Manyan Labarai
Wata Kotu ta yanke wa wasu mutane uku hukuncin Kisa ta hanyar rataya a Kano

Babbar kotun jaha mai zamanta a sakateriyar Audu Bako da ke Kano, a arewacin Najeriya, ƙarkashin mai Shari’a Amina Adamu, ta yanke wa wasu mutane uku hukuncin kisa ta hanyar rataya, sakamakon samun su da laifin kashe wani mutum mai suna Alhaji Hamisu Alasan Yar Zabaina.
Ƙunshin tuhumar da ake yi wa mutanen ya bayyana cewar, tun a shekarar 2019 ne suka haɗa baki inda suka kashe mutumin bayan da suka yi masa sata a gona, ya kuma gane daya daga cikinsu har ya ambaci sunansa daga nan suka yi masa yankan rago.
Lauyan gwamnati Barrister Bashir Sale ya gabatar da shaidu uku a gaba kotun, inda suma waɗanda aka yanke wa hukuncin suka kare kansu.
Kotun ta karbi shaidun masu gabatar da kara yayin da aka yi watsi da shaidun kariya.
“Mai Shari’a Amina Adamu ta ayyana cewar kotun ta same su da laifi, inda ta ayyana hukuncin kisan ta hanyar rataya akan su”
Wakilin Dala FM Kano, Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewar, mutanen da aka yanke wa hukuncin sun haɗar da Abdurrahman Ado, da Rabi’u Muhammad, da kuma Hamisu Ibrahim wanda aka fi sani da Hogan.

Manyan Labarai
An yi jana’izar Shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano Ahmadu Haruna Zago

Ɗaruruwan mutane ne suka halarci sallar jana’izar shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano Alhaji Ahmadu Haruna zago, wanda aka gudanar a kofar kudu a fadar mai martaba sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu.
Babban kwamandan hukumar Hisbah na jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, shine ya jagorancin sallar jana’izar a tsakar ranar Alhamis ɗin nan.
Daga cikin manyan manyan mutane da Suka hallarci sallar jana’izar marigayin Alhaji Ahmadu Haruna zago, akwai gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da tsohon kwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwakwanso, da mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, da sauran manyan mutane ciki har da masu riki da mukaman gwamiti.
Da safiyar Alhamis ɗin nan ne dai marigayi Ahmadu Zago, mai shekaru 74 ya rasu, a Asibitin Aminu Kano, bayan fama da rashin lafiya, kafin rasuwar sa yana da mata huɗu da ƴaƴa 37, da jikoki da dama.
Mai martaba sarkin kano Khalifa Muhammadu Sunusi na yayi addu’ar fatan Allah ya jikan marigayin ya kuma baiwa iyalansa da al’ummar jihar Kano jure rashin.
Tuni dai gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya miƙa saƙon ta’aziyyar sa ga al’ummar jihar da kuma iyalan marigayi Ahmadu Haruna Zago, tare da fatan Allah ya gafarta masa.

Manyan Labarai
Majalisar dokokin Kano ta amince da kafa rundunar tsaro mallakin jihar

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dokar kafa Rundunar tsaro mallakin gwamnatin jiha, bayan ɗaukar tsawon lokaci ana dambarwa a majalisar kan saɗarar dokar da ya ce ba’a yarda wanda yake riƙe da katin shaidar kowace jam’iyyar siyasa ba ya shugabanci rundunar tsaron.
Majalisar ta amince da samar da dokar ne bayan shafe kusan fiye da tsawon awa ɗaya ana muhawara akan da yawa daga cikin tanadin da dokar samar da rundunar tsaron ya yi kafin ayi mata karatu na uku.
Da yake ƙarin bayani akan kunshin dokar, Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Husani Dala, ya ce sun yi cikakken Nazari da hangen nesa kafin yin dokar wadda zata taba kowane bangare na jihar Kano wajen daukar ma’aikatan ta musamman wadanda basu da alaka da harkar siyasa.
“Dokar da muka samar ta amincewa jami’an rundunar tsaron ta jihar Kano da za a kafa su ɗauki kowane irin makami domin gudanar da ayyukan su, wanda ya haɗa da kamawa, hana aikata laifi da fatattakar masu aikata laifuka a fadin jihar Kano, “in ji Dala”.
Ditective Auwal Bala Durumin Iya guda daga cikin masana harkokin tsaro ne a ƙasar nan, ya ce akwai buƙatar abi ƙa’idoji wajen ɗaukar jami’an da za su gudanar da aikin rundunar tsaron da zarar gwamnan Kano ya sanya hannu a kan dokar.
A dai zaman na ranar Talata 04 ga watan Fabrairun 2025, majalisar dokokin Kano ta kuma amince da yin gyara akan dokar hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar nan, da hukumar da ke kula da sufuri a kwaryar birnin kano domin samun damar nada musu mataimaka.

Manyan Labarai
Za’a fara cin tarar Naira dubu 25 akan masu tofar da Yawu ko Majina, ko zubar da Shara ba bisa ƙa’ida ba a Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta yi dokar cin tarar Naira dubu 25 ga duk wanda aka kama da tofar da Yawu, da Majina, yin Bahaya ko zubar da Shara a sha tale-tale da kuma karkashin gadojin dake Kano.
Wannan ya biyo bayan dokar da majalisar ta Samar wadda za ta gudanar da ayyukan hukumar ƙawata birnin Kano da Kula da wuraren shaƙatawa.
Da yake Karin bayani ga manema labarai, Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Hussaini Dala, ya ce ya zama wajibi gwamnati ta dauki matakan da za su tsaftace Kano domin shigar da jihar sahun biranen duniya a fannin tsafta da cigaba.
“Bayan tarar ta Naira dubu 25, akwai kuma sauran hukunce-hukunce da dokar ta tanada wadanda za’ayi amfani dasu wajen ladabtar da duk wanda aka samu da laifukan, “in ji Lawan Dala”.
Majalisar ta kuma yi karatu na biyu kan gyaran dokar hukumar kwashe Shara da tsaftar Muhalli ta Kano domin Samar da mataimakin Shugaba.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
You must be logged in to post a comment Login