Connect with us

Manyan Labarai

Matashin Ɗan Jarida ya musuluntar da wani Fasto a Kano.

Published

on

Matashin ɗan jaridar nan a jihar Kano, da ya ke aiki a gidan Radio Dala FM Kano, Mu’azu Musa Ibrahim, ya musuluntar da wani mutun wanda a baya yake amfani da suna (AEROUN) wanda a bayan yake a matsayin Fasto.

Tunda fari matashin ɗan jaridar Mu’azu Musa Ibrahim, sun haɗu da tsohon Faston ne sakamakon shirin da yake gabatarwa mai suna Duniya Labari, inda Faston ya kasance ɗaya daga cikin masu sauraron shirin daga jihar Kaduna, bayan kwashe tsawon lokaci yana bibiyar shirin har ta kai alaƙa ta ƙullu a tsakaninsu.

Tsohon Faston mai shekaru 64, wanda a yanzu ya koma mai suna Harun, ya musulunta ne a ranar 25 ga watan Disamban 2024, inda ɗan jaridar ya ba shi kalmar Shahada, kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

Shirin Duniya Labari, shiri ne dai da ya shafe shekaru biyar ana gabatar da shi a gidan rediyon Dala FM 88.5 da ke jihar Kano, a arewacin Najeriya, wanda ya karɓu a tsakanin al’umma har ma suke rububin sauraron sa.

A cikin shirin dai da Mu’azu Musa Ibrahim, ke jagoranta, mutane sukan bayar da labarin abinda ya faru da su ne musamman ma a cikin rayuwar su tun daga farko zuwa lokacin da suka bayar da labarin, ciki har da na Nasarori da kuma ƙalubale, domin ɗaukar darasi a ciki.

Baba Suda

Gwamnatin Kano ta musanta labarin da ke cewa za ta saka kafar Wando daya da Sojojin Baka

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo na cewa za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishinan yada labaran jihar Kwamred Ibrahim Waiya shi ne ya bayyana hakan lokacin wani taron karawa juna sani da hukumar kula da kafafen yada labarai NBC ta shirya a yau Alhamis.

 

Yace gwamnatin Kano za ta hada kai da Yan siyasa masu magana a Rediyo da aka fi Sani da Sojojin Baka, domin tsaftace harkokin siyasar Kano.

 

Haka kuma kwamishinan ya musanta labarin da ke cewa Gwamnatin Kano za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishina Waiya ya kuma ce za su hada kai da kafafen yada labarai domin Kara kawo tsafta a harkokin siyasar Kano.

Continue Reading

Manyan Labarai

Da Ɗumi-Ɗumi! Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar Rivers da mataimakin sa da ƴan majalisar jihar na watanni 6.

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara, da mataimakiyar sa Mrs. Ngozi Odu, har na tsawon watanni 6.

Shugaba Tinubu ya bayyana daukar matakin ne a cikin wani taƙaitaccen jawabin sa da ya gabatar a cikin daren Talatar nan, ya ce ya yi amfani da damar da kundin tsarin mulki ya ba shi wajen sanya wannan doka wacce ta kwace mulkin jihar daga hannun gwamnan jihar Siminalayi Fubara da mataimakin sa har sai lamura sun dawo dai-dai a jihar.

Kazalika, shugaba Tinubu ya kuma bayyana dakatar da dukkanin ƴan majalisar dokokin jihar suma na tsawon watanni shidan, tare da sanya dokar ta ɓaci a jihar.

Wannan dai na zuwa ne biyo bayan rikicin siyasar da ya daɗe da kunno kai a tsakanin gwamna Fubara da ministan birnin tarayya Abuja Nyesome Wike, al’amarin da ya janyo takun saƙa tsakanin sa da ƴan majalisar dokokin jihar.

Continue Reading

Manyan Labarai

Isra’ila ta kashe sama da mutane 200 bayan karya yarjejeniyar tsagaita Wuta a Gaza

Published

on

Isra’ila ta keta yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, tare da ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Falasdinawa.

Jaridar TRT Hausa ta ruwaito cewa, aƙalla Isra’ila ta kashe fiye da mutum 200 tare da jikkata ɗaruruwa a yayin da ake ci gaba da kai gawawwaki asibiti, kamar yadda majiyoyin wani asibiti a yankin Gaza suka bayyana.

Continue Reading

Trending