Connect with us

Manyan Labarai

Ku gujewa ɗaukar doka a hannu don gudun matsala – Human Right Forum

Published

on

Gamayyar ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam a nan Kano sun yi kira ga hukumomin tsaro da su yi aiki kafaɗa da kafaɗa domin samar da zaman lafiya a faɗin jihar.

Shugaban gamayyar ƙungiyoyin Kwamared A-A Haruna Ayagi, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau mai ɗauke da sa hannunsa, aka aikowa Dala FM Kano, a wani ɓangare na murnar shiga sabuwar shekarar 2025.

Ayagi, ya kuma buƙaci al’ummar jihar Kano da su bi doka da oda, tare da gujewa ɗaukar doka a hannu, duk abinda basu gamsu da shi ba su sanar da jami’an tsaro mafi kusa.

Sanarwar ta kuma buƙaci dukkanin mambobin su da sauran hukumomin shari’a da su yi aiki tare ba tare da nuna tsoro ba.

A-A Ayagi ya kuma yi kira ga babbar jojin jihar Kano, mai Shari’a Dije Abdu Aboki, da ta ci gaba da sanya ido wajen ganin cewa an gudanar da shari’o’i cikin gaskiya da riƙon amana a jihar Kano baki ɗaya.

Manyan Labarai

Wata Sabuwa: Lauya ya nemi kotu ta kama kwamishinan Shari’a na jihar Kano

Published

on

Wani lauya mai zaman kan sa a jihar Kano Barista Haruna Musa Muhammad, ya yi ƙorafi a gaban babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar, akan ta kama kwamishinan Shari’a na jihar Kano Barista Haruna Isah Dederi, da wasu manyan mukarraban gwamnatin jihar.

Lauyan wanda yake wakiltar mai kara Nura Bashir Ahmad, ya bayyana cewar gwamnatin jihar Kano ta rushe wa Nura gida duk da cewar ya samu hukunci a babbar kotun tarayya akan kada a rushe masa gidan.

Cikin wata ƙunshin Shari’a mai lamba FHC/KN/CS/240/2023, mai Shari’a Simon Amobida, ya ayyana cewar kotun tarayya ta gamsu da takardun mallaka da mai ƙara Bashir Ahmad ya gabatar mata, don haka ne ma ta ayyana cewar gidan mallakinsa ne.

Kotun dai tun a ranar 13 ga watan biyu na shekarar da ta gabata ta 2024, ta zartas da hukuncin akan batun.

Mai karar Bashir ta bakin lauyansa Barista Haruna Musa, sun bayyana cewar sun rubuta koke zuwa gaban kotun da ta yi hukuncin tun da dai suna zargin waɗanda ake ƙarar sun raina wannan hukunci kamar yadda ya bayyana a zantawar sa da wakilin Dala FM Kano.

Akan wannan batu ne wakilin namu ya tuntuɓi kwamishinan Shari’a na jihar Kano Barista Haruna Isah Dederi, ta wayar salula, sai dai bai samu damar ɗaa wayar ba, ya kuma aike masa da gajeren saƙon kar ta kwana nan ma bai bada amsa ba, amma yana dakon sa.

Continue Reading

Manyan Labarai

Budurwa ta mutu yayin wata Gobara da ta kama cikin gidan su a Kano

Published

on

Wata Gobara da ta tashi a wani gida ta yi sanadiyyar rasuwar wata budurwa a unguwar Ja’en Sabere da ke ƙaramar hukumar Gwale a Kano da ke arewacin Najeriya, tare da ƙonewar wasu sassan gidan.

Mamallakin gidan da lamarin ya faru mai suna Saminu Abba ne ya tabbatar wa tashar Dala FM faruwar lamarin a ranar Alhamis, 16 ga watan Janairun 2025.

Ya ce gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe ɗaya na daren jiya Laraba, lamarin da jami’an hukumar kashe Gobara ta jihar Kano da ma ƴan Bijilanten yankin da sauran al’umma suka kai ɗauki.

“Muna cikin Bacci muka ji wata ƙara da ihun mutanen unguwa, da muka tashi muka ga Gobara ce ta tashi a wasu sassan gidan mu kuma wutar ta tare hanyar da za mu fita gashi tana ci ba ƙaƙƙautawa, “in ji Saminu”.

Ya ci gaba da cewa, “Bayan jami’an hukumar kashe Gobara da ƴan Bijilanten yankin, da sauran al’umma sun kawo musu ɗauki, ne aka fasa Gini ta gidan maƙotan su inda su shida suka fita daga gidan sai dai ƴar su budurwa mai shekaru 18 mai lalurar Sikila ta rasu”.

Mallam Saminu Abba ya ƙara da cewa, kayayyakin su na sawa da wasu tarin kayayyaki da dama ne suka ƙone ƙurmus, lamarin da ya nemi ɗaukin mahukunta da su kai musu ɗauki bisa halin da suka samu kan su a ciki.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ba kan ta: An sace birkin jirgin sama guda 80 a Kano

Published

on

Kotun majistret mai lamba 70 da ke jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Faruk Ibrahim Umar, ta aike da wasu mutane gidan ajiya da gyaran hali bisa zargin su da haɗa baki da Sata.

Ƙunshin zargin da ake yi wa mutanen ya ayyana cewar, a ranar 11 ga watan 12 na shekarar da ta gabata ta 2025, wani mutum mai suna Otaru Bashir ma’aikaci a kamfanin sifirin jiragen sama na Azman, ya yi ƙorafi cewar mai gadin kamfanin nasu ya haɗa baki da wasu mutane sun sace musu birkin jirgin sama guda 80.

Ana dai zargin mutanen ne da sace waɗannan barakun wato birkin jirgin sama guda tamanin a filin jirgin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano.

Mutanen da ake zargin sun hadar da Nuhu Auwalu da Yakubu Bala da Emanuel Luka, sai kuma safiyanu Abdullahi.

Ko da aka karanta wa mutanen ƙunshin zargin da ake yi musu dukkaninsu sun musanta, a nan ne kotun ta aike da mutanen gidan gyaran hali tare da sanya ranar 11 ga watan gobe dan sauraron shaidu akan shari’ar.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewar, yayin zaman kotun an ambata cewar, binciken ƴan sanda ya bayyana cewar kimar kayan ya kama Naira miliyan dari da arba’in, sai dai yayin bincike an gano birkin jirgin guda uku a hannun wanda ake zargi na uku mai suna Yakubu Bala.

Continue Reading

Trending