Manyan Labarai
An cafke magidantan da suke buɗe asusu da sunan mata suna Damfara a shafukan sada zumunta

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta samu nasarar kama wasu magidanta da ake zargin su da damfarar mutane a shafukan sada zumunta, ta hanyar buɗe asusu da sunan mata wasu kuma na bayyana kansu a matsayin ƴan Sanda.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ta cikin sanarwar da ya aikowa Dala FM Kano a ranar Litinin, ya ce daga cikin Garada huɗun da ake zargin da buɗe asusun da sunan mata, yanzu haka biyu sun shiga hannun su, ana faɗaɗa bincike akan su, tare kuma da neman sauran.
“Mutanen suna buɗe asusu ne da sunan mata a shafukan sada zumunta, tare da ɗora hotunan mata don su ja hankalin Maza, wasu ma suna nuna cewar su ƴan sanda ne, idan tsautsayi ya rufta wa mutum su cuce shi Kuɗade ko kuma wayoyi, “in ji Kiyawa”.
Kakakin rundunar ƴan sandan na Kano Haruna Kiyawa, ya kuma gargaɗi al’umma musamman ma Matasa masu amfani da shafukan sada zumunta, da su kiyaye da irin mutanen da suke mu’amula da su a shafukan sada zumuntar, don gujewa faɗawa komar ɓata gari.
Da suke nasu jawabin magidantan da aka kama da zargin wannan aika-aikatar, sun bayyana nadamar su inda suka ce hakan ya zama izina a gare su kuma ba za su ƙara ba.
“Idan wasun mu sun gayyaci mutum a shafukan sada zumunta a matsayin za’a haɗu, daga ƙarshe mu kuma sai mu je wajen mu kama shi a matsayin mu na ƴan sanda amma fa na bogi; yau kuma dubun mu ta cika muna dana sani, “in ji magidancin”.

Manyan Labarai
An kuma: Kwamishina ya yi murabus a Kano

Kwamishinan tsaron Cikin gida na jihar Kano Major Janar Muhammad Inuwa ldris mai ritaya, ya yi murabus daga aikin sa a jihar.
Daraktan yada labaran Gwamnan Kano, Sanusi Bature D-Tofa ne ya sanar da hakan a cikin daren Talata 25 ga watan Maris ɗin shekarar 2025.
Ya ce tuni Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da takardar ajiye aikin Kwamishinan Sabuwar Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Ayukka na Musamman.
Ko dai a ranar 5 ga watan Janairun 2025, sai da Kwamishinan bibiyar ayyuka na jihar Muhammad Diggol, ya yi murabus daga muƙamin sa, al’amarin da ya janyo cece-kuce a tsakanin al’umma.
Daga bisani dai, gwamna Abba Kabir ya kuma yi wa tsohon Kwamishinan tsaron Cikin gida da ayyuka na musamman ɗin fatan alkhairi bisa ƙoƙarin da ya yi tare da gode masa kan sadaukar da lokacin sa don ci gaban al’umma a jihar.

Hangen Dala
Take hakki:- Matakin Amnesty game da kama wasu ‘yan jarida a Kano

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International, ta yi ala-wadai da cin zarafin ‘yan jarida biyu a Kano, wato mawallafin jaridar kano Times, Buhari Abba da kuma Isma’il Auwal.
Cikin sanarwar sa Ƙungiyar ta wallafa a shafin ta na facebook,
ta ce babu shakka abin da rundunar ‘Yansandan jihar Kano ta yi bisa umarnin Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ibrahim Waiya abin takaici ne.
Rundunar ‘Yansandan jihar Kano dai ta gayyaci Buhari Abba zuwa sashin binciken manyan laifuka (CID) ne, harma kuma ta tsare shi na tsawon awanni.
Kuma dai ana tuhumar mutanen biyun ne da zargin ɓata sunan kwamishinan, ta hanyar wani ra’ayi da jaridar ta wallafa wanda Isma’il Auwal ya rubuta.
Kungiyar ta Amnesty ta ce duk ba zata lamunci duk wani yunƙuri na takewa waɗannan ‘Yan jarida haƙƙinsu ba.
A ƙarshe ƙungiyar taja hankalin gwamantin kano da kuma rundunar ‘Yansandan jihar, da su guji yunƙurin daƙile ‘yancin faɗin albarkacin baki.

Manyan Labarai
Kotun ɗaukaka ƙara ta amince da roƙon gwamnatin Kano kan dambarwar Masarauta

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta amince da roƙon gwamnatin jihar Kano a kan batun dambarwar masarautar jihar Kano.
Tun da farko lauyan gwamnatin Kano Barrister Ibrahim Isah Wangida, sh ne ya shigar da buƙatar a gaban katun ɗaukaka ƙara inda ya bayyana wa kotun cewar, sun shigar da ɗaukaka ƙara a gaban kotun koli akan umarnin da kotun daukaka kara ta bayar ranar a ranar 14 ga wannan watan inda ta ayyana cewar kowane bangare ya tsaya a inda yake.
Da yake bayyana roƙon, Barrister Wangida ya ce sun cika duk wata ƙa’ida ta ɗaukaka ƙara akan batun umarnin kotun na ranar 14 ga wata.
Kotun ɗaukaka ƙarar dai ta rushe hukuncin babbar kotun tarayya ta Kano wadda ta ayyana soke naɗin Malam Muhammadu Sanusi na biyu, a matsayin sarkin Kano na 16, inda kotun ɗaukaka ƙarar ta ayyana cewar kotun tarayya ba ta da hurumin shiga sabgar masarauta la’akari da hurumin na babbar kotun jiha ne.
Sai dai mai kara tun da fari Aminu Babba Dan Agundi, ya ƙalubalanci hukuncin ta hanyar ɗaukaka kara a kotun Ƙoli, kuma ya sake roƙon kotun ɗaukaka ƙara da ta dakatar da zartas da hukunci har zuwa lokacin da kotun koli zanta bayyana matsayar ta.
Barrister Ibrahim Isah Wangida da ke wakiltar gwamnatin jihar Kano, ya ce yanzu hannun kotun daukaka kara a naɗe yake kasancewar basu gamsu da wancan umarni da ta bayar ba, kuma sun ɗaukaka ƙara.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa, wannan lamarin dai ya faro ne tun a lokacin da majalisar dokokin Kano ta rushe dokar masarautu wadda tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya gyara a lokacin mulkinsa, kuma bayan rushe dokar Aminu Babba Dan Agundi ya shigar da ƙara akan tsarin an tauye masa haƙƙi.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su