Connect with us

Labarai

Watan Azumi: Mun baza jam’ian mu na Operation Damisa Ƙisa Sabo don yaƙi da ɓata gari a Kano – Anty Snaching Phone

Published

on

Rundunar tsaron nan da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen waya da kuma daƙile Shaye-shayen kayan maye ta Anty Snaching Phone da ke nan Kano, ta buƙaci al’umma da su ƙara kula wajen rufe ƙofofin su yayin da za su tafi Sallar Dare, ta Tarawi da ta Tuhajjud da ke tafe a cikin wannan wata na Ramadana, domin gujewa faɗawa komar ɓata gari.

Kwamandan rundunar tsaron Inuwa Salisu Sharaɗa ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano, ya kuma ce akwai buƙatar mutane su kaucewa yin sakaci wajen kula da muhallansu a cikin watan domin kaucewa haɗuwa da ɓata gari masu sace-sacen kayan mutane.

Inuwa Sharaɗa, ya kuma ƙara da cewa a ƙokarin su na daƙile harkokin ɓata garin da ke addabar mutane a sassan jihar Kano, tuni rundunar ta baza jam’ian ta domin ganin an kara wanzar da zaman lafiya a jihar.

“Jami’an mu suna kewayawa gurare daban-daban cikin dare da Rana, da ma kowanne lokaci, domin samar da tsaro ga al’umma, a cikin wannan wata na azumin Ramadana da wasu ke nauyin Bacci, “in ji shi”.

Inuwa Sharaɗa, wanda shi ne mai bai wa gwamnan jihar Kano shawara akan harkokin Tsaro, ya kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da basu haɗin kan da ya dace, don ganin an samu nasara a yaƙin da suke yi da ɓata gari a sassan jihar.

Hangen Dala

Take hakki:- Matakin Amnesty game da kama wasu ‘yan jarida a Kano

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International, ta yi ala-wadai da cin zarafin ‘yan jarida biyu a Kano, wato mawallafin jaridar kano Times, Buhari Abba da kuma Isma’il Auwal.

Cikin sanarwar sa Ƙungiyar ta wallafa a shafin ta na facebook,
ta ce babu shakka abin da rundunar ‘Yansandan jihar Kano ta yi bisa umarnin Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ibrahim Waiya abin takaici ne.

Rundunar ‘Yansandan jihar Kano dai ta gayyaci Buhari Abba zuwa sashin binciken manyan laifuka (CID) ne, harma kuma ta tsare shi na tsawon awanni.

Kuma dai ana tuhumar mutanen biyun ne da zargin ɓata sunan kwamishinan, ta hanyar wani ra’ayi da jaridar ta wallafa wanda Isma’il Auwal ya rubuta.

Kungiyar ta Amnesty ta ce duk ba zata lamunci duk wani yunƙuri na takewa waɗannan ‘Yan jarida haƙƙinsu ba.

A ƙarshe ƙungiyar taja hankalin gwamantin kano da kuma rundunar ‘Yansandan jihar, da su guji yunƙurin daƙile ‘yancin faɗin albarkacin baki.

Continue Reading

Labarai

Zan haɗa kai da hukumomin tsaro da Baturan ƴan Sanda don magance matsalolin tsaro a Kano – CP Bakori

Published

on

Sabon kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Dr. Ibrahim Adamu Bakori, ya ce zai haɗa kai da dukkannin hukumomin tsaro da baturan ƴan sandan da ke kan iyakokin jihar, don ganin an sami ingantacciyar tsaro a faɗin jihar.

Dr. Ibrahim Bakori ya bayyana hakan ne a zantawar sa da manema labarai ciki har da wakilin tashar Dala FM Kano, a ranar Laraba 19 ga watan Maris ɗin 2025.

Ya kuma ce zai amfani da fasahar sadarwa wajan gudanar da aikin sa, tare kuma da wayar da akan al’umna kasancenwar aikin tsaro na kowa ne.

A makon da ya gabata ne dai rundunar ƴan Sanda ta ƙasa ta turo CP Ibrahim Adamu Bakori, jihar Kano, wanda ya maye gurbin Salman Dogo Garba, bisa samun ƙarin girma da ya yi zuwa matakin AIG.

Continue Reading

Labarai

Tsohon shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya ƙaryata ficewar sa daga APC zuwa SDP

Published

on

Tsohon shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya musanta wata jita-jita da ake yaɗawa kan cewar ya fice daga cikin jam’iyyar APC mai mulki a ƙasa, zuwa SDP, al’amarin da ya ce bashi da tushe ballantana makama.

A cikin wata sanarwar da mashawarci na musamman ga tsohon Sanatan a kafafen yaɗa labarai Ezrel Tabiowo, ya fitar a jiya Lahadi, ta ce jita-jitar da ake yaɗawa na cewar Ahmad Lawan ya fice daga jam’iyyar ta APC, ƙarya ce tsagwaronta.

Jaridar Daily trust ta ruwaito cewar, sanarwar ta kuma ce, har yanzu Ahmad Lawan ɗan Jam’iyyar APC ne, kuma yana biyayya ga jam’iyyar, wadda yake alfahari da ita.

Continue Reading

Trending