Labarai
Rashin bayar da shawarwari na kawo tsaiko a karatun Ɗaliban Najeriya – Farfesa Abdurrasheed Garba
Shugaban jam’i’ar Khalifa Isyaka Rabi’u ta Chairun da ke jihar Kano Farfesa Abdrulrahsheed Garba, ya ce rashin shigar da tsarin jagoranci da bada shawarwari a mafi yawa daga cikin makarantu a Nijeriya, na taimaka wa wajen sanya matasa su gaza hawa kan kyakkyawar turbar da ta dace da su a rayuwar karatun su da ma sauran al’amura daban-daban.
Farfesa Abdrulrahsheed Garba ya bayyana hakan ne a ganawar sa da gidan rediyon Dala FM, yayin wata ziyara ya da ya kawo gidan a yammacin Juma’a 27 ga watan Disamban 2024.
“Tun kusan shekaru hamsin aka sanya jagorancin da bada shawarwarin wato Guiding and Cancelling, a cikin tsarin ilmin ƙasa a Najeriya, sai dai har kawo yanzu da yawa daga cikin gwamnatocin jahohi da ma gwamnatin tarayya sun gaza tabbatar da shi, “in ji shi”.
Farfesa Abdrulrahsheed Garba, ya kuma ƙara da cewa akwai buƙatar iyaye da makarantu su ƙara dagewa akan ƴaƴan, ita kuma gwamnati ta kara samar da ingantattun makarantu, domin ganin rayuwar ɗalibai ta ƙara hawa kan turba mai kyau.
Labarai
Ƙarancin kayan aiki na bamu matsala wajen kakkaɓe masu faɗan Daba da ƙwacen Waya a Kano – Anty Snaching Phone
Rundunar tsaron nan mai yaki da fadan Daba da ƙwacen Waya da kawar da Shaye-shaye ta Anty Snaching da ke jihar Kano, ta sha alwashin ci gaba da kakkabe bata garin da ke addabar al’umma da fadan Daba a sassan jihar, domin ƙara wanzuwar zaman lafiya a fadin jihar.
Kwamandan rundunar Inuwa Salisu Sharada, shi ne ya bayyana hakan a zantawarsa da gidan redivon Dala FM, a ranar Litinin.
Ya ce za su ci gaba da kokari wajen shiga lungu da sako wajen kawar da dukkanin masu kokarin tayar da hankalin al’umma, duk kuwa da ƙalubalen da suke fuskanta.
“Daga cikin ƙalubalen da muke fuskanta akwai ƙarancin motar fita aiki domin mota ɗaya muke da ita, idan jami’an mu za su fita aiki da mutane da yawa sai dai su hau Baburan Adai-dai Sahu, duk hatsarin wuri; akwai mota a gidan gwamnatin Kano muna fatan gwamna zai bamu ita a ciki gaba da aiki, “in ji Inuwa”.
Kazalika Sharada ya kuma ƙara da cewa akwai buƙatar al’umma su ƙara himma wajen ba su hadin kan da ya dace domin ganin sun kara samun dama wajen magance matsalar tsaro musamman ma ta fadace-fadacen Daba, da ta addabi al’umma a sassan jihar Kano.
A cewar sa, “Ƙarancin motocin fita aikin na ba mu matsala domin a wasu lokutan daga wuri mai nisa ake kiran mu don kai ɗauki akan matsalar tsaro, amma rashin wadatattun motocin mukan fuskanci ƙalubale, “in ji shi”.
Wannan dai na zuwa ne yayin da al’umma ke a gaba da neman dauki wajen magance matsalar tsaron da ke damun su a sassan jihar, musamman ma a wasu unguwanni da ke ƙwaryar bimin Kano.
Labarai
Dalilan da suka sa gwamnan Kano ya bai wa Sani Danja muƙami.
Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗa fitaccen ɗan fina-finan Hausar nan na Kannywood, Sani Musa Danja, a matsayin mai ba shi shawara na musamman a kan harkokin matasa da wasanni.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da babban daraktan yaɗa labaran gwaman jihar Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Lahadi 15 ga watan Disamban 2024.
Sunusi, ya kuma ce gwamnan ya amince da naɗin Sani Danja tare da wasu mutane da shugabannin hukumomin da aka sauya wa ma’aikatu da masu bai wa gwamna shawara daban-daban.
Idan dai ba’a manta ba a mako mai ƙarewa ne dai gwamnan jihar Kano ya yi wa majalisar zartarwarsa garambawul, inda ya sauke wasu ƙusoshin gwamnatinsa, daga ciki kuwa har da sauke sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Baffa Bichi, da shugaban ma’aikatar fadar gwamnatinsa Shehu Wada Sagagi.
Har ila yau, a makon dai gwamnan ya sauke kwamishinan yaɗa labaransa Baba Halilu Ɗan Tiye, da wasu Kwamishinoninsa, a ranar Alhamis ɗin da ta gabata.
Kafar yaɗa labarai ta Dala FM Kano, ta rawaito cewar, Sani Danja, dai na daga cikin ƴan takarar shugabancin ƙaramar hukumar Nassarawa, a zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a baya-bayan nan.
Labarai
Wasu lauyoyi sun musanta labarin da wata Jaridar Internet ta wallafa akan wata Shari’a.
Wasu lauyoyi ƙarƙashin jagorancin Barrister Yusuf Sulaiman, sun yi martani akan wani labari da wata kafar yaɗa labarai ta zamani take yadawa, da ta ke cewa wai wani mutum ya sa an aike da yaronsa gidan gyaran hali da tarbiyya.
Labarin dai ya bayyana cewar wai dan mutumin ya nemi yaron nasa domin ya yi aikin alfasha dashi, shi kuma yaƙi amincewa da hakan, lamarin da lauyoyin suka ce wannan labari ba shi da tushe ballantana makama.
Barrister Yusuf Sulaiman, ya bayyana cewar labarin da waccan kafar yada labarai ta Internet take yaɗawa ba gaskiya ba ne ba.
Lauyan ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labaran da lauyoyin suka gudanar, ya kuma ce akwai Shari’a a gaban babbar Kotun Shari’ar Muslunci ta Kumbotso a jihar Kano, wadda Ƴan Sanda suka gurfanar da wani matashi mai suna Khalifa Garba wanda ake zargi da laifin bata sunan wani mutum mai suna Alhaji Sa’idu Iliyasu.
A zaman kotun na baya dai matashin ya amsa laifinsa na ɓata suna, lamarin da kotun ta sanya ranar Litinin 16 ga wannan watan domin ta hukunta shi.
Barrister Sulaiman, ya ƙara da cewa wannan kafar yaɗa labarai da ta sanya wannan labarin a kafafen sada zumunta na zamani, labarin da ta yada jita-jita ce kawai, kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su