Labarai
Ƙarancin kayan aiki na bamu matsala wajen kakkaɓe masu faɗan Daba da ƙwacen Waya a Kano – Anty Snaching Phone

Rundunar tsaron nan mai yaki da fadan Daba da ƙwacen Waya da kawar da Shaye-shaye ta Anty Snaching da ke jihar Kano, ta sha alwashin ci gaba da kakkabe bata garin da ke addabar al’umma da fadan Daba a sassan jihar, domin ƙara wanzuwar zaman lafiya a fadin jihar.
Kwamandan rundunar Inuwa Salisu Sharada, shi ne ya bayyana hakan a zantawarsa da gidan redivon Dala FM, a ranar Litinin.
Ya ce za su ci gaba da kokari wajen shiga lungu da sako wajen kawar da dukkanin masu kokarin tayar da hankalin al’umma, duk kuwa da ƙalubalen da suke fuskanta.
“Daga cikin ƙalubalen da muke fuskanta akwai ƙarancin motar fita aiki domin mota ɗaya muke da ita, idan jami’an mu za su fita aiki da mutane da yawa sai dai su hau Baburan Adai-dai Sahu, duk hatsarin wuri; akwai mota a gidan gwamnatin Kano muna fatan gwamna zai bamu ita a ciki gaba da aiki, “in ji Inuwa”.
Kazalika Sharada ya kuma ƙara da cewa akwai buƙatar al’umma su ƙara himma wajen ba su hadin kan da ya dace domin ganin sun kara samun dama wajen magance matsalar tsaro musamman ma ta fadace-fadacen Daba, da ta addabi al’umma a sassan jihar Kano.
A cewar sa, “Ƙarancin motocin fita aikin na ba mu matsala domin a wasu lokutan daga wuri mai nisa ake kiran mu don kai ɗauki akan matsalar tsaro, amma rashin wadatattun motocin mukan fuskanci ƙalubale, “in ji shi”.
Wannan dai na zuwa ne yayin da al’umma ke a gaba da neman dauki wajen magance matsalar tsaron da ke damun su a sassan jihar, musamman ma a wasu unguwanni da ke ƙwaryar bimin Kano.

Labarai
Zan haɗa kai da hukumomin tsaro da Baturan ƴan Sanda don magance matsalolin tsaro a Kano – CP Bakori

Sabon kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Dr. Ibrahim Adamu Bakori, ya ce zai haɗa kai da dukkannin hukumomin tsaro da baturan ƴan sandan da ke kan iyakokin jihar, don ganin an sami ingantacciyar tsaro a faɗin jihar.
Dr. Ibrahim Bakori ya bayyana hakan ne a zantawar sa da manema labarai ciki har da wakilin tashar Dala FM Kano, a ranar Laraba 19 ga watan Maris ɗin 2025.
Ya kuma ce zai amfani da fasahar sadarwa wajan gudanar da aikin sa, tare kuma da wayar da akan al’umna kasancenwar aikin tsaro na kowa ne.
A makon da ya gabata ne dai rundunar ƴan Sanda ta ƙasa ta turo CP Ibrahim Adamu Bakori, jihar Kano, wanda ya maye gurbin Salman Dogo Garba, bisa samun ƙarin girma da ya yi zuwa matakin AIG.

Labarai
Tsohon shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya ƙaryata ficewar sa daga APC zuwa SDP

Tsohon shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya musanta wata jita-jita da ake yaɗawa kan cewar ya fice daga cikin jam’iyyar APC mai mulki a ƙasa, zuwa SDP, al’amarin da ya ce bashi da tushe ballantana makama.
A cikin wata sanarwar da mashawarci na musamman ga tsohon Sanatan a kafafen yaɗa labarai Ezrel Tabiowo, ya fitar a jiya Lahadi, ta ce jita-jitar da ake yaɗawa na cewar Ahmad Lawan ya fice daga jam’iyyar ta APC, ƙarya ce tsagwaronta.
Jaridar Daily trust ta ruwaito cewar, sanarwar ta kuma ce, har yanzu Ahmad Lawan ɗan Jam’iyyar APC ne, kuma yana biyayya ga jam’iyyar, wadda yake alfahari da ita.

Labarai
Babu adalci a ƙarin kuɗin Data da na kiran Waya da aka yi a Najeriya – Human Rights

Ƙungiyar wayar da kan jama’a da kare haƙƙin ɗan adam da kuma tallafawa mabuƙata a Najeriya, ta ce Abin takaici ne yadda gwamnatin tarayya ta amince da ƙarin kuɗin Data da na kira, al’amarin da ta kira da rashin adalci ga ƴan Ƙasa.
Daraktan ƙungiyar ta Awareness for Human Rights and Charity Foundation a Najeriya Kwamared Auwal Usman Awareness, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya aikowa tashar Dala FM Kano, a ranar Lahadi.
“Ƙarin kuɗin Data da na kiran waya da kamfanonin sadarwa suka yi wa al’umma a Najeriya, abin damuwa ne, saboda ƙarin ya zo ne a dai-dai lokacin da jama’a ke fama da matsin tattalin arziƙi, da hauhawar Farashi, da wahalhalun Rayuwa, “in ji Auwal Usman”.
Ya kuma ce duba da halin mummunan tasirin wannan karin na kuɗin Data da na kiran Waya, kamata ya yi gwamnatin tarayya ta umarci kamfanonin sadarwar su sauƙaƙa wa al’umma saɓanin yi musu ƙarin.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ɗin, ta Awareness for Human rights and Charity Foundation, ta kuma buƙaci a soke ƙarin kuɗin kira da na datar da aka yi, tare da kafa dokoki da za su hana ƙara farashin ba tare da tuntuɓar al’umma ba.
Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, tuni dai ƴan Najeriya suka fara nuna takaicin su kan ƙarin kuɗin kira da na datar da kamfanonin sadarwa suka yi musu, lamarin da suke ci gaba da kira ga mahukunta da a rage kudaɗen bisa yadda ƙarin ya yi yawa.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su