Connect with us

Manyan Labarai

Da Ɗumi-Ɗumi! Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar Rivers da mataimakin sa da ƴan majalisar jihar na watanni 6.

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara, da mataimakiyar sa Mrs. Ngozi Odu, har na tsawon watanni 6.

Shugaba Tinubu ya bayyana daukar matakin ne a cikin wani taƙaitaccen jawabin sa da ya gabatar a cikin daren Talatar nan, ya ce ya yi amfani da damar da kundin tsarin mulki ya ba shi wajen sanya wannan doka wacce ta kwace mulkin jihar daga hannun gwamnan jihar Siminalayi Fubara da mataimakin sa har sai lamura sun dawo dai-dai a jihar.

Kazalika, shugaba Tinubu ya kuma bayyana dakatar da dukkanin ƴan majalisar dokokin jihar suma na tsawon watanni shidan, tare da sanya dokar ta ɓaci a jihar.

Wannan dai na zuwa ne biyo bayan rikicin siyasar da ya daɗe da kunno kai a tsakanin gwamna Fubara da ministan birnin tarayya Abuja Nyesome Wike, al’amarin da ya janyo takun saƙa tsakanin sa da ƴan majalisar dokokin jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Manyan Labarai

An kuma: Kwamishina ya yi murabus a Kano

Published

on

Kwamishinan tsaron Cikin gida na jihar Kano Major Janar Muhammad Inuwa ldris mai ritaya, ya yi murabus daga aikin sa a jihar.

Daraktan yada labaran Gwamnan Kano, Sanusi Bature D-Tofa ne ya sanar da hakan a cikin daren Talata 25 ga watan Maris ɗin shekarar 2025.

Ya ce tuni Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da takardar ajiye aikin Kwamishinan Sabuwar Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Ayukka na Musamman.

Ko dai a ranar 5 ga watan Janairun 2025, sai da Kwamishinan bibiyar ayyuka na jihar Muhammad Diggol, ya yi murabus daga muƙamin sa, al’amarin da ya janyo cece-kuce a tsakanin al’umma.

Daga bisani dai, gwamna Abba Kabir ya kuma yi wa tsohon Kwamishinan tsaron Cikin gida da ayyuka na musamman ɗin fatan alkhairi bisa ƙoƙarin da ya yi tare da gode masa kan sadaukar da lokacin sa don ci gaban al’umma a jihar.

Continue Reading

Hangen Dala

Take hakki:- Matakin Amnesty game da kama wasu ‘yan jarida a Kano

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International, ta yi ala-wadai da cin zarafin ‘yan jarida biyu a Kano, wato mawallafin jaridar kano Times, Buhari Abba da kuma Isma’il Auwal.

Cikin sanarwar sa Ƙungiyar ta wallafa a shafin ta na facebook,
ta ce babu shakka abin da rundunar ‘Yansandan jihar Kano ta yi bisa umarnin Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ibrahim Waiya abin takaici ne.

Rundunar ‘Yansandan jihar Kano dai ta gayyaci Buhari Abba zuwa sashin binciken manyan laifuka (CID) ne, harma kuma ta tsare shi na tsawon awanni.

Kuma dai ana tuhumar mutanen biyun ne da zargin ɓata sunan kwamishinan, ta hanyar wani ra’ayi da jaridar ta wallafa wanda Isma’il Auwal ya rubuta.

Kungiyar ta Amnesty ta ce duk ba zata lamunci duk wani yunƙuri na takewa waɗannan ‘Yan jarida haƙƙinsu ba.

A ƙarshe ƙungiyar taja hankalin gwamantin kano da kuma rundunar ‘Yansandan jihar, da su guji yunƙurin daƙile ‘yancin faɗin albarkacin baki.

Continue Reading

Manyan Labarai

Kotun ɗaukaka ƙara ta amince da roƙon gwamnatin Kano kan dambarwar Masarauta

Published

on

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta amince da roƙon gwamnatin jihar Kano a kan batun dambarwar masarautar jihar Kano.

Tun da farko lauyan gwamnatin Kano Barrister Ibrahim Isah Wangida, sh ne ya shigar da buƙatar a gaban katun ɗaukaka ƙara inda ya bayyana wa kotun cewar, sun shigar da ɗaukaka ƙara a gaban kotun koli akan umarnin da kotun daukaka kara ta bayar ranar a ranar 14 ga wannan watan inda ta ayyana cewar kowane bangare ya tsaya a inda yake.

Da yake bayyana roƙon, Barrister Wangida ya ce sun cika duk wata ƙa’ida ta ɗaukaka ƙara akan batun umarnin kotun na ranar 14 ga wata.

Kotun ɗaukaka ƙarar dai ta rushe hukuncin babbar kotun tarayya ta Kano wadda ta ayyana soke naɗin Malam Muhammadu Sanusi na biyu, a matsayin sarkin Kano na 16, inda kotun ɗaukaka ƙarar ta ayyana cewar kotun tarayya ba ta da hurumin shiga sabgar masarauta la’akari da hurumin na babbar kotun jiha ne.

Sai dai mai kara tun da fari Aminu Babba Dan Agundi, ya ƙalubalanci hukuncin ta hanyar ɗaukaka kara a kotun Ƙoli, kuma ya sake roƙon kotun ɗaukaka ƙara da ta dakatar da zartas da hukunci har zuwa lokacin da kotun koli zanta bayyana matsayar ta.

Barrister Ibrahim Isah Wangida da ke wakiltar gwamnatin jihar Kano, ya ce yanzu hannun kotun daukaka kara a naɗe yake kasancewar basu gamsu da wancan umarni da ta bayar ba, kuma sun ɗaukaka ƙara.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa, wannan lamarin dai ya faro ne tun a lokacin da majalisar dokokin Kano ta rushe dokar masarautu wadda tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya gyara a lokacin mulkinsa, kuma bayan rushe dokar Aminu Babba Dan Agundi ya shigar da ƙara akan tsarin an tauye masa haƙƙi.

Continue Reading

Trending