Manta Sabo
Kotu ta dakatar da rantsar da Ali Musa Wardwoker ko Ghali Basaf a matsayin shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso
Babbar Kotun jaha mai lamba huɗu da ke zamanta a sakateriyar Audu Bako a Kano, ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Usman Na’abba, ta bayyana matsayarta akan hukuncin da ta yanke dangane da shari’ar da ake yi a tsakanin Ali Musa Hardworker da Jam’iyyar NNPP a Kano.
Kotun ta ayyana cewar kowanne ɓangare ya dakata da batun rantsuwar kama aiki har zuwa lọkacin da kotun ɗaukaka ƙara za ta ayyana matsayarta.
Idan dai ba’a manta ba Dala FM ta ruwaito yadda a baya kotun ta ayyana Ali Musa Hardworker a matsayin halastaccen ɗan takarar lamarin da ya sanya jam’iyyar NNPP da Ghali Basaf suka ɗaukaka ƙara akai.
Manta Sabo
An zargi wani Matashi da satar wayar direban mai Shari’a ana tsaka da Shari’a a Kano
Babbar Kotun jaha mai zamanta a miller road karkashin jagorancin mai Shari’a Maryam Ahmad Sabo, ta yi umarnin yan sanda su fadada bincike akan wani matashi mai suna Haruna Buhari wanda ake zargi da laifin kutse da sata.
Tunda fari dai an zargi Haruna da kutsawa cikin ofishin mai Shari’ar tare da ɗauke wayar salula ta direban mai shari’ar wadda aka jona caji a ofishin ta.
Tuni dai yan sandan kotun suka fice da shi daga Harabar kotun dan mika shi shelkwatarsu da ke Bompai, domin gudanar da binciken.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya zanta da wani shaidar gani da ido wanda yace daman an dame su da satar takalma a masallacin harabar kotun idan sun je Sallah, a Masallaci.
Mai korafin dai ya kuma bayyana cewar an fi satar takalman alkalai a masallacin.
Manta Sabo
Kotu ta umarci CBN da ya sakarwa ƙananan hukumomin Kano kuɗaɗen su.
Babbar kotun jaha karkashin jagorancin mai Shari’a Ibrahim Musa Ƙaraye, ta dakatar da babban bankin Najeriya CBN, da ofishin babban akanta na kasar nan daga yin jinkiri wajen biyan ƙananan hukumomin Kano kudadensu na arzikin kasa da gwamnatin tarayya ke bayarwa.
Cikin wata ƙara wadda shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomin Kano da mutane shida amadadin ƙungiyar suka shigar.
Waɗanda ake karar dai a gaban kotun sun hadar da babban akanta na kasar nan da kuma babban bankin Najeriya CBN, sai kuma wasu bankuna guda 7 da dukkanin ƙananan hukumomin Kano.
Masu ƙarar ta bakin lauyan su Barrister Bashir Yusuf Tudun Wuzurci, sun bayyana wa kotun cewar idan aka hana ƙananan hukumomin kudadensu hakan zai haifar da koma baya a jahar Kano kuma yin hakan ya saɓawa doka.
Kotun ta amince da dukkan roke-roken masu karar inda aka kùma ayyana cewar kodai babban bankin ƙasa CBN, ko babban akanta na kasar da ragowar waɗanda aka yi karar ko yan korensu cewar kada su yi jinkiri wajen biyan ƙananan hukumomin Kano kudadensu na arzikin kasa da ake rabawa kowace karamar hukuma.
Kotun ta kuma yi umarni da a aikewa waɗanda ake ƙara kwafin umarnin da ta bayar.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewar kotun ta sanya ranar 21 ga wannan watan dan sauraren kowanne ɓangaren.
Manta Sabo
Kotun ta umarci jami’an tsaro da su ƙauracewa zaben ƙananan hukumomin da za’a gudanar a Kano
Babbar kotun tarayya mai zamanta a Kano karkashin jagorancin mai Shari’a Simon Amobeda, ta rushe shugabancin hukumar zabe ta jahar Kano Kanseic.
Kotun dai ta ɗauki wannan mataki ne bisa dogaro da hujjojin da áká gabatar mata na rashin cancantarsu, kasancewarsu ƴan Siyasa kuma suna ɗauke da katin Jam’iyyar NNPP.
Cikin wata kara wadda Aminu Aliyu Tiga da Jam’iyyar APC suka shigar suna rokon kotun da ta rushe su.
Kotun ta kuma umarci jami’án tsaro da su ƙauracewa zaben ƙananan hukumomin da za’a gudanar tare da umartar hukumar zabe ta kasa INEC, da kada ta bayar da kayan zaben.
A ranar Asabar ne dai 26 ga watan Oktoban 2024, za’a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar Kano.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
You must be logged in to post a comment Login