Hangen Dala
Gwamnoni sun bukaci a kawo karshen matasalar Filato

Ƙungiyar Gwamnonin kasar nan (NGF) ta buƙaci jagororin jihar Plateau su haɗa kan al’ummar jihar mai yawan al’adu da ƙabilu domin dakatar da kashe-kashen mutane da ake yawan samu a jihar.
Shugaban ƙungiyar, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Kwara – Abdulrahman Abdulrazaq, ne ya bayyana haka ranar Alhamis lokacin da ya kai ziyarar jaje.
“Muna kira da jagorori da masu faɗa a ji a duka garuruwan jihar da sauran fannoni da su haɗa hannu da gwamnan jihar wajen haɗa kan al’ummar jihar tare da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa”, in ji shugaban ƙungiyar ta NGF.
“Ya kamata shugabannin matasan al’umomin jihar su fito su haɗa kai wajen yin Allah wadai da tashin hankalin da ake samu a jihar, muna kira da a riƙa sasanta duka matsalolin da suka taso ta hanyar tattaunawa da lalama tare da girmama juna,” a cewar Abdulrahman Abdulrazaq.
Fiye da mutum 100 ne aka kashe cikin mako biyu da suka gabata, lokacin da wasu mahara suka kai hari a wasu garuruwan ƙananan hukumomin Bokkos da Bassa a jihar.
A ranar Talata ne babban sifeton ƴansandan ƙasar, Kayode Egbetokun ya ziyarci jihar inda ya sha alwashin kamo waɗanda suka ƙaddamar da kashe-kashen, da ya bayyana da na rashin imani, domin hukunta su.

Baba Suda
Hukumar tattara kudaden shiga ta Kano ta rufe wasu bankuna

Hukumar Tattara kudaden shiga ta jahar kano ta kulle bakin Eco da Zenith dake kan titin Murtala Muhammad. Sakamakon rashin biyan haraji.
Cikakken labarin na Zuwa….

Baba Suda
Kisan Makurdi:- Gwamnatin Kano za ta tura wakilai

Gwamnatin Jihar Kano tayi Allah wadai da kisan mutane biyu Yan Jihar a garin Makurdi dake Jihar Benue.
Cikin sanarwar da Daraktan Gwamnan Kano kan harkokin yada labarai Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ruwaito Gwamnan na Mika sakon jaje ga alummar Jihar da iyalai da ‘yan uwan wadanda abin ya rutsa dasu, Barhma Suleman da Jamilu Ahmad.
Kazalika Gwamnan yayi alkawarin daukar Matakin da ya dace kan batun, tare da fadin gwamnatin Kano za ta tashi wakilai har Zuwa Jihar Benue domin tabbatar da daukar Matakin da ya dace.

Baba Suda
NNPP:- Kwankwaso ya sulhunta rikicin jamiyyar

Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da jagoran kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wani zama da Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado, Tofa da Dawakin Tofa, Wato Honorable Abdulkadir Jobe, da kuma Daraktan yada labaran Gwamnan Kano Honorable Sunusi Bature Dawakin Tofa.
Ganawar wadda ta gudana a yammacin wannan Alhamis ta kawo karshen Jan Zaren dake faruwa tsakanin Dan majalisar da kuma Sunusi Bature.
A baya bayan nan dai an kai ruwa rana tsakanin su, Inda kowa ne bangare ke mayar da martani.
Abdulkadir Jobe da kuma Sunusi Bature dukkanin su mabiya jamiyyar NNPP ne tsagin kwankwasiyya.

-
Nishadi6 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su