Connect with us

Manyan Labarai

Ba za mu lamunci nuna halin ko in kula ba ga karatun Ɗalibai da rashin zuwan malamai makarantu – Gwamnatin Kano 

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ce ta sha alwashin daukar mataki akan shugabannin makarantar G.S.S Gano da ke karamar hukumar Dawakin Kudu, bisa samun shugabannin makarantar da nuna halin ko in kula ga makarantar, baya ga batun samun karancin zuwan malamai da kuma dalibai a makarantar.

Kwamishinan ma’aikatar ilmi na jihar Kano Gwani Ali Haruna Makoda, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar ba zata da ya kai wasu daga cikin makarantu da ke jihar nan, biyo bayan yadda aka koma makarantun sakandire da na Firamare na jeka ka dawo ranar Litinin a jihar, inda aka kuma koma na kwana a ranar Lahadi.

“Gwamnatin Kano, ba za ta lamunci yadda wasu daga cikin shugabannin makarantun suke nuna halin ko in kula a makarantun ba; za mu ɗauki matakin gaggawa, “in ji Makoɗa”.

Haka na zuwa ne bisa yadda kwamishinan ya samu makarantar sakandiren maza ta G.S.S Gano da ke ƙaramar hukumar Dawakin Kudu, da nuna halin ko in kula da makarantar, ciki har da samun kashin Dabbobi, wanda haka ke nuna cewa ana ajiye Dabbobi da suke kwana a sama da ƙasa na makarantar, lamarin da ya ce gwamnatin ba za ta amince da shi ba.

Sauran makarantun da Kwamishinan ya ziyarta sun haɗar da G.S.S Gano, da makarantar sakandiren kwana ta Maza, G.S.C.S Wudil, da kuma makarantar Mata ta G.G.S.S Ƴar-Gaya da ke jihar Kano.

Gwani Makoɗa, ya ƙara da cewa, sun raba jami’an su inda suka zagaya makarantu daban-daban domin ganewa idanun su yadda malamai da ɗaliban suka koma makaranta a ranar Litinin 06 ga watan Janairun 2025, tare da kawo musu sakamakon abubuwan da suka gani, domin ɗaukar matakan da suka kamata.

Baba Suda

Gwamnatin Kano ta musanta labarin da ke cewa za ta saka kafar Wando daya da Sojojin Baka

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo na cewa za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishinan yada labaran jihar Kwamred Ibrahim Waiya shi ne ya bayyana hakan lokacin wani taron karawa juna sani da hukumar kula da kafafen yada labarai NBC ta shirya a yau Alhamis.

 

Yace gwamnatin Kano za ta hada kai da Yan siyasa masu magana a Rediyo da aka fi Sani da Sojojin Baka, domin tsaftace harkokin siyasar Kano.

 

Haka kuma kwamishinan ya musanta labarin da ke cewa Gwamnatin Kano za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishina Waiya ya kuma ce za su hada kai da kafafen yada labarai domin Kara kawo tsafta a harkokin siyasar Kano.

Continue Reading

Manyan Labarai

Da Ɗumi-Ɗumi! Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar Rivers da mataimakin sa da ƴan majalisar jihar na watanni 6.

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara, da mataimakiyar sa Mrs. Ngozi Odu, har na tsawon watanni 6.

Shugaba Tinubu ya bayyana daukar matakin ne a cikin wani taƙaitaccen jawabin sa da ya gabatar a cikin daren Talatar nan, ya ce ya yi amfani da damar da kundin tsarin mulki ya ba shi wajen sanya wannan doka wacce ta kwace mulkin jihar daga hannun gwamnan jihar Siminalayi Fubara da mataimakin sa har sai lamura sun dawo dai-dai a jihar.

Kazalika, shugaba Tinubu ya kuma bayyana dakatar da dukkanin ƴan majalisar dokokin jihar suma na tsawon watanni shidan, tare da sanya dokar ta ɓaci a jihar.

Wannan dai na zuwa ne biyo bayan rikicin siyasar da ya daɗe da kunno kai a tsakanin gwamna Fubara da ministan birnin tarayya Abuja Nyesome Wike, al’amarin da ya janyo takun saƙa tsakanin sa da ƴan majalisar dokokin jihar.

Continue Reading

Manyan Labarai

Isra’ila ta kashe sama da mutane 200 bayan karya yarjejeniyar tsagaita Wuta a Gaza

Published

on

Isra’ila ta keta yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, tare da ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Falasdinawa.

Jaridar TRT Hausa ta ruwaito cewa, aƙalla Isra’ila ta kashe fiye da mutum 200 tare da jikkata ɗaruruwa a yayin da ake ci gaba da kai gawawwaki asibiti, kamar yadda majiyoyin wani asibiti a yankin Gaza suka bayyana.

Continue Reading

Trending