwa rana tsakanin su, Inda kowa ne bangare ke mayar da martani.
Abdulkadir Jobe da kuma Sunusi Bature dukkanin su mabiya jamiyyar NNPP ne tsagin kwankwasiyya.

Labarai
Real Madrid ta kaddamar da Alexander

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta ƙaddamar da ɗan wasa Trent Alexander Arnold a yau a matsayin ɗan wasan ta
Inda shugaban ƙungiyar Flerontino Perez yace yau suna matuƙar Farin ciki kasancewar sun mallaki babban ɗan wasan baya a duniya.
Shima ɗan Wasa Arnold ya bayyana cewa yana cikin farin ciki kuma mafarkin sa ya cika na zama ɗan Wasan Madrid a yau.

Daurin Boye
Zan shiga kawancen ‘yan jamiyyar hamayya – tsohon Minista

Tsohon ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce a shirye yake don shiga ƙawancen ƴan jamiyyar hamayya domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027
A wata hira da BBC, tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce suna ƙoƙarin samar da haɗakar siyasar da za ta samar da sauyi a ƙasar.
Amaechi wanda ɗan jam’iyyar APC ne ya nuna damuwa kan abin da ya ƙira halin ƙuncin rayuwa da ƙasar ke ciki.
Amaechi ya ce bai cire tsammanin yin takarar shugaban ƙasa ba, illa lokaci ne kawai zai tantance.

-
Nishadi6 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su