Connect with us

Labarai

Ku tallafawa mabuƙata a cikin watan Ramadana don rage musu raɗaɗin rayuwa – Dr. Mujahedden

Published

on

Mataimakin Babban kwamandan Hisbah ta Jahar Kano Dakta Mujahideen Aminudden ya shawarci masu Hannu da shuni da su ƙara fitowa wajen tallawa masu ƙaramin ƙarfe musamman ma a wannan lokaci na azumin Ramadana, domin rage musu wani raɗaɗi da kuma samun gwaggwaɓar lada a wajen Ubangiji S.W.T.

Dakta Mujahedden Aminudden ya bayyana hakan ne yayin da ya ƙaddamar da rabon tallafin kayan Abinci ga iyayen Marayu da mabuƙata aƙalla su 2500, a yankin Nassarawa da ke nan Kano, domin rage musu wani radaɗin rayuwa musamman ma a watan nan na azumin Ramadana da ake ciki.

Da yake jawabi ga manema labarai Dakta Mujahideen, yayin rabon tallafin kayan abincin a ranar Asabar, ya ce sun bai wa mabuƙata da iyayen Marayu tallafin kayan abincin ne da suka haɗar da Shinkafa da Masara da Gero da kuma Burodi, domin rage musu wata damuwa ta yau da kullum don su samu wani sauƙi.

Dakta Aminudden ya kuma jinjinanwa gwamnatin jahar Kano, da babban kwamandan Hisbah a jihar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da ma ɗai-ɗai kun jama’a bisa gudunmawar da suke bayar wa wajen tallafawa mabuƙata.

Hangen Dala

Take hakki:- Matakin Amnesty game da kama wasu ‘yan jarida a Kano

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International, ta yi ala-wadai da cin zarafin ‘yan jarida biyu a Kano, wato mawallafin jaridar kano Times, Buhari Abba da kuma Isma’il Auwal.

Cikin sanarwar sa Ƙungiyar ta wallafa a shafin ta na facebook,
ta ce babu shakka abin da rundunar ‘Yansandan jihar Kano ta yi bisa umarnin Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ibrahim Waiya abin takaici ne.

Rundunar ‘Yansandan jihar Kano dai ta gayyaci Buhari Abba zuwa sashin binciken manyan laifuka (CID) ne, harma kuma ta tsare shi na tsawon awanni.

Kuma dai ana tuhumar mutanen biyun ne da zargin ɓata sunan kwamishinan, ta hanyar wani ra’ayi da jaridar ta wallafa wanda Isma’il Auwal ya rubuta.

Kungiyar ta Amnesty ta ce duk ba zata lamunci duk wani yunƙuri na takewa waɗannan ‘Yan jarida haƙƙinsu ba.

A ƙarshe ƙungiyar taja hankalin gwamantin kano da kuma rundunar ‘Yansandan jihar, da su guji yunƙurin daƙile ‘yancin faɗin albarkacin baki.

Continue Reading

Labarai

Zan haɗa kai da hukumomin tsaro da Baturan ƴan Sanda don magance matsalolin tsaro a Kano – CP Bakori

Published

on

Sabon kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Dr. Ibrahim Adamu Bakori, ya ce zai haɗa kai da dukkannin hukumomin tsaro da baturan ƴan sandan da ke kan iyakokin jihar, don ganin an sami ingantacciyar tsaro a faɗin jihar.

Dr. Ibrahim Bakori ya bayyana hakan ne a zantawar sa da manema labarai ciki har da wakilin tashar Dala FM Kano, a ranar Laraba 19 ga watan Maris ɗin 2025.

Ya kuma ce zai amfani da fasahar sadarwa wajan gudanar da aikin sa, tare kuma da wayar da akan al’umna kasancenwar aikin tsaro na kowa ne.

A makon da ya gabata ne dai rundunar ƴan Sanda ta ƙasa ta turo CP Ibrahim Adamu Bakori, jihar Kano, wanda ya maye gurbin Salman Dogo Garba, bisa samun ƙarin girma da ya yi zuwa matakin AIG.

Continue Reading

Labarai

Tsohon shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya ƙaryata ficewar sa daga APC zuwa SDP

Published

on

Tsohon shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya musanta wata jita-jita da ake yaɗawa kan cewar ya fice daga cikin jam’iyyar APC mai mulki a ƙasa, zuwa SDP, al’amarin da ya ce bashi da tushe ballantana makama.

A cikin wata sanarwar da mashawarci na musamman ga tsohon Sanatan a kafafen yaɗa labarai Ezrel Tabiowo, ya fitar a jiya Lahadi, ta ce jita-jitar da ake yaɗawa na cewar Ahmad Lawan ya fice daga jam’iyyar ta APC, ƙarya ce tsagwaronta.

Jaridar Daily trust ta ruwaito cewar, sanarwar ta kuma ce, har yanzu Ahmad Lawan ɗan Jam’iyyar APC ne, kuma yana biyayya ga jam’iyyar, wadda yake alfahari da ita.

Continue Reading

Trending