Manyan Labarai
Har yanzu jam’iyyu 6 ne suka cika ƙa’idar zaɓen ƙananan hukumomin da za a gudanar kuma babu APC a ciki – KANSEIC

Hukumar zaɓe ta jihar Kano (KANSIEC), ta bayyana sunayen jam’iyyu 6 a matsayin waɗanda suka cika ƙa’idar shiga zaben ƙananan hukumomin da za a gudanar ranar Asabar a Kano.
Shugaban hukumar Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan babbar kotun jaha ta tabbatar da halaccin hukumar zaben.
Farfesa Malumfashi ya bayyana cewar jam’iyyun da suka cika ƙa’idar sun haɗar da Jam’iyyar AA, AAC, Accord, ADC, da APM da kuma jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa, shugaban hukumar zaben ya bukaci hukumomin tsaro da su fito su kare rayuka da dukiyoyin al’umma a lokacin gudanar da zaben, kamar yadda babbar kotun jaha ta umarce su a hukuncin da ta yi da ranar Juma’a 25 ga watan Oktoban 2024.
A ranar Alhamis dai an jiyo yadda kwamoshina mai kula da harkokin yaɗa labarai da al’amuran Shari’a na hukumar zaɓe ta jihar Kano Kanseic, Lawan Badamasi, ya ce za su yi amfani da jami’an tsaron cikin gida domin samar da tsaro yayin zaɓen.
Ya ci gaba da cewa daga cikin jami’an tsaron cikin gidan akwai irin su ƴan Karota, da na Hisbah, da kuma Ƴan Bijilante, domin samar da tsaro idan ƴan sanda suka ƙauracewa shiga aikin zaɓen kamar yadda suka samu umarnin hakan daga wata babbar kotun tarayya da ke jihar Kano.

Baba Suda
Gwamnatin Kano ta musanta labarin da ke cewa za ta saka kafar Wando daya da Sojojin Baka

Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo na cewa za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.
Kwamishinan yada labaran jihar Kwamred Ibrahim Waiya shi ne ya bayyana hakan lokacin wani taron karawa juna sani da hukumar kula da kafafen yada labarai NBC ta shirya a yau Alhamis.
Yace gwamnatin Kano za ta hada kai da Yan siyasa masu magana a Rediyo da aka fi Sani da Sojojin Baka, domin tsaftace harkokin siyasar Kano.
Haka kuma kwamishinan ya musanta labarin da ke cewa Gwamnatin Kano za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.
Kwamishina Waiya ya kuma ce za su hada kai da kafafen yada labarai domin Kara kawo tsafta a harkokin siyasar Kano.

Manyan Labarai
Da Ɗumi-Ɗumi! Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar Rivers da mataimakin sa da ƴan majalisar jihar na watanni 6.

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara, da mataimakiyar sa Mrs. Ngozi Odu, har na tsawon watanni 6.
Shugaba Tinubu ya bayyana daukar matakin ne a cikin wani taƙaitaccen jawabin sa da ya gabatar a cikin daren Talatar nan, ya ce ya yi amfani da damar da kundin tsarin mulki ya ba shi wajen sanya wannan doka wacce ta kwace mulkin jihar daga hannun gwamnan jihar Siminalayi Fubara da mataimakin sa har sai lamura sun dawo dai-dai a jihar.
Kazalika, shugaba Tinubu ya kuma bayyana dakatar da dukkanin ƴan majalisar dokokin jihar suma na tsawon watanni shidan, tare da sanya dokar ta ɓaci a jihar.
Wannan dai na zuwa ne biyo bayan rikicin siyasar da ya daɗe da kunno kai a tsakanin gwamna Fubara da ministan birnin tarayya Abuja Nyesome Wike, al’amarin da ya janyo takun saƙa tsakanin sa da ƴan majalisar dokokin jihar.

Manyan Labarai
Isra’ila ta kashe sama da mutane 200 bayan karya yarjejeniyar tsagaita Wuta a Gaza

Isra’ila ta keta yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, tare da ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Falasdinawa.
Jaridar TRT Hausa ta ruwaito cewa, aƙalla Isra’ila ta kashe fiye da mutum 200 tare da jikkata ɗaruruwa a yayin da ake ci gaba da kai gawawwaki asibiti, kamar yadda majiyoyin wani asibiti a yankin Gaza suka bayyana.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su